Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta yi watsi da sabbin takunkuman Amurka kan alƙaliyar kotun Tomoko Akane ƴar Japan da kuma babban lauyan ofishin mai shigar da ƙara na kotun Mr Abdoulaye Seye, takunkuman da Amurkan ta sanar a jiya duk dai dangane da tuhumar da kotun ke yiwa Isra’ila da aikata laifukan yaƙi a Gaza.
Sanarwar watsi da wannan takunkumai na Amurka da ICC ta fitar a yau Laraba, ta ce takunkumai sun shirin ƙalubalantar cikakken ƴancin da kotun ke da shi, haka zalika karan tsaye ne a ƙoƙarin Amurkan na kassara ayyukan shari’a.
Zuwa yanzu dai 9 cikin alƙalan kotun ta ICC 18 na ƙarƙashin makamantan takunkuman na Amurka har kuwa da mataimakan babban mai shigar da ƙara na kotun 2 da kuma tsohon babban mai shigar da ƙara baya ga wani ma’aikacin kotun na daban.
ICC ta ce takunkuman na Amurka ba abun lamunta ba ne, kuma wani yunƙuri ne da kai tsaye ke ƙalubalantar ayyukan kotun don mayar da ita mai kawar da kai game da taɓargazar da ake aikatawa.
Sanarwar ta ICC ta ce takunkumai kan alƙalai a kowanne matakai wani yunƙuri ne na yaƙi da tabbatuwar adalaci ko kuma hukunta masu laifi.
Kotun ta ce ