ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Har Yanzu Manyan Mutane Na Samun Rakiyar Ƴansanda Duk Da Haramcin Shugaban Ƙasa

by Rabi'u Ali Indabawa
3 weeks ago
Mutane

Umarnin shugaban ƙasa na janye jami’an ƴansanda da aka ɗora wa mutane masu muhimmanci na musamman (ƁIPs) waɗanda ba su da izini, yana fuskantar aiwatarwa iri-iri a jihohi daban-daban. Binciken da LEADERSHIP Sunday ta gudanar ya nuna cewa ƴan siyasa da dama, ƴan kasuwa da sauran manyan mutane har yanzu suna tafiya tare da rakiyar ƴansanda duk da wannan umarni.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ne a ranar 23 ga Nuwamba, 2025, yayin wani babban taron tsaro da aka gudanar a Abuja.

Ya ce ya kamata a janye jami’an ƴansanda da aka ɗora wa aikin gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya, sannan a mayar da su aikin tsaron al’umma na yau da kullum.

ADVERTISEMENT

Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa ƁIPs da ke buƙatar rakiyar jami’an tsaro ya kamata su nemi jami’an ɗauke da makamai daga Hukumar Tsaron Farar Hula, Gyaran Hali, Kashe Gobara da Sabis na Kurkuku ta Nijeriya (NSCDC).

Umarnin, wanda Rundunar Ƴansandan Nijeriya (NPF) ta ƙarfafa ta hanyar umarnin aiki, ya buƙaci a gaggauta janye jami’an ƴansanda daga rakiyar ƁIPs waɗanda ba su da izini. Haka kuma, an bayar da umarnin kama jami’an ƴansanda da aka samu suna yin aikin rakiyar ƁIPs ba bisa ƙa’ida ba.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Domin tabbatar da bin wannan umarni, Sufeto-Janar na Ƴansanda (IGP) ya umurci kwamandojin tsaron filayen jiragen sama na Abuja da Legas da su kama duk wani jami’in ɗansanda da aka gani yana rakiyar ƁIP da ba shi da izini.

Sai dai, binciken LEADERSHIP Sunday a wasu jihohi ya nuna cewa duk da cewa ana aiwatar da umarnin a ƙa’ida, aiwatar da shi a aikace ba ya tafiya daidai a ko’ina. An bayyana matsalolin tsaro da kuma wasu keɓantattun izini a matsayin dalilan da suka sa har yanzu ake ci gaba da amfani da rakiyar ƴansanda.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan (PPRO), Henry Okoye, ya ce:

“Mun janye sama da kashi 60 cikin 100 na jami’an ƴansanda da aka ɗora wa ƴan siyasa, ƴan kasuwa da sarakunan gargajiya waɗanda ba su cancanci samun wannan kariya ba. Sai dai gwamna, mataimakin gwamna, kakakin majalisa, babban jojin jihar da sarakunan gargajiya masu daraja ta farko waɗanda ke fuskantar barazanar tsaro ne kawai suka ci gaba da samun kariyar da doka ta tanada.”

Mutane
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Mutane

2027: INEC Za Ta Yi Amfani Da Fasahar Zamani Don Sa Ido Kan Kuɗaɗen Yaƙin Neman Zaɓe

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.