ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Sabbin Matakan Dakile Haɗura A Titin Bypass

by Shehu Yahaya and Sulaiman
2 months ago
Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta ƙara ɗaukar sabbin matakai domin rage yawan haɗurran da ke faruwa a babbar hanyar Nnamdi Azikiwe (western bypass) domin kare rayuwakar Al’umma masu amfani da hanyar.

A Wani taron masu ruwa da tsaki wanda ma’aikatar yada labarai da Al’adu ta Jihar Kaduna ta shirya wanda aka tattaro shugabannin gargajiya, hukumomin tsaro, Hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) , kamfanonin da ke aikin hanyar da ƙungiyoyin direbobi, domin cimma matsaya kan yadda za’a kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da ingantaccen tsaro a kan hanyar.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin Sarkin Ruwan Zazzau, Alhaji Tahir Mahmoud, Hakimin Tudun Wada, inda mahalarta suka tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen rage haɗurran da ke yawaita a kan wannan muhimmiyar hanya.

ADVERTISEMENT

A jawabinsa, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, wanda Babban Sakataren Ma’aikatar Iliya Duniya ya wakiltar, ya ce gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Sanata Uba Sani ta kafa kwamitin karta ta kwana domin tabbatar da rage yawan haɗurra a kan hanyar. Ya ce gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar duk wani mataki da zai tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Malam Ahmed Maiyaki ya kuma yaba da irin gudunmawar da sarakunan gargajiya da limamai ke bayarwa wajen wayar da kan jama’a da goyon bayan manufofin gwamnatin jihar na inganta tsaro da kiyaye doka a kan hanyoyi.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A nasa jawabin, wakilin rukunin masana’antun Kamfanin Dangote Injiniya Jonathan Magoro, ya bayyana cewa ana sa ran kammala aikin babbar hanyar nan da watan Disamba, tare da sanya alamun rage gudu a wuraren da aka gano suna da haɗari domin rage afkuwar hatsarori.Yace sun samar da sabbin matakan rage hadura Akan hanyar wadanda suka hada da sanya alamun rage gudu da sanya ido wajen ganin masu amfani da hanyar suna bin dokoki yadda ya kamata. Suma Kamfanin Dantata wadanda aka suke kwangilar aikin hanyar sunce suna aiki kafaɗa da kafaɗa da masu riƙe da sarautun gargajiya wajen tabbatar da nasarar aikin.

Sun bayyana cewa bayan kammala aikin za a girka fitilun kan titi, sannan an tantance wurare tara da ke da haɗari inda za a sanya alamun rage gudu.A nasa bangaren, Shugaban kungiyar masu manyan Motoci ta kasa (NARTO) rehsen jihar Kaduna Alhaji Babangida Ja’afar, ya yi kira ga masu amfani da hanya su guji ganganci, yana mai cewa tukin babbar mota ya bambanta da na ƙarama.

Ya buƙaci limamai da shugabannin gargajiya su ƙara wayar da kan jama’a kan bin dokokin hanya da kuma kaucewa daukar doka a hannunsu yayin da aka samu hadari. Ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu ke ƙona manyan motocin da ke ɗauke da iskar gas ko man fetur bayan haddasa haɗari, cewa hakan na iya haddasa mummunar gobara da ƙarin asarar rayuka da dukiyoyi.

Haka kuma ya gargadi direbobin ƙananan motoci da su daina shiga gaban tireloli ba tare da isasshen tazara ba saboda hatsarin da hakan ke haifarwa.

Kungiyoyin masu babura masu ƙafa uku (Keke Napep) sun bayyana gamsuwarsu da matakan da gwamnatin Jihar Kaduna ke ɗauka domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a babbar hanyar Nnamdi Azikiwe. Sun kuma yi alƙawarin haɗa kai da gwamnati wajen tabbatar da cikakken aiwatar da duk shawarwari da matakan da aka cimma a taron.

Kaduna
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna
Kaduna
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Tsohon Mataimakin Babban Sakataren MDD Ya Yaba Wa Dabarun Sin Kan Mulkin Kasa

Tsohon Mataimakin Babban Sakataren MDD Ya Yaba Wa Dabarun Sin Kan Mulkin Kasa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.