Ci gaba daga makon jiya
Shafi ne da ya saba zaƙulo muku fitattun jaruman finafinan hausa manya da ƙanana, daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood. A yau shafin ya yi cozali da wata fitacciyar jarumar wacce ta shahara ta ga jiya ta ga yau a cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood wato, FATI MUHAMMAD Inda ta warwarewa masu karatu zare da abawa game da cece-kucen da wasu ke yi na jita-jitan da aka yaɗa a kanta. Har ma da wasu bayanan da suka shafi rayuwarta.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar Jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Tsakanin harkar fim da kuma siyasa, wanne ne ki ke ganin ya fi kawo miki ci gaba a rayuwarki a yanzu?
Faɗa ma ɓata baki ne, amsa ma ko ban faɗa ba masu karatu za su bayar da amsa. Ai babu abin da ya kawon ci gaba irin fim, dalilin fim ne har ta kai ni ga samun nasarar shiga siyasa. Inda ace yau ban shiga fim duniya ta sanni ba to, da siyasar ma ba abin da zan tsinana musu. Ba ni da abin da ya wuce fim, zancen da nake har kwanan duniyar gobe zan rufe fuskata na saka niƙab amma mutane idan suka ji muryata za su ce Fati Muhammad, a ina suka san Fati Muhammad? a fim.
- Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo
- Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli
- Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus
- ’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP
- An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos
A cikin masana’antar Kannywood idan aka ce ki zab’i mutum uku, su wa za ki ɗauka, kuma me ya sa?
Abin da ban taɓa faɗa a jarida ba yau zan faɗa, na farko Ali Nuhu, shi mutum ne wanda muka fara ‘industry’ kullum ina faɗa, akwai alkhairansa da halayensa masu kyau, mutane suna yi masa mummunan fahimta wanda suke ganinsa daga nesa ba su san shi ba. Mutum ne me tausayi, wanda a rayuwa idan ya ganka cikin matsala yana ƙoƙarin bakin gwargwado ya ga ya fitar da kai ko bao yi maka 100% ba to, zai kamata ko da 60% ko70% to, ka ga kuwa duk mutumin da zai yi maka haka a rayuwa masoyinka ne. Ali Nuhu mutum ne na gari ina alfahari da shi. Mutum na biyu shi ne Dauda Kahutu Rarara shugaban ƙasar mawaƙa, shi ma mutum ne nagari wanda tsakanina da shi sai sam barka, ya taimaki rayuwata ko kuma na ce yana kan taimako na Allah ya ƙara masa basira da ɗaukaka. Sai na uku Ali Isah Jita, dama shi ƙani ne a gare ni tunda ƙanin tsohon mijina ne ƙanin zan kira shi suruki kuma, Ali Jita shi kansa ya taka rawar gani akan rayuwata kan yanayin da na ɗan tsinci kaina suna ɗaya daga ciki waɗannan mutum ukun suna dafa min. Allah ne ya haɗa ni da su kuma ba su kaɗai na sani a masana’antar ba.
Ali Jita yana da alaƙa da tsohon mijin da ki ka aura kenan?
Eh, ƙanin tsohon mijina ne da na taɓa aura na biyu Umar Kanu, uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Kuma ina da kyakkyawar alaƙa da Ali Isah Jita sosai da sosai.
Ya batun aure, shin kina da ra’ayin ƙara yin aure ko babu, sannan wanne irin namiji ki ke son ƙara aura?
[Dariya] Kai! Dole ma, aure ne ya haife ni fa, har yanzu a shekaruna ban wuce arba’in ba a duniya ba, zan so ace nayi aure na haifi tawa zuri’ar ina ganinsu a gabana sosai kuwa. Ko yanzu-yanzu Allah ya kawo miji kuma Allah yayi rabona ne zan yi aure domin shi ne darajar ‘ya mace. Duk kyanki, duk mulkinki, duk mutuncinki duk abin da ki ke taƙama, darajarki ɗakin miji. Saboda haka kawai jarrabawa ce da ƙaddara Allah ya ɗora min, kuma Allah ya sa na ci wannan jarrabawar kullum ina faɗa. Mijin da nake son aura me tsoron Allah wanda yake da ibada, wanda ubangiji Allah ya sa zai tausayina kuma in nayi ba daidai ba zai nusarshe ni cewar, wannan abin da ki ka yi kuskure ne ki gyara to, shi ne mijin da nake sha’awar na aura.
