ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Sojojin Nijeriya Na Samun Nasarori Duk Da Kalubalen Tsaro

by Rabi'u Ali Indabawa
5 months ago

Fadar Shugaban Kasa ta ce masu sukar yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da batun rashin tsaro a Nijeriya suna yin watsi da irin sadaukarwa da nasarorin da sojojin kasar ke samu a kullum a fannoni daban-daban na ayyukan tsaro.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a cikin wata mukala mai taken “Murnar Jarumtar Ayyukan Sojojinmu a Fannonin Ayyuka Daban-daban”

Ya ce wasu ‘yan Nijeriya  da “masu sharhi daga nesa” suna fi mayar da hankali kan munanan abubuwa kamar sace-sace, fashe-fashen abubuwan fashewa, hare-haren kunar bakin wake da sauran laifuka, yayin da suke yin watsi da nasarorin da sojoji ke samu.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, irin wannan fahimta na rage darajar jarumtar da jami’an rundunar sojin Nijeriya  ke nunawa wajen yakar ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da masu satar danyen mai.

Onanuga ya ce rahotannin tsaro na baya-bayan nan sun nuna cewa sojoji na samun gagarumar nasara a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a sassa daban-daban na kasar.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ya bayar da misali da ceto fasinjojin da aka yi garkuwa da su a Jihar Binuwe , inda sojojin Operation Whirl Stroke suka gudanar da aikin ceto cikin nasara a yankin Ohimini.

Haka kuma ya ambaci ayyuka a Jihar Filato, inda aka kama wadanda ake zargi da hannu a kashe-kashe, aka kwato makamai, tare da dakile satar shanu da kuma mayar da martani ga hare-hare.

A jihohin Borno  da Yobe  kuwa, ya ce sojoji sun kashe ‘yan ta’adda, sun dakile hare-hare, sannan sun kama masu safarar kayan taimakon ‘yan ta’adda da ake zargi suna da alaka da Boko Haram da ISWAP.

Ya kuma ce an gano tare da lalata abubuwan fashewa a wasu yankuna na Borno da Imo yayin sintiri da aikin share gari.

A Jihar Edo, sojoji sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a Auchi, sun ceto wadanda aka yi garkuwa da su tare da kama wasu mutane. A jihar Kogi kuma, an lalata sansanin ‘yan ta’adda tare da kama wani mai kai musu kaya a wani aiki na hadin gwiwa.

Fadar Shugaban Kasa ta ce duk da kalubalen tsaro da ke ci gaba da wanzuwa, sojojin Nijeriya suna ci gaba da sadaukar da kansu wajen kare ‘yan kasa, inda wasu ke rasa rayukansu a bakin aiki.

Onanuga ya kara da cewa: “Kalubale na nan, kuma yakin bai kare ba. Amma abin da sojoji da gwamnati ke bukata daga mu shi ne godiya da karramawa, ba zagi da kushe ba.”

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Boko Haram Ta Kashe Manoma Da Masu Yankan Itace 20 A Wani Sabon Hari A Borno

Boko Haram Ta Kashe Manoma Da Masu Yankan Itace 20 A Wani Sabon Hari A Borno

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.