ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Na Fuskantar Shari’a Kan Ɓacewar Naira Biliyan 55.9 Kuɗaɗen Zaɓen 2019

by Leadership Hausa
8 months ago
Inec

Ƙungiyar kare haƙƙin tattalin arziki da bin diddigin ayyuka (SERAP) ta maka hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a gaban kotu kan zargin ɓacewar naira biliyan 55.9 da aka ware domin sayen na’urar tantance karanta kati da takardun zaɓe da takardun sakamakon zaɓe da sauran kayan zaɓen 2019.
Zargin, wanda aka jaddada a sabon rahoton shekara-shekara na babban mai binciken kuɗi na gwamnatin tarayya da aka fitar tun a ranar 9 ga Satumbar 2025, na cewa INEC ta kasa bayar da cikakken bayani kan kuɗaɗen da aka raba wa masu aikin kwangila, tare da cewa wasu biyan kuɗin an yi su ba tare da bin ƙa’ida ba.

  • PDP Ta Maka INEC A Kotu Kan Ƙin Amincewa Da Shugabancin Turaki 
  • INEC Ta Fara Kashi Na Biyu Na Rajistar Masu Zabe

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/38/2026, wadda aka shigar a ranar Juma’a da ta gabata a babban kotun tarayya a Abuja, SERAP tana neman umarnin kotu don tilasta wa INEC bayyana cikakkun bayanai game da kuɗaɗen da suka ɓace, ciki har da sunayen duk masu kwangilar da daraktocinsu da masu hannun jari da kuma dawo da kuɗin.

A cewar SERAP, gazawar hukumar wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana yana tauye haƙƙin ƴan Nijeriya na samun sahihin zaɓe mai cike da ƴanci da adalci.

ADVERTISEMENT

“INEC ba za ta iya tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe cikin gaskiya ba idan ba ta magance waɗannan zargin yadda ya kamata ba, an gurfanar da masu laifi, kuma an dawo da kuɗaɗen da ake zargin cin hanci da rashawa,” in ji ƙungiyar.

Rahoton babban mai binciken kuɗi na gwamnatin tarayya ya tayar da ƙura game da rashin daidaito da dama.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

An bayar da rahoton cewa an biya ɗaruruwan naira biliyan 5.3 ga sayan na’urar tantance ba
tare da amincewar hukumar kula da sayen kayayyaki gwamnati ko majalisar zartarwa ta
gwamnatin tarayya, sannnan kuma ba tare da hujjar cewa an kawo kayan ba.

INEC ta yi iƙirarin cewa ta sayen kayan ya shiga cikin tsaron ƙasa, dalilin da babban mai binciken kuɗi na gwamnatin tarayya ya ƙi yarda da shi. Biyan fiye da naira biliyan 4.5 ga ɗimbin kwangiloli guda shida kan takardun jefa ƙuri’a da takardun sakamakon zaɓe ba su da takardu na tabbatarwa, ciki har da hujjojin hanyoyin yin tayin da cancantar kwangiloli.

Ƙarin biyan kuɗaɗen da ake zargin sun haɗa da naira miliyan 331 don kwangiloli daban-daban da naira biliyan 41 don bugu kayan zaɓe ba tare da bin ƙa’ida ba, da naira miliyan 297 don sayan motocin Toyota Land Cruiser guda huɗu, wanda kuɗaɗen ya wuce farashinsu a kasuwa.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar ba ta mayar da naira miliyan 630 a matsayin rance na kuɗi ga jami’ai ba kuma ta yi watsi da cire fiye da naira biliyan 2.1 a matsayin harajin takarda daga kwangiloli.

Ƙungiyar SERAP, ƙarƙashin jagorancin Kolawole Oluwadare, Kehinde Oyewumi, da Andrew Nwankwo, ta yi iƙirarin cewa tuhumar da ake yi tana wakiltar mummunar keta amincewar jama’a da kundin tsarin mulkin Nijeriya da ƙa’idodin yaƙi da cin hanci na duniya.” Ba a sanya ranar sauraron shari’ar ba tukuna.

Inec
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Komawa Makarantu: Iyaye Sun Shawarci Gwamnati Kan Tsaron Ɗalibai Da Malamai

Komawa Makarantu: Iyaye Sun Shawarci Gwamnati Kan Tsaron Ɗalibai Da Malamai

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.