ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Hadin Kan Al’umma Don Kawo Karshen Matsalar Tsaro

by Rabi'u Ali Indabawa
5 days ago
Tsaro

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi gargadin cewa matakin soji kadai ba zai iya kawo karshen rashin tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya ba, yana mai kira ga al’ummomi, sarakunan gargajiya da shugabannin addini, matasa, mata da kuma ’yan kasuwa masu zaman kansu da su hada kai da hukumomin tsaro wajen yaki da miyagun laifuka tare da magance tushen matsalar tashin hankali.

Tinubu ya yi wannan kiran ne ranar Litinin a Taron Tsaro na Yankin Arewa ta Tsakiya na 2026 da aka gudanar a Makurdi, Jihar Benuwe, inda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya wakilce shi.

Da yake magana kan taken taron, “Hanyoyin Hadin Gwiwa Wajen Karfafa Tsaro da Daidaiton Yanki,” Shugaban Kasar ya ce rashin tsaro ya zama mai sarkakiya sosai, wanda ya sa ba za a iya magance shi ta hanyar hukumar tsaro guda daya, gwamnati guda ko al’umma guda ba.

ADVERTISEMENT

Ya ce, “Babu wata hukuma guda, babu wani matakin gwamnati guda, kuma babu wata al’umma guda da za ta iya tabbatar da tsaron wannan yanki ita kadai. Rashin tsaro ba ya mutunta iyakokin jihohi ko ikon hukumomi.”

Tinubu ya bukaci masu ruwa da tsaki su kawo karshen hamayya, maimaita ayyuka da kuma boye bayanan sirri, yana mai cewa miyagu kan rika tsallaka iyakokin kananan hukumomi da jihohi, yayin da martanin hukumomin tsaro ke kasancewa ba tare da cikakken hadin kai ba.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Yayin da yake yabawa rundunar soji, ’yansanda da hukumomin leken asiri kan nasarorin da suka samu a baya-bayan nan wajen yaki da ’yan ta’adda da sauran kungiyoyin masu aikata laifuka, ciki har da hallaka kwamandoji, mika wuya da mayakan suka yi da kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, Shugaban Kasar ya ce dole ne a hada ayyukan soji da matakan da za su magance abubuwan da ke haddasa tashin hankali.

Ya ce, “Matakin soji kadai ba zai samar da zaman lafiya mai dorewa a Arewa ta Tsakiya ba. Karfi na iya danne tashin hankali; amma ba zai warware korafe-korafen da ke haifar da shi ba.”

Tinubu ya bayyana rikicin neman filaye da ruwa, sauyin yanayi, yaduwar hamada, rikice-rikicen amfani da filaye da ba a warware su ba, raunin hanyoyin warware rikici a matakin al’umma da yaduwar makamai ba bisa ka’ida ba a matsayin wasu daga cikin abubuwan da ke ci gaba da haifar da rashin tsaro.

Ya bukaci sarakunan gargajiya da shugabannin addini su kasance sahun farko wajen kare al’umma daga barazanar da ke tasowa, ta hanyar bayar da gargadin farko da kuma inganta sulhu.

Ya ce, “Ina rokonku da ku kasance sahun farko wajen bayar da gargadin farko, kuma ku zama amintattun muryoyinmu wajen sasanta rikice-rikice.”

Ya kuma yi kira ga al’ummomi da su rika bai wa hukumomin tsaro bayanan sirri cikin lokaci tare da daina kare masu aikata laifuka saboda dangantakar iyali, kabila ko wasu alaka.

Ya ce, “Tsaro yana farawa ne daga gare ku. Ina kira ga kowane dan kasa da ya rika bai wa hukumomin tsaro bayanai, ya kuma daina kare aikata laifi saboda zumunci ko son rai.”

Shugaban Kasar ya ce mata da matasa dole su kasance a tsakiyar ayyukan samar da zaman lafiya, yayin da gwamnati za ta fadada hanyoyin samun guraben tattalin arziki domin rage sha’awar matasa shiga ayyukan laifi.

Tsaro
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Ba Za Ku Taba Nadamar Zaben APC A Karkashin Mulkina Ba – Tinubu

Kyamar Baki: Tinubu Ya Yi Karar Afirka Ta Kudu A Gaban Kungiyar Tarayyar Afirka

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.