Masana tattalin arziƙi, sun buƙaci gwamnatin tarayya, da ta yi watsi da shawarar da asusun ba da lamuni na duniya (IMF), ya bayar na sanya haraji kan ayyukan man fetur da na sadarwa, inda suka yi gargaɗin cewa; irin waɗannan matakan, za su ƙara tabarbarewar hauhawar farashin kayayyaki tare da ƙara gurgunta kuɗaɗen shiga na gida da kuma ƙara wa ƴan Nijeriya matsalolin tattalin arziƙi.
Har ila yau, masana tattalin arziƙin, waɗanda suka yi watsi da shawarar ta IMF, sun bayyana ta a matsayin wadda za ta tabarbara al’amura, suna masu jayayyar cewa; magidanta na matuƙar shan wahala sakamakon ƙarin kuɗin wutar lantarki, farashin sadarwa da hauhawar farashin kayayyaki, don haka a halin yanzu, ba za su iya jure wani ƙarin harajin na daban ba.
IMF ta shawarci gwamnatin Nijeriya, da ta yi la’akari da tsawaita harajin mai da kuma bullo da haraji kan ayyukan sadarwa a wani bangare na ƙoƙarin samar da kuɗaɗen shiga da kuma samar da gurbi na kasafin kuɗi, don samar da ci gaba.
A cikin rahoton shawarwari na mataki na IƁ na 2026 kan Nijeriya, IMF ta yi gargaɗin cewa; duk da sauye-sauyen harajin da aka yi a baya-bayan nan, akwai yiwuwar a buƙaci ƙarin matakan kuɗaɗen shiga na tsawon matsakaicin lokaci, domin tallafa wa muhimman ayyuka da sauran ababen more rayuwa.
A cewar Asusun, dole ne ƙoƙarin tara kuɗaɗen shiga na Nijeriya ya zarce iya gyare-gyaren gudanarwa, don magance matsalar ƙarancin kuɗaɗen shiga zuwa na ƙasar da kuma hauhawar farashin kayayyaki.
IMF ta ce; “Wataƙila za a buƙaci ƙarin sauye-sauyen manufofin haraji, kamar habaka ƙimar harajin kayayyaki da faɗaɗa zuwa kayan mai, daidaita kashe kuɗin harajin, musamman kebancewarsa a kan masana’antu masu haƙo mai da wasu harajin kwastam da gabatar da hanyoyi na sadarwa, don habaka ribar gudanarwa.”
An yi nuni da cewa, yayin da ake sa ran yin gyare-gyaren harajin da aka yi kwanan nan, zai inganta tattara kuɗaɗen shiga cikin lokaci, wasu matakan za su iya rage kuɗaɗen shiga cikin ƙanƙanin lokaci, kuma za su ɗauki lokaci kafin a samu gagarumar nasara.
IMF ta jaddada cewa, ci gaba da tattara kuɗaɗen shiga na da matuƙar muhimmanci, idan gwamnati na son ci gaba da kashe kuɗaɗe masu yawa tare da faɗaɗa shirye-shiryen shiga tsakani na zamantakewa da nufin rage tasirin sake fasalin tattalin arziƙi ga ƴan Nijeriya masu rauni.
“A cikin tsaka-tsakin lokaci, ci gaba da tattara kuɗaɗen shiga na da muhimmanci, don samar da ci gaba da ciyar da al’umma gaba,” in ji Asusun, yana mai cewa; akwai matsala, idan har ba a yi ƙoƙarin ci gaba da habaka kuɗaɗen da ake kashewa, tare da ƙarin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ba.
Duk da haka, cibiyar Bretton Woods ta yi gargaɗin cewa; lokacin da za a ɗauki sabbin matakan haraji, ya kamata a yi la’akari da ƙaruwar talauci da ƙarancin abinci a ƙasar.
Ya nanata cewa, duk wani ƙarin haraji ya kamata ya kasance tare da cikakken kuɗaɗe da kuma ingantaccen shirin musayar kuɗi, don kare al’umma daga ƙarin wahalhalun tattalin arziƙi.
“Lokacin da za a yi gyare-gyare, dole ne a yi la’akari da talauci da yanayin rashin abinci da kuma tabbatar da cewa; tsarin musayar kuɗaɗe na aiki da kuma samar da kuɗaɗe,” in ji rahoton.
Shawarar ta IMF, ta zo ne a daidai lokacin da Nijeriya ke ci gaba da fuskantar ƙarancin kuɗaɗen shiga, duk kuwa da sauye-sauyen da aka yi a baya-bayan nan da suka haɗa da cire tallafin man fetur da kuma ƙoƙarin inganta harkokin haraji.
Asusun ya yi hasashen cewa, talauci da ƙarancin abinci ka iya tabarbara al’amura, yayin da ake samun hauhawar farashin man fetur da kuma farashin abinci a duniya, inda ya ce; tuni talauci ya shafi kashi 63 cikin 100 na al’ummar ƙasar, yayin da kimanin ƴan Nijeriya miliyan 27 ke fuskantar ƙarancin abinci a shekarar 2025.
