ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Huldar Dake Tsakanin Sin Da Afirka Na Kara Yaukaka

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
Sin

Daga ranar Laraba da ta gabata zuwa jiya Litinin, Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai ziyara hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da kasashen Habasha, da Tanzania, da Lesotho, daya bayan daya. Ziyararsa ta sake tabbatar da al’adar kasar Sin a fannin diplomasiyya, wato ministan wajen kasar ya kan kai ziyara nahiyar Afirka a farkon duk shekara. Hakika kasar Sin ta riga ta kiyaye wannan al’ada har tsawon shekaru 36.

Minista Wang Yi ya yi tsokaci kan dalilin kasar Sin na kiyaye wannan al’ada, inda ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka suna da abokantaka mai zurfi da dogon tarihi, don haka, a ganin kasar Sin, ya kamata ta karfafa wannan hulda da kasashen Afirka a farkon duk shekara, kamar dai yadda wani mutum ke mika gaisuwa da fatan alheri ga ’yan uwansa, gami da ziyartar gidajensu a bikin sabuwar shekara. A zahiri, wannan ziyara da mista Wang Yi ya yi, ta nuna dorewar manufar kasar Sin ta fuskar hulda da kasashen Afirka, da hadin kan kasashe masu tasowa a duniya, gami da aza harsashi ga karin hadin gwiwar bangarorin Sin da Afirka a shekarar da muke ciki.

A yayin ziyararsa a nahiyar Afirka, ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya jagoranci taron tattaunawar bangarorin Sin da Afirka kan manyan tsare-tsare, a hadin gwiwarsa da Mahmoud Youssouf, shugaban kwamitin kungiyar AU, inda dukkan bangarorin 2 suka jaddada bukatar karfafa karfi a kokarin kare hakkin Sin da Afirka, da tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya. Ban da haka, jami’an 2 sun gane ma idanunsu yadda aka kaddamar da Shekarar Cudanyar Al’ummun Sin Da Afirka, inda a karkashin wannan take, za a gudanar da shirye-shirye kusan 600 da suka shafi harkokin matasa, da ta al’adu, da hadin gwiwar kafofin watsa labaru, da dai sauransu, tsakanin bangarorin Sin da Afirka, a shekarar 2026.

ADVERTISEMENT

Watakila za ka so sanin dalilin da ya sa ake da irin wannan hulda mai kyau tsakanin Sin da Afirka. To, dalili shi ne kasar Sin tana hadin gwiwa da kasashen Afirka bisa wani ra’ayi na tushe, wato akidar gaskiya, da daukar hakikanan matakai, da kauna, da sahihanci, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar. Ban da haka, manufofin kasar Sin da na kasashen Afirka sun nuna cewa, bangarorin 2 suna da ra’ayi iri daya, wato neman ci gaba, da haifar da alfanu ga juna, da kokarin kare adalci a duniya. To, wadannan ra’ayoyi sun sa kasar Sin ke rungumar kasashen Afirka, ko da yake wasu kasashe su kan nuna musu kyama. Ban da haka, a lokacin da kasashen Afirka ke fuskantar takunkumi na harajin kwastam da aka kakaba musu, kasar Sin a nata bangare ta dauki niyyar yafe musu haraji. Kana sabanin yadda wasu kasashe ke tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen Afirka, kasar Sin har kullum tana goyon bayan kasashen Afirka a kokarinsu na tabbatar da ikon mulkin kai, gami da kare mutuncinsu.

Jaridar the Vanguard ta kasar Najeriya, ta wallafa wani bayani a kwanan baya, wanda ya ce, al’adar kasar Sin ta tura ministan harkokin wajenta ziyara a kasashen Afirka a farkon duk shekara, ta shaida kauna da girmamawa da kasar take nuna wa bangaren Afirka, wadda ta haifar da hakikanin matakin da ya kusanta kasar Sin da zukatan jama’ar kasashen Afirka. To, muna jiran ganin karin irin wannan mataki da za a dauka a hadin gwiwar Sin da Afirka a shekarar da muke ciki, ta yadda za a rika yaukaka huldar dake tsakaninsu, da tabbatar musu da makoma mai haske, da ta daukacin kasashe masu tasowa. (Bello Wang)

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Amurka Ta Miƙa Wa Nijeriya Kayayyakin Soji Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Miƙa Wa Nijeriya Kayayyakin Soji Domin Yaƙi Da Ta'addanci

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.