Wane irin abinci da abin sha ki ka fi so?
Ina son Tuwo musamman Tuwo miyar Kuka, ko ya kwana ya wuni zan ci shi. Abin sha na fi son ruwa.
Wane irin kaya ki ka fi son sakawa?
Ina son saka Abaya don ta fi daɗin sakawa, ba sai ka ta ɗaure-ɗauren ɗan kwali ba, sai dai na yafa mayafi. Sannan ina son saka Atamfa.
Wacce shawara za ki bawa masu ƙoƙarin shiga harkar fim?
Kullum ina faɗa su san da wacce zuciya za su shigo harkar, tunda sana’a ce. Mu sana’a muka ɗauke ta kuma har yanzu muna alfahari da ita, idana ka san sana’a za ka/ki zo to a san da zuciyar da za a zo da ita me kyau ce to, sai ka ga ka samu nasarar abin da ba ka tunani. Sannan shawara musamman mata kisan idan kin shigo ki riƙe mutuncinki da sana’ar ki hannu bibbiyu, ki riƙe amana, ki girmama iyayenki, ki san cewar umarnin mahaifinki za ki shigo harkar haka kai ma.
Ko akwai wata shawara da za ki bawa sauran jarumai masu taka rawa a yanzu cikin masana’antar Kannywood?
Shawarar da zan basu na farko sanin mutuncin na gaba, da sanin darajar na gaba, cika alƙawari. Idan aka ce an kira ki location ki tabbatar za ki zo akan lokaci, babu raina darakta, ko furodusa, ko jarumai iyaye musamman iyaye da suka haife ki ko wanda ma ba su haife ki ba, idan sun riga ki zuwa wannan masana’antar ki basu girmamawa da darajantawa.aka ce “bin na gaba – bin Allah” kai ma kana so a girmamaka wannan na iya sakawa mutuncinka da darajarka ya ƙaru, da kuma shigar mutunci.
Ko akwai wani saƙo da ki ke da shi ga sauran al’umma, har ma da masoyanki?
Mutanen masana’antar Kannywood maza da mata, ina so a riƙe harkar nan hannu bibbiyu kamar yadda na faɗa a baya, ka san sana’a ka zo yi, kuma a ƙara gyara tsaftace harkar ɗari bisa ɗari, wanda suke gurɓatattu a harkar a tankaɗe su a rairaye a watsar. A gyara harkar sosai, dan hausa fim ya tafi inda ba a tunani, wallahi duk wanda yake shiga fim ɗan baiwa ne saboda ba ilimi bane abun baiwa ce, wani duk iliminsa in ka saka masa kyamera ba zai iya yin abin da muke yi ba. Sannan masoyana ina godiya ina ganin saƙonninku , idan aka yi hira da ni Fati Muhammad yadda kuke nuna addu’o’inku da fatan alkhairi maza da mata, manya da yara wallahi ba ni da abin da zan biyaku da shi sai dai fatan alkhairi. Ina jin daɗi sosai kuma ina farinciki Allah ya bar ni da ku. Addu’ar nan dai da ku ke min ba zan daina cewa ku daina yi min ita ba, Allah ubangiji ya hayyu ya ƙayyum ya ba ni miji nagari wanda zai riƙe ni, ya riƙe maraici na, na rufawa kaina asiri na mutu cikin sutura. Kullum wannan addu’ar ita nake fata a wurinku kuma ina yi Allah kar ka ɗau rayuwar Fati Muhammad sai a gidan miji dan alfarmar Annabi, ina wannan fatan ina wannan addu’ar.
Ki gaishe da mutum biyar.
Na farko zan fara da babbar aminiyata Abida Muhammad, sai kuma Maijidda Abdulƙadir, ita ma ƙawara ce tunda tare muka yi Mujadala, sai Aunty Saima Muhammad wannan yayarmu ce, amman dole a gaishe ta, sai kuma Mansura Isah, sannan kuma sai Maryam Jankunne. Ba wai sauran ba na yi da su bane iya abin da aka buƙata ne kuma suna da yawa.
Muna matuƙar godiya
Ni ma na gode.















Discussion about this post