Hukumar Kwastam ta Kasa (NCS) ta bayyana sunayen mutanen da ake zargi da shigo da bindigogi ƙirar ‘Pump-Action’ har guda 399 ta tashar jirgin ruwa ta Tin Can Island da ke Jihar Legas. Babban Kwanturolan Hukumar, Bashir Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Legas, a lokacin da yake miƙa makaman a hukumance ga Cibiyar Kula da Ƙananan Makamai ta Ƙasa (NCCSALW).
Kwanturola Adeniyi ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin da cewa su ne Robert Eze da kuma Ejiogu Godson, inda ya tabbatar da cewa a halin yanzu dukkanin su biyun suna tsare. Ya ƙara da cewa ana sa ran gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas a ranar 25 ga watan Agustan 2026 domin fuskantar shari’a kan zargin shigo da makaman ba bisa ƙa’ida ba.
Da yake ƙarin haske kan yadda aka gano makaman, shugaban na kwastam ɗin ya bayyana cewa an wargaza sassan bindigogin ne da gangan tare da boye su a cikin kwantena da nufin gudanar da fasa-kwaurinsu ba tare da an gane ba. Sai dai binciken kwakwaf da jami’an hukumar suka gudanar a kan kwantenar ne ya kai ga gano waɗannan miyagun makamai.
Tuni dai aka miƙa waɗannan makamai ga Kodinetan Cibiyar NCCSALW, DIG Johnson Kokumo mai murabus. Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne Mai Shari’a Friday Ogazi na Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Godson da Eze na tsawon kwanaki 15, domin bai wa hukumar kwastam cikakkiyar damar kammala bincikenta kafin fara shari’arsu.














