ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Manoma 2,930 Buhun Taki 11,720 A Abuja

by Abubakar Abba
3 weeks ago
taki

Gwamnatin tarayya, ta yunƙuro kan ƙoƙarin da take ci gaba da yi na ƙara samar da wadataccen abinci a ƙasar.

Wannan na zuwa ne, yayin da gwamnatin ta raba wa ƙananan manoma 2,930 buhunhunan takin zamani 11,720 a Abuja.

Hukumar samar da kuɗin tallafi ga manoma ta ƙasa (NADF) ce ta jagoranci rabar da takin, wanda aka ƙaddamar da rabonsa a Abuja.

ADVERTISEMENT

A yayin ƙaddamarwar, ƙaramar ministar birnin, Mariya Mahmoud, ta jaddada ƙoƙarin gwamnatin, na cimma burin samar da wadataccen abinci a ƙasar, ta hanyar samar da ɗauki ga fannin.

Ta ce, wannan ɗaukin, zai taimaka matuƙa wajen inganta rayuwar manoman da suka amfana da takin.

LABARAI MASU NASABA

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu

A cewarta, wannan ɗaukin, ya nuna irin mayar da hankalin da gwamnatin Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ke ci gaba da yi na ƙara ƙarfafa tsarin samar da wadataccen abinci da rage matsalolin da manoman ƙasar ke fuskanta a fannin.

Ta yi nuni da cewa, fannin aikin noma ne kan gaba, wajen haɓaka tattalin arzƙin ƙasar, wanda ta ce; tallafa wa manoman, wani ƙarin yunƙuri ne, na ƙara samar da wadataccen abinci a ƙasar.

Sannan ta yaba wa Shugaba Tinubu, musammamn kan ƙirƙiro da tsare-tsaren da suka taimaka, na samun rancen kuɗaɗen yin noma.

Ta buƙaci manoman da suka amfana da wannan tallafi, da su amfani da shi, yadda ya dace tare da kuma rungumar yin noma da kayan aiki na zamani, musamman domin su rinƙa yin girbi mai yawa.

Ministar ta bayar da tabbacin cewa, mahukuntan birnin, za su ci gaba da yin haɗaka da abokan haɗaka da sauran hukumomi da kuma masu ruwa da tsaki, domin samar da kayan aiki ga manoma da kuma horas da su.

A jawabinsa tun da farko, Shugaban Hukumar ta NADF, Injiniya Mohammed Ibrahim ya ce; wannan shirin ya nuna irin mayar da hakali da gwamnatin ke ci gaba da yi, na ƙara samar da wadataccen abinci a ƙasar da ƙara haɓaka tattalin arziƙin ƙasar.

Ya ce, ta hanyar aikin noma, ana iya samar da ayyukan yi wanda zai ƙara inganta rayuwar miliyoyin ƴan ƙasa.

Ibrahim ya ƙara da cewa, an tsara wannan shiri ne, domin tabbatar da an samar da ingantaccen takin ga manoman, musamman domin su tunkari noman kakar bana a cikin nasara.

Ya ci gaba da cewa, wannan ɗaukin, ana sa ran zai rage wa manoman tsadar aikin noma, wanda hakan zai ƙara ba su damar yin girbi mai matuƙar yawa.

taki
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Dalilin Da Ya Sa Kungiyar NCTR Ta Jinjina Wa Shugaban NPA
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari A Kan Wasu Cututtuka Da Ke Shafar Dabbobi Lokacin Damina
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu
Noma Da Kiwo

Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu

July 4, 2026
Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana
Noma Da Kiwo

Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana

July 3, 2026
Next Post
taki

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

LABARAI MASU NASABA

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

July 17, 2026
Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti

Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti

July 17, 2026
Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima

Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima

July 17, 2026
Kwamitin Ba Da Shawara Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Na Dandalin BRI Ya Yi Taronsa Na 2026

Kwamitin Ba Da Shawara Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Na Dandalin BRI Ya Yi Taronsa Na 2026

July 17, 2026
Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

July 17, 2026
Yawan Mu’amalar Kudi Tsakanin Mazauna Sin Da ’Yan Kasashen Waje Ya Hau Wani Sabon Matsayi A Tarihi

Yawan Mu’amalar Kudi Tsakanin Mazauna Sin Da ’Yan Kasashen Waje Ya Hau Wani Sabon Matsayi A Tarihi

July 17, 2026
Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi

Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi

July 17, 2026
Matatar Man Dangote Ta Dawo Sayar Da Fetur A Dala

Matatar Man Dangote Ta Dawo Sayar Da Fetur A Dala

July 17, 2026
Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

July 17, 2026
Falalar Salatut Tasbihi

Falalar Salatut Tasbihi

July 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.