Har ila yau, ta sake nanata kiran da ta yi na a tsaya tsayin daka a kasafin kuɗi na wannan shekara ta 2026, inda ta yi gargaɗin cewa; kashe kuɗaɗen da ke da nasaba da talauci, ƙarancin abinci da shirye-shiryen babban zabe na 2027, na iya faɗaɗa gibin kasafin kuɗi da kuma ƙara yawan buƙatun kuɗi, idan ba a kula sosai ba.
Da yake mayar da martani ga shawarar, Farfesa a fannin tattalin arziƙi na Jami’ar Benin, Hassan Oaikhenan, ya gargaɗi gwamnatin tarayya game da aiwatar da shawarwarin da IMF ta bayar na ƙara yawan kuɗin haraji da kuma bullo da haraji kan ayyukan sadarwa.
Ya bayyana shawarwarin da cewa, sun yi yawa kuma ya yi gargaɗin cewa; za su iya ƙara tabarbarewar tattalin arziƙi a kan ƴan Nijeriyan da ke fama da tsadar rayuwa.
“Yan Nijeriya sun riga sun samu kansu cikin damuwa,” in ji shi. “Gwamnati ta riga ta samar da kuɗaɗen shiga masu yawa, don haka, ƙara yawan haraji kan harkokin sadarwa zai zama wuce gona da iri.”
Masanin tattalin arziƙin ya yi nuni da cewa, ƙarin kuɗin wutar lantarki da kuma kuɗaɗen sadarwa na baya-bayan nan, ya sanya ƙarin matsin lamba kan kuɗaɗen shiga na magidanta, yana mai gargaɗin cewa; ƙara harajin na iya ƙara wahalhalun tattalin arziƙi.
A cewarsa, sanya sabbin haraji a daidai lokacin da ƴan ƙasar da dama ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin isassun samun kuɗaɗen sayayya, zai kai ga faɗawa mummunar takura da matsi.
Don haka, ya buƙaci gwamnati da kada ta yi la’akari sosai da shawarar IMF, yana mai jaddada cewa; shawarar ba mai amfani ba ce, musamman idan aka yi la’akari da yanayin tattalin arziƙin da ake ciki a halin yanzu.
Oaikhenan ya kuma nuna shakku, kan dalilan ɗaukar manufofin da za su iya ƙara rage yawan kuɗaɗen shiga na ma’aikata da sauran magidanta.
A nasa bangaren, babban jami’in bayar da shawarwari na CFG, Tilewa Adebajo, ya ce; wannan ko kaɗan bai dace ba, ganin yadda gwamnati za ta duba ƙarin haraji ko kuma bullo da sabbi, musamman ganin an fara aiwatar da sabuwar dokar haraji a bana.
Adebajo, wanda kuma masanin tattalin arziƙi ne, ya yi zargin cewa; shawarar da IMF ta bayar na cewa, gwamnati na iya buƙatar ƙarin haraji ya saba wa amincewa da ci gaban da ake samu ta hanyar gyaran harajin gwamnati.
Ya yi nuni da cewa, sauye-sauyen da aka fara aiwatarwa a watan Janairu, ya fara samun karbuwa tare da samar da sakamako. Don haka, ya ce; bullo da ƙarin haraji ko ƙara yawan waɗanda ake da su a wannan mataki, ya yi wuri.
A cewarsa, sanya haraji mai yawa kan tattalin arziƙin da har yanzu ke fafutukar samun ci gaba mai inganci, yayin da ƴan kasuwa ke fama da illar rashin tabbas na tattalin arziƙin duniya, na iya yin illa ga nasarorin da aka samu ta hanyar yin gyare-gyaren da ake ci gaba da yi.
Haka zalika, Shugaban Hukumar Kula da Kuɗaɗe ta Agusto & Co, Ayokunle Olubunmi, ya ce; yanayin tattalin arziƙin da ake ciki yanzu, bai goyi bayan bullo da sabbin haraji ko ƙarin harajin da ake da su ba, ganin irin wahalhalun da magidanta da kasuwanci ke fuskanta.
“Yan Nijeriya na ci gaba da kokawa kan tasirin sauye-sauyen tattalin arziƙin da ake ci gaba da yi, waɗanda suka haɗa da cire tallafi, sake farfaɗo da kasuwar canji da kuma aiwatar da sabuwar dokar haraji.
“Shugaban da kansa ya amince da waɗannan ƙalubalen a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya. Haka kuma, 2027 shekarar zabe ce.”
Wani masanin tattalin arziƙi, Dakta Justin Amase, ya ce; shawarar Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) na cewa; Nijeriya ta ƙara haraji kan ayyukan sadarwa, ko kaɗan bai dace ba a yanayin tattalin arziƙin da ake ciki.
Amase ya ce, duk da cewa; yawan harajin da Nijeriya ke samu a cikin gida zai iya kasancewa mafi ƙaranci a Afirka, amma ƙarin haraji a daidai lokacin da ake fama da hauhawar farashi da ƙarancin samun kuɗin shiga da ƙalubalen yanayin kasuwanci, zai ƙara matsin lamba ga ƴan ƙasa da sauran ƴan kasuwa baki-ɗaya.















Discussion about this post