ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jam’iyyun Adawa Na Cikin Tsoron Soke Rajistarsu – Baba-Ahmed

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Shugaban Jam’iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana fargaba kan yadda yanayin siyasar ƙasar ke ƙara tsananta, inda ya yi gargaɗin cewa jam’iyyun adawa a Nijeriya suna rayuwa cikin tsoron yiwuwar soke rajistarsu.

Yayin da yake jawabi a cikin wani shiri na gidan talabijin na Channels TV, Baba-Ahmed ya bayyana cewa abubuwan da ke faruwa a fagen siyasa da kuma hukunce-hukuncen kotu na baya-bayan nan sun ƙara jefa makomar jam’iyyun adawa cikin rashin tabbas.

Lokacin da aka tambaye shi ko jam’iyyarsa ta PRP tana tsoron soke rajistar, Baba-Ahmed ya amsa da cewa babu wata jam’iyyar adawa da ke kwana da idanuwanta biyu a rufe a halin yanzu, in ban da jam’iyyar APC mai mulki. Ya jaddada cewa kowace jam’iyyar adawa da ke da’awar cewa tana cikin kwanciyar hankali, to kuwa ba ta ɗauki harkar siyasar ƙasar da gaske ba, duba da yadda hukuncin Babbar Kotun Tarayya ta Lokoja ya soke rajistar jam’iyyar NDC a cikin makon nan.

ADVERTISEMENT

Baya ga batun rajista, Baba-Ahmed ya taɓo batun tsaron ƙasa, inda ya soki yunkurin gwamnatin tarayya na samar da ‘yansandan jihohi (state police). Ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kwashe shekaru uku tana jan kafa kan batun, kuma samar da su ba tare da an gyara tsarin rundunar ‘yansandan tarayya da sojoji ba, zai ƙara dagula matsalolin tsaron ƙasar ne kawai tare da ba wa gwamnoni damar yin abin da suka ga dama.

A ƙarshe, shugaban na PRP ya jaddada cewa akwai abubuwa da dama da Shugaba Tinubu zai iya yi da jami’an tsaron da ke ƙasa a halin yanzu domin kawo ƙarshen garkuwa da mutane da kashe-kashen da ke faruwa.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Game da tarihin jam’iyyar PRP kuwa, ya ƙaryata iƙirarin cewa jam’iyyar ta samo asali ne daga marigayi Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna, inda ya bayyana cewa a can baya ma jam’iyyar ta kasance ƙaya ce a jikin gwamnatin Sardaunan saboda adawa da siyasarsa.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Rage Farashin Mai Na Ɗangote: Dillalan Man Fetur Sun Yi Burus Da Sauya Nasu Farashin

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.