ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Taraktoci 2,000 Domin Noman Hekta Miliyan 1.5

by Sulaiman
7 months ago
Noma

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wasu sabbin taraktocin noma guda 2,000 domin bunkasa aikin noma na zamani a fadin kasar nan, tare da manufar noma sama da hekta miliyan 1.5 a duk shekara.

Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ne ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da shirin a ranar Litinin a Abuja, inda ya ce wannan mataki wani gagarumin sauyi ne a bangaren noma karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

ADVERTISEMENT
  • Saka Ya Rattaba Hannu Akan Karin Kwantiragin Shekaru 5 A Arsenal 
  • Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Zamfara Saniyar Ware Wajen Tallafin Kuɗi Saboda Ba Ta APC – Dauda Lawal

A cewarsa, an kaddamar da shirin ne a karkashin shirin gwamnatin tarayya na Renewed Hope National Agricultural Mechanisation Programme, wanda zai samar da taraktoci masu karfin aiki tare da na’urorin noma sama da 9,000 domin inganta yawan amfanin gona.

LABARAI MASU NASABA

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ya bayyana cewa za a fara da tura taraktoci 600 a mataki na farko, sannan a biyo da wasu 750 da kuma 650 a matakai na gaba har a kai ga cika adadin 2,000 a fadin kasar nan baki daya.

Ministan ya kara da cewa ba za a bai wa mutane taraktocin a matsayin mallaka kai tsaye ba, sai dai za a mika su ga masu samar da ayyukan injinan noma (Mechanisation Service Providers), inda kowace na’ura za ta iya noma kusan hekta 600 a shekara.

Ana sa ran shirin zai taimaka wa manoma sama da miliyan 1.2 a duk fadin Najeriya, tare da inganta samar da abinci da kuma bunkasa tattalin arzikin karkara.

Hakazalika, ya ce gwamnatin ta samar da asusun tallafin noma na Naira biliyan 50 ta hannun Bankin Masana’antu domin saukaka harkokin zuba jari a fannin noma, yayin da aka kuma tanadi Naira biliyan 250 domin tallafa wa kananan manoma miliyan daya a daminar shekarar 2026.

Bugu da kari, gwamnatin ta shirya samar da motocin gyaran taraktoci guda 36, da kuma gina cibiyoyin kula da injinan noma guda bakwai a sassan kasar nan, tare da shirin kafa babbar masana’antar hada taraktoci da za ta rika samar da tsakanin guda 2,000 zuwa 4,000 a duk shekara.

Gwamnatin ta bayyana cewa wannan shiri zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, rage wahalar aikin noma, da kuma kara yawan amfanin gona domin tabbatar da wadatar abinci a kasar nan.

Noma
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Next Post
Yaya Da Kani Sun Mutu A Cikin Ramin Masai A Kano

Ramadan: Kano Ta Bayar Da Umarnin Rufe Wuraren DJ Da Tarukan Nishaɗantarwa

LABARAI MASU NASABA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.