ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu

by Sani Anwar
5 months ago
Kwankwaso

A wannan mako da muke ciki ne, wakilinmu SANI ANWAR, ya zanta da Ɗan Majalisar Jihar Kano, mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Nassarawa, Injiniya Yusuf Bello Aliyu, wanda tattaunawar tasu ta ƙunshi batutuwa da dama, ciki har da batun zarge-zargen da suke yi wa gwamnan Jihar Kano, na cin amanar jagoransu na Kwankwasiyya da sauran wasu batutuwa da dama da suka shafi siyasar Kano da ma ƙasa baki-ɗaya. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Ko za ka gabatarwa da masu karatu kanka?

Sunana Hon. Injiniya Yusuf Bello Aliyu, ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Nassarawa, a zauren majalisa ta goma a Jihar Kano.

ADVERTISEMENT

Kwankwaso

Za mu so ka ɗan tsakuro mana kaɗan daga cikin gwagwarmayar siyasarka, sannan wane ne jagoranka na siyasa?

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

  • Binciken CGTN: Yaki Ya Mayar Da Amurka Saniyar Ware Fiye Da Kowane Lokaci
  • Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

Alhamdu lillahi, muna gode wa Allah SWT, mai yin yadda ya so a lokacin da ya so. Tun muna jami’a muka fara gwagwarmayar siyasa, ba zan manta ba, muna jami’ar Wudil, na fara riƙe muƙamin ‘Social Director na Ciɓil Engineering’, daga bisani kuma na zama ‘Welfare Officer na Nigerian Uniɓersity of Engineering Student’, daga nan kuma na yi Sanata har sau biyu a ƙungiyar NAKSS (Kano State Sutudents Association), na kuma riƙe muƙamin ‘Speaker’ sau biyu a lokacin da ina aji huɗu a jami’ar.

A lokacin da ina aji huɗun dai a jami’a, akwai ƙungiya ta Kwankwasiyya a mazaɓata ta Gama da na tsunduma, muke kuma ba da gudunmawa a ƙungiyance. Bayan na kammala jami’a, sai na ɗora daga inda muka tsaya, wato wannan tsari na Kwankwasiyya da har gobe muke ciki.

A matsayina na Injina, a lokacin da nake aiki da kamfanonin gine-gine, akwai manya-manyan ayyuka da muka yi, lokacin da mai girma Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yana gwamna. Mu ne muka gina jami’ar North West da sauran wasu manya-manya ayyuka, ina yin wannan aiki, ina kuma yin siyasa. Daga nan ne, sai na kafa wata ƙungiya na sa mata suna ‘MB Foundation’, a ƙarƙashin gidauniyar ne muke bai wa matasa aikin yi tare da bayar da tallafi, musamman ga waɗanda ba su da abin yi kwata-kwata.

Wannan dalili ne ya haska mana buƙatar shiga gwamnati, ta hanyar yin takara, duk da cewa; a lokacin ban ma san wace takara ya kamata na yi ba, kwamitin da muke zama da su a wannan ƙungiya ne suka ce lallai sai na yi takarar ɗan majalisar tarayya. Bayan nan ne, muka sake fitowa muka kafa wata ƙungiyar mai suna ‘Kwankwasiyya Youth Mobilization’, wadda har yanzu tana nan da ita muke yin aiki a ko’ina, tun daga matakin jiha, ƙaramar hukuma da kuma mazaɓa.

Bayan mun shiga jam’iyyar NNPP ne, Allah ya ba mu nasara, duk da ba mu samu takarar majalisar tarayya ba, sai muka samu ta majalisar jiha, inda muka samu nasarar cin zaɓe da ƙuri’u masu gagarumin rinjaye. Domin kuwa, a duk Kano, babu ɗan majalisar da ya samu yawan ƙuri’un da na samu da suka kai kimanin sama da 50,000, wanda yake biye min, ratata da shi ta ƙuri’a ta kai kimanin 25,000, shi yasa ko kutu ma bai kai ƙara ba, saboda zaɓe ne na kece raini.

Haka zalika, ba ni da wani jagora ko mudubi da muke kallo, tamkar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, dukkannin nasarorin da muka samu, albarkacinsa muka ci, domin shi ne ya ba mu takara, ya yi gwagwarmayar tallata mu har muka samu gwamnati. Shi yasa na sha faɗa cewa, ko yanzu ya umarce ni da kada na fito takara, to wallahi zan haƙura ba zan fito ba.

Kwankwaso
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu

Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.