ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: INEC Za Ta Yi Amfani Da Fasahar Zamani Don Sa Ido Kan Kuɗaɗen Yaƙin Neman Zaɓe

by Yusuf Shuaibu
2 months ago
INEC

Kafin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki a ranar 19 ga Agusta, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta yi amfani da sabbin hanyoyin fasaha don hana jam’iyyun siyasa kaucewa iyakokin kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe kamar yadda dokar zaɓe ta 2026 ta tanada.

Wannan ya biyo bayan iƙirarin jam’iyyar adawa ta PDP cewa ƙoƙarin rage kashe kuɗi wajen yaƙin neman zaɓe ba zai yiwu ba. Amma jam’iyyar mai mulki ta APC ta ce za ta bi ƙa’idojin dokar zaɓe ta 2026 kan kashe kuɗi a lokacin yaƙin neman zaɓe, yayin da jam’iyyar LP ta ce yaƙin neman zaɓenta ba su da manyan masu kashe kuɗi, don haka ba su cikin haɗarin karya dokar zaɓe.

INEC, wanda ta yi magana ta bakin mataimakin darakta mai kula harkokin sadarwa, Wilfred Osilama Ifogah, ya ce sun riga sun kafa tsarin da zai sa ido kan kuɗaɗen da jam’iyyun siyasa za su kashe wajen yaƙin neman zaɓe.

ADVERTISEMENT

“Muna da wata sashen da aka ɗora wa alhakkin bin diddigin da sa ido kan ayyukan jam’iyyun siyasa, ciki har da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe. Sashen, wanda dokar zaɓe da ƙa’idoji suka jagoranta, zai gudanar da wannan aiki. Sunan sashen shi ne, sashen sa ido kan zaɓe da jam’iyyun siyasa (EPM), in ji shi.”

Har ila yau, yaba wa hukumar bisa ƙirƙirar sashin bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe kamar yadda dokar zaɓe ta shekara ta 2026 ta tanada.

LABARAI MASU NASABA

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo

Kwamishina kuma shugaban kwamitin kula da sashin sa ido kan zaɓe (EPMC), Dakta Baba Bila, y ace tuni ƙa’idoji da dokokin zaɓe ta shekarar 2022 sun riga sun rufe rahoton kuɗaɗen da za a kashe wajen yaƙin neman zaɓe.

Dakta Bila ya sake tabbatar da ƙudurin hukumar don ƙarfafa gaskiya da kafin zaɓen 2027 ta hanyar gyare-gyaren da fasahar zamani ke jagoranta.

“Kuɗaɗen da ake kashewa a siyasa yana ɗaya daga cikin muhimman ginshiƙai na kowace tsarin dimokuraɗiyya. Amincewar jama’a ga zaɓe yana da alaƙa da bayyananniyar gaskiya da ɗawainiya da ke tattare da kuɗin yaƙin neman zaɓe da jam’iyyun siyasa ke kashewa da bin ƙa’idoji,” in ji shi.

A watan Maris, Shugaban INEC, Joash Amupitan, ya faɗi haka a wani bitar fasaha na tsawon kwanaki uku da gidauniyar ‘Westminster Foundation for Democracy’ (WFD) ya ɗauki nauyi, ya ce sabbin dokokin zaɓe ta 2026 da aka sabunta za su kawo ƙa’idoji masu tsauri don bayyana kuɗaɗen da ake kashewa wajen yaƙin neman zaɓe.

A watan Mayu, kwamishinan zaɓe na Jihar Legas, Farfesa Ayobami Salami, ya ce za a saka idanu sosai kan yadda jam’iyyu suke kashe kuɗaɗensu a yayin yaƙin neman zaɓen 2027. Ya yi wannan bayani ne a lokacin wani toro ga shugabannin sassa, EPM, daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja da shugabannin jam’iyyu, kan tsarin rahoton kuɗi da binciken jam’iyyu (PFRAS), da dokokin zaɓe ta 2026 ya tanada.

