ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukumar NDLEA Ta Lalata Sama Da Tan 12 Na Miyagun Ƙwayoyi A Kano

by Sani Anwar
2 months ago
Kano

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta Jihar Kano, ta bankaɗo wasu miyagun ƙwayoyi da suka kai kimanin kilo 12,233.946 (kimanin tan 12.2), na haramtattun ƙwayoyi da abubuwan da aka kama ta hanyar gudanar da ayyukan sirri a faɗin Jihar Kano da kuma filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Atisayen, wanda kwamandan rundunar ta Kano, CN Dahiru Yahaya Lawal ya jagoranta, wani ɓangare ne na yaƙin wanda hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (WADA) ke yi da nufin daƙilewa da gurfanar da su da kuma kawar da miyagun ƙwayoyi na din-din-din.

Baje kolin lalatawar ya haɗa da kilo 11,890.427 da rundunar ta kama da kuma 343.519 da aka kama a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

ADVERTISEMENT

Magungunan sun haɗa da ‘cannabis satiɓa, tramadol, codeine, heroin, hodar iblis, methamphetamine, pregabalin, diazepam, pentazocine da sauran makamantansu.

A cewar hukumar ta NDLEA, an kama waɗanda aka kaman ne daga wani samame da jami’an leƙen asiri suka jagoranta da hare-hare na musamman da suka haɗa da ‘Operation Sharar Mafaka da Operation Ramadan Mubarak’.

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

Binciken ya kuma gano wasu kayayakin maɓoyar muggan ƙwayoyi da suka haɗa da ramuka da kogo a yankin Rimin Kebe, wanda ya nuna hanyoyin da masu fataucin ke bi wajen gujewa jami’an tsaro.

Kwamanda Lawal ya bayyana cewa, tun daga watan Janairun 2026, rundunar ta kama mutane 904 da ake zargi, maza 869 da mata kuma 35, sannan sun kama fiye da tan 2.5 na haramtattun abubuwa tare da samun sama da hukunce-hukunce 54.

Wasu da aka samu da laifin, ya ce; an yanke musu hukuncin ɗaurin shekara 15 a gidan yari.

Ya jaddada cewa, duk da cewa; aiwatar da doka na da matuƙar muhimmanci, yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na buƙatar ɗaukar matakin haɗin gwiwa da ya haɗa da hukumomin tsaro, shugabannin gargajiya da na addini, cibiyoyin ilimi, masu ɗaukar ma’aikata, iyaye da kuma al’umma.

Lawal ya yaba wa Shugaba kuma Babban Jami’in Hukumar NDLEA, Brig.-Gen. Mohamed Buba Marwa (Rtd), CON, OFR, bisa jagorancinsa, ya kuma yaba wa gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa ci gaba da bayar da goyon baya, musamman a aikin yaƙi da zaizayar ƙasa a Rimin Kebe, wanda ya kawar da maɓoyar masu laifi.

Ya kuma yaba wa alƙalan babbar kotun tarayya, bisa hukuncin da suka yanke a kan lokaci tare da jinjina wa daraktan ayyuka da bincike na ƙasa, DCGN Ahmad Sulaiman Ningi, bisa sadaukarwar da ya yi.

Kano
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa
Labarai

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Next Post
Kano

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.