ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Halin Da Matsalar Tsaro Ta Jefa ‘Yan Gudun Hijira A Arerwacin Nijeriya

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
2 months ago

Kisan ƙare dangi da ƴan ta’adda ke yi a Arewacin Nijeriya tare da cin karensu ba babbaka ya zama silar tarwatsa ɗimbin al’umma daga garuruwan su a muhallan su domin tsira da rai a bisa ga yadda yankunan su suka zama lahira kusa.

Yadda mayaƙan Boko- Haram a Arewa- Maso- Gabas da ɓarayin daji a Arewa Maso- Yamma da Arewa ta -Tsakiya suke ƙunar bakin wake, ƙone garuruwa, garkuwa da mutane da hanawa manoma noma albarkatun gona ba tare da hukumomin da lamarin ya shafa sun kawo ƙarshen gawurtacciyar matsalar ba tuni miliyoyin jama’a suka zama ƴan gudun hijira a cikin ƙasar su.

A kasafin kuɗin shekarar 2026, Gwamnatin Tarayya ta ware tsabar zunzurutun kuɗi naira na gugar naira har tirliliyan 5 da bilyan 41 domin kawar da matsalar tsaro wadda a 2025 aka keɓe naira tirliyan 4 da bilyan 9, haka ma a 2024 an keɓe naira tirliyan 3 da bilyan 85 sai dai har yanzu al’ummar ƙasa na ƙorafin ba su ga canji a ƙasa ba.

ADVERTISEMENT

Da yawan jama’a na nuna damuwa kan duk da maƙuddan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro da ƙwarewar jami’an sojojin Nijeriya amma ƴan ta’adda sun rinjaye su ba tare da sun shawo kan matsalar ba ta yadda a yau hatta jami’an tsaro ba su tsira daga hannun ƴan ta’adda ba.

Nijeriya na fuskantar yawaitar ƴan gudun hijira ta yadda hukumomin jin ƙai ke gargaɗin cewa rikita- rikitar da ke ruruwa na ƙara bazuwa fiye da wuraren da aka saba fama, lamarin da ke jefa rayuwar miliyoyin mutane cikin haɗari.

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

A dalilin tarwatsa garuruwa, miliyoyin al’umma sun tarwatse sun warwastu a yankuna da dama a matsayin ƴan gudun hijira waɗanda wasu ke a ƙarƙashin cibiyoyin da gwamnati ta assasa da ke da rajista a yayin wasu ke a a wasu wuraren a zaman kan su a cikin ƙunchi.

Bayanai daga ofishin majalisar ɗinkin duniya da ke kula da ƴan gudun hijira ya bayyana cewar Nijeriya na da kusan mutane miliyan 3.5 zuwa 3.7 da suka rasa muhallansu a cikin a shekarar 2025–2026.

An tattara alƙaluma ne tare da haɗin guiwar ƙungiyar kula da ƴan gudun hijira ta duniya da hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da kuma ofishin Kwamishinan kula da ƴan gudun hijira na majalisar ɗinkin duniya.

Bayanan sun nuna adadin mutane sama da miliyan uku da suka rasa muhallansu ya sanya Nijeriya a cikin jerin ƙasashen da ke da mafi yawan masu gudun hijira a nahiyar Afurka.

Alƙaluman ƙididdigar sun nuna Arewa- maso- Gabas na da kusan mutane miliyan 2.25 da ke gudun hijira waɗanda galibin su sun bar gidajen su a sakamon rikiciin Boko- Haram da suka kwashe tsayin shekaru suna cin karensu ba babbaka.

Haka ma yankin Arewa- maso- Yamma da ke fama da hare- haren ta’addancin ɓarayin daji da garkuwa da mutane ne ke da kaso na biyu da aƙalla kusan mutane 718,126, sai kuma Arewa ta Tsakiya da ke da adadin mutane 604,640 da suka ƙauracewa gidajensu domin tsira da rai.

Sai dai wasu rahotanni sun nuna cewar babu tabbacin samun sahihan alƙaluman ƙididdigar ƴan gudun hijira domin ƙididdigar na iya samun tangarɗa saboda ba dukkanin ƴan gudun hijira ne ke zaune a sansanonin da ke da rajista ba, haka ma su kan sauya matsugunni daga wannan zuwa wancan, akwai kuma bambancin hanyoyin ƙididdiga, haka ma sababbin hare- hare na iya canza alƙaluman ƙididdigar.

Hukumar kula da ƴan gudun hijira da ƴan ci rani a ƙarƙashin jagorancin Tijjani Aliyu Ahmed ita ce babbar hukuma a Nijeriya da ke kula da lamurran neman mafaka tare da sa ido daga hukumar hana shige da fice.