Jam’iyyar APC ta ce za ta tabbatar da cewa duk ƴan takararta da ke neman muƙaman siyasa a zaɓen suna bin dokar zaɓe.

Daraktan yaɗa labarai na jam’iyya, Bala Ibrahim ya bayar da tabbaci a ƙarshen mako a wata hira da ƴan jarida.

Binciken ya nuna cewa bisa ƙa’idojin dokar zaɓe ta 2026, akwai wani shinge ga ƴan takara na wasu muƙamai.

Sabuwar dokar ta ninka kuɗaɗe yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, daga naira biliyan 5 zuwa naira biliyan 10, sannan ta kuma ƙara iyakar gudummawar mutum ɗaya daga naira miliyan 50 zuwa naira miliyan 500.

Dokar ta ƙara kuɗin da za a iya kashewa wajen neman kujeran gwamna daga naira biliya 1 zuwa naira biliyan 3, yayin da ƴan takarar sanata za su iya kashe naira miliyan 500.

Kafin fara yaƙin neman zaɓe, jam’iyyun adawa sun zargi gwamnonin da ke ƙarƙashin jam’iyyar APC da yin watsi da rage kuɗi daga rabon kowane wata na asusun tarayya na jihohinsu a matsayin kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe. Haka nan sun ƙara zargin cewa ana tura irin wannan kuɗaɗe zuwa jakadu na shirin sabuwar fata da dandamalin yaƙin neman sake zaɓen Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

A halin yanzu, bincike ya nuna cewa ƴan siyasa da jam’iyyunsu suna ƙirƙirar hanyoyi masu waya na kashe fiye da mafi ƙarancin adadin kuɗaɗe da dokar zaɓe ta tanada a lokutan yaƙin neman zaɓe.

Majiyoyi sun shaida cewa jam’iyyun siyasa da ƴan siyasa suna kafa ƙungiyoyin don tallata muradunsu kuma suna ɗaukar nauyin ayyuka da dama waɗanda ba lallai su zama na jam’iyya ko na ɗan takara ba kai tsaye.

Sai dai, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP ya bayyana kowane yunƙuri na rage kashe kuɗi a zaɓe a matsayin abin dariya.

A cewar jam’iyyar, yayin da ra’ayin daidaita kashe kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe abu ne mai kyau, a lokaci guda kuma ba zai yiwu a cimma shi ba.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Kwamared Ini Ememobong, wanda ya yi magana kan matsayin jam’iyyar, ya nuna cewa gwamnati kanta, wadda ke da alhakkin aiwatarwa ta riga ta karya doka.

Ememobong ya kawo babban kuɗaɗe da gwamnatocin jihohi daban-daban ke sanya wa talla a matsayin misali na yadda dokar za ta gaza tun da farko.

Amma jam’iyyar LP ta ce ba ta damu da kuɗin yaƙin neman zaɓe ko wuce iyaka ba saboda ta shirya wani tsari da ba ya buƙatar kashe kuɗi masu yawa.

“Ba mu ma tunanin wuce iyakar da dokar zaɓe ta tanada, saboda muna da tsari da muka shirya don kula da kuɗaɗen ƴan takararmu da na jam’iyya a lokacin kamfen,” in ji sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Mista Ken Asogwa.

INEC
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
     2027: Ƙaruwar Ta’addancin Siyasa Na Haifar Da Fargabar Yaƙin Neman Zaɓe A Jihohi
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

MASU ALAKA

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
Siyasa

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026
Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo
Siyasa

Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo

October 22, 2026
Wike Ya Buƙaci ’Yan Jam’iyyar PDP A Abuja Su Goyi Bayan Tinubu da ’Yan Takarar APC A 2027
Siyasa

Wike Ya Buƙaci ’Yan Jam’iyyar PDP A Abuja Su Goyi Bayan Tinubu da ’Yan Takarar APC A 2027

October 22, 2026
Next Post
INEC

Nasarar Adeleke Ta Nuna Masu Zaɓe Ke Yanke Hukunci - Reset Nigeria Movement

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.