ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Kai, Hakuri Da Riko Da Addini Su Ne Jigon Zaman Lafiyar Nijeriya – Tinubu

by Sani Anwar
7 months ago
Addini

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Shugaba Bola Tinubu ya roki ‘yan Nijeriya, da su rungumi hadin kai, koyarwar addini, hakuri da zaman lafiya a matsayin ginshikan tsaro, kwanciyar hankali da ci gaban kasa.

Shugaban ya yi wannan kira ne a jiya a wajen taron kasa da kasa karo na 4 na Cibiyar Wayewar Musulunci da Tattaunawar Addinin Musulunci da aka gudanar a Kano.

  • Za A Gudanar Da Dandalin Tattaunawa Na Masana Na Jam’iyyar JKS Da KMT A Birnin Beijing
  • Akpabio: Ba A Canza Komai A Cikin Sabbin Dokokin Haraji Ba 

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya wakilce shi a wajen taron.

Tinubu ya yaba wa wannan cibiya da masallacin Sultan Bello Kaduna, bisa yadda suke ci gaba da gudanar da cudanya da juna da nufin samar da zaman lafiya da hadin kan kasa.

“Wannan taro, yana ci gaba da tabbatar da manufofin zaman lafiya da hadin kan al’ummarmu, ta hanyar tattaunawa. Ko shakka babu, an girmama ni da wannan gayyata da aka yi min,” in ji shugaban.

Ya kuma bayyana yadda taron ya mayar da hankali a kan abubuwan da marigayi Sheikh Mahmud Abubakar Gummi ya bari na alhairi da kuma ilmantarwa, inda ya bayyana cewa; fitaccen malamin addinin musuluncin ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da hadin kai a lokutan da suka taka muhimmiyar rawa a tarihin Nijeriya.

“Sheikh Gummi, ya fahimci mahadar imani da siyasa, sannan kuma ya yi aiki kafada da kafada da hukumomi, bayan samun ‘yancin kai da yakin basasa, don inganta hadin kai da zaman lafiya,” in ji shi.

Shugaban ya ci gaba da bayyana Sheikh Gummi a matsayin fitaccen malami, wanda ya kawo gyara, kuma jigo a kasa wanda tasirinsa yake da matukar yawa a fannin addini.

“Ya kasance malami, wanda ya kawo canje-canje, mai ba da shawara, kuma fitaccen marubuci.

Ya shawarci tsararrakinsa da su yi duk abin da ya, domin samun hadin kan Nijeriya, a aikace da kuma addinance, ”in ji shi.

Da yake magana a kan kalubalen da kasa ke fuskanta a halin yanzu, Shugaba Tinubu ya bukaci ‘yan Nijeriya, da su yi watsi da labaran da za su raba kan al’umma, musamman wadanda ke nuni da cewa; ‘yan kasar ba ta da ‘yancin yin addini.

“Dole ne mu karfafa kudurinmu na samar da kasa dunkulalliya, sannan wajibi ne a tsaya tsayin daka, wajen dakile yunkurin da ake yi na bata Nijeriya a matsayin kasa da ke tauye ‘yancin addini,” in ji shi.

Ya jaddada cewa, tsaron kasa ba ya taba rabuwa da hadin kai tare da mutunta juna a tsakanin ‘yan kasa, ba tare kuma da la’akari da bambancin addini ko kabilanci ba.

“Tsaron kasarmu, yana da nasaba da hadin kanmu, hadin kanmu da mutunta bambancin addini, dole ne mu hada karfi da karfe wajen yaki da masu neman raba kanmu,” in ji shugaban.

Da yake jaddada kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyi, Tinubu ya ce; ana daukar kwararan matakai na tunkarar matsalar rashin tsaro a fadin wannan kasa.

“Gwamnatina, tana yin aiki tukuru wajen kare rayuka da dukiyoyi tare kuma da aiwatar da yaki da ta’addanci ta kowane bangare,” in ji shi.

Addini
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana
Labarai

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Next Post
An Nada Liu Xianfa Wakilin Musamman Na Gwamnatin Sin Kan Harkokin Afirka

An Nada Liu Xianfa Wakilin Musamman Na Gwamnatin Sin Kan Harkokin Afirka

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.