An kafa hukumar ne a shekarar 1989, a lokacin mulkin Shugaba Ibrahim Babangida, hasalima hukumar ta bayyana cewar an ƙirƙire ta ne domin “tabbatar da kare haƙƙin ƴan gudun hijira da masu neman mafaka tare da ba su tallafin da suke buƙata domin gudanar da ayuwa cikin tsaro da mutunci.”

‘Yan gudun hijira na fuskantar ɗimbin matsalolin da suka dabaibaye rayuwarsu suka hana masu walwala da jin daɗi a sansanonin gudun hijira daban- daban waɗanda suke fatar samun agaji da kulawar musamman gabanin fita daga ƙangin da suke ciki ta hanyar komawa gidajen su. 

Cinkoson jama’a a sansanonin gudun hijira da rashin tsafta kan haddasa yaɗuwar cututtuka kamar kwalara da zazzabin cizon sauro tare da matsanancin rashin abinci mai gina jiki musamman ga ƙananan yara.

Tantin wucin- gadi a wasu sansanonin gudun hijira ko kaɗan ba su kare mabuƙatan daga tsananin yanayi ta yadda a lokacin sanyi suke fuskantar tsananin sanyi, yayin da a lokacin damina kuma ambaliya ke shafar su sosai. A yanzu haka mafi yawan sansanin gudun hijira babu ma maganar tanti ko wata kariyar da suke samu.

Bugu da ƙari mata da ƴan mata a sansanonin gudun hijira na fuskantar barazanar sacewa, fyaɗe da cin zarafi, har ma a wasu lokuta ba su da zaɓi face bayar da jikin su domin samun abinci, hakan ya tilastawa wasu da dama shiga bahaguwar hanyar karuwancii.

Baya ga wannan dubban ƙananan yara ba sa samun damar zuwa makaranta a sansanonin gudun hijira. A wasu sansanonin a kan samu wasu da ke zuwa suna sadaukar da lokacin su wajen karantar da yaran, sai dai galibi ba wani ƙwaƙƙwaran karatu suke samu ba.

Rufe sansanoni da gwamnati ke yi tare da tilasta mayar da ƴan gudun hijira ba tare da samar da ingantaccen matsuguni ko hanyoyin samun abin yi ba, kan ƙara jefa dubban mutane cikin ƙunchi da talauci, musamman waɗanda aka mayar zuwa wurare marasa tsaro.

Tsarin magudanan ruwa ta hanyar yin bayan gida a fili na haifar da barazana mai tsanani ga lafiyar jama’a, yayin da samun tsaftataccen ruwa da ingantattun hanyoyin kula da tsafta da muhalli ke ci- gaba da kasancewa babban ƙalubale a sansanonin.

Haka ma rashin wadataccen abinci babbar matsala ce mai zaman kan ta musamman ga al’ummomin da a baya suke dogaro da kan su ta hanyar noma amma a yanzu sun koma gaba ɗaya suna jiran tallafin abinci daga waje wanda kuma ba ya da tabbas.

Wata babbar matsalar da ƴan gudun hijira ke fuskanta shine yadda gwamnatoci ke kasa yin hoɓɓasar da ta kamata domin mayar da su garuruwan su ta hanyar samar masu ingantaccen tsaro da kuma gazawa wajen samar masu sabbin matsuguni.

A ƙoƙarin bayar da kulawa ga waɗannan matsalolin, Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da tsare-tsare da manufofi daban-daban domin taimakawa ƴan gudun hijira domin sauƙaƙawa rayuwarsu musamman a jihohin da ke fama da rikice-rikice.

Daga cikin shirye-shiryen akwai Tsarin Gaggawa na 2026–2028 wanda aka ƙaddamar tare da haɗin guiiwar Tarayyar Turai da ƙungiyar ƴan gudun hijira ta duniya domin samar da matsuguni, ruwa mai tsafta da tallafin jin ƙai ga ƴan gudan hijira.

Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta goyi bayan aiwatar da wasu manufofin kan ƴan gudun hijira tare da fara aiwatar da su a jihohin Katsina da Zamfara domin samar da hanyoyin inganta rayuwarsu, ba su muhalli, tallafin sana’oi domin su ci-gaba da rayuwa a cikin aminci.

Bugu da ƙari a wannan shekarar, gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin jin ƙai da magance talauci ta hanyar haɗa kai wajen yaƙi da talauci da taimakon gaggawa ga al’umma masu rauni ciki har da ƴan gudun hijira da ke warwatse a cikin al’umma.

A bisa ga yadda gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da manufofii da tsare- tsaren kula da ƴan gudun hijira a ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan hukumar kula da ƴan gudun hijira da ci- rani na ƙasa, Tijjani Aliyu Ahmed, ya bayyana cewar hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya ta inganta rayuwar waɗanda matsalar ta shafa.

A ƙarkashin jagorancinsa, an fara aiwatar da tsare-tsare mayar da ƴan gudun hijira gida da kuma sake tsugunar da su tare da gina sabbin matsugunai, horas da sana’o’i da kuma inganta haɗin guiwar hukumomi.

Duk da haka LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar ƴan gudun hijira dama na kukan rashin kulawa yadda ya kamata daga gwamnati da hukumomin da lamarin ya shafa ta yadda galibi ba su da zaɓi face yawon bara domin samun abin da za su ci tare da kula da ƴaƴan su.

Gwamnatin Borno a ƙarkashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum na daga cikin waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen kula da ƴan gudun hijira domin a cikin ƴan shekaru, gwamnatin ta mayar da hankali kan rufe sansanonin ƴan gudun hijira a Maiduguri tare da ƙarfafa musu guiwar komawa garuruwan su na asali.

Gwamna Zulum ya sha bayyana cewa zaman dogon lokaci a sansani ba abu ne mai ɗorewa ba don haka komawa gida shi ne mafita ta din-din-din. A kan wannan gwamnatin ta: gina gidajen da ta sake tsugunar da mutane a garuruwa kamar Bama, Ngala da Dikwa tare da gyara da sake gina makarantu, asibitoci da muhimman ababen more rayuwa da kuma

haɗa kai da jami’an tsaro domin inganta tsaro a yankunan da aka sake tsugunar da jama’a.

Gidauniyar ASSATAHIR ta yi fice wajen sanyayawa marasa galihu musamman marayu, mata da ƙananan yara, ta bayar da himma wajen bayar da gagarumar gudunmuwa wajen kawar da matsalolin ƴan gudun hijira da inganta jin daɗin su ta hanyar tallafa masu a lokacin da suka fi buƙatar agaji.

Gidauniyar ASSATAHIR wadda Malam Aliyu Sidi Attahir ya assasa kan ziyarci sansanonin gudun hijira da ke Sakkwato musamman a Ramen Kura da Guiwa Eka tare da jajanta masu kan halin da suke ciki tare da ba su tallafin musamman domin sauƙaƙawa halin da suke ciki.

Ɗaya daga cikin ƴan gudun hijira a Sakkwato, Abubakar Hassan ya bayyana cewar yadda Gidauniyar ASSATAHIR ke ƙoƙarin share masu hawaye da za a samu ire- iren ƙungiyoyi masu zaman kan su da za su riƙa bayar da kulawar musamman ga ƴan gudun hijira da matsalolin su sun zama tarihi.

A birnin tarayya, Idriss Ibrahim Halilu shine ke kula kuma kakakin sansanonin ƴan gudun hijira 18 da ke Abuja ya kuma bayyana cewa kusan kashi 98 cikin 100 na tallafin abinci da kayan more rayuwa da sansanonin gudun hijira ke samu na fitowa ne daga hannun mutane masu zaman kansu yana cewar  rawar da gwamnati ke takawa a wannan fanni ƙalilan ce.

A ra’ayin wani ɗan gudun hijira a Zamfara, Haruna Magaji ya bayyana cewar “Mun jima muna rayuwa cikin wahala domin taimako daga gwamnati ba ya zuwa akai-akai kuma idan ya zo ma ba zai wadace mu ba. Yawancinmu muna dogaro ne da taimakon jama’a ko ƙungiyoyi masu zaman kansu. Don haka muna buƙatar gwamnati ta ƙara kulawa da mu musamman wajen abinci, lafiya da ilimi ga ƴaƴan mu.”

Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ postsBio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Taƙaddamar Kafa Hukumar Bogi: Tinubu Ya Umarci A Yi Binciken Ƙwaƙwaf
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Shekara 200 Bayan Shehu Ɗan Fodiyo: Hubbarensa Na Ci Gaba Zama Wajen Ziyara Da Neman Tabarruki
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Damunar Bana: Yadda Gwamnati Da Manoma Ke Tunkarar Barazanar Ƴan Ta’adda
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

MASU ALAKA

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu
Labarai

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi
Labarai

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
Next Post
Ya Dace A Rike Damarmakin “Shekarar Kasar Sin” Na Taron APEC

Ya Dace A Rike Damarmakin “Shekarar Kasar Sin” Na Taron APEC

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.