ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Ta Kammala Shirye-shiryen Zaɓen Gwamnan Ekiti Da Zaɓukan Cike Gurbi A Jihohi 6

by Abubakar Sulaiman
3 weeks ago

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da zaɓukan cike gurbi da za a gudanar a ranar Asabar a wasu jihohin ƙasar nan.

Zaɓukan sun haɗa da na gwamnan Jihar Ekiti da kuma na cike gurbi a mazaɓar tarayya ta Dawaki Kudu/Warawa a Jihar Kano, da mazaɓar Zuru a Jihar Kebbi, tare da wasu mazaɓun Sanata a jihohin Ondo, Rivers, Nasarawa da Enugu.

Mataimakin Daraktan Wayar da Kai da Ilimantar da Masu Zaɓe na INEC, Wilfred Ifogah, ya ce hukumar ta horas da ma’aikatanta da jami’an wucin gadi tare da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana. Ya ce jami’an tsaro za su kasance a cibiyoyin kaɗa ƙuri’a da wuraren ajiyar kayan zaɓe, yayin da aka umurci jami’an zaɓe su isa wuraren aikinsu da ƙarfe 7:30 na safe kafin fara kaɗa ƙuri’a da ƙarfe 8:30.

ADVERTISEMENT

A wani ɓangare kuma, INEC ta bayyana cewa an ƙarbi katunan zaɓe na dindindin (PVC) guda 1,028,929 a faɗin Jihar Ekiti, adadin da ya kai kashi 97.1 cikin 100 na masu rajistar zaɓe. Hukumar ta ce wannan ya fi adadin da aka samu a zaɓen shekarar 2023, inda aka karɓi katuna 958,052.

Hukumar ta kuma ce yawan masu rajistar zaɓe a Ekiti ya ƙaru daga 987,647 a shekarar 2023 zuwa 1,059,360 a shekarar 2026 bayan kammala aikin sabunta rajistar masu zaɓe. INEC ta buƙaci jam’iyyun siyasa da magoya bayansu su guji duk wani abu da ka iya tayar da rikici, tare da kira ga masu zaɓe da suka karɓi katunansu da su fito cikin lumana su kaɗa ƙuri’unsu.

LABARAI MASU NASABA

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnati Ta Shirya Gina Gidaje 20,000 Duk Shekara Haɗin Gwuiwar Jamus
  • Abubakar Sulaiman
    Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta
  • Abubakar Sulaiman
    Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga A Wani Ƙauyen Katsina

MASU ALAKA

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta
Manyan Labarai

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Manyan Labarai

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

July 11, 2026
2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa
Da ɗumi-ɗuminsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
Next Post
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Majalisar Wakilai Ta Fara Yunƙurin Gyaran Dokokin Soja

LABARAI MASU NASABA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

July 11, 2026
Gwamna Dauda Ya Raba Buhunan Taki 72,000 Da Kayan Noma Kyauta Ga Manoman Zamfara

Gwamna Dauda Ya Raba Buhunan Taki 72,000 Da Kayan Noma Kyauta Ga Manoman Zamfara

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello

July 11, 2026
Gwamnati Ta Shirya Gina Gidaje 20,000 Duk Shekara Haɗin Gwuiwar  Jamus

Gwamnati Ta Shirya Gina Gidaje 20,000 Duk Shekara Haɗin Gwuiwar Jamus

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ra’ayin Al’umma Game Da Shirin Gwamnati Na Sake Fasalin Hukumar NYSC

July 11, 2026
Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

July 11, 2026

Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

July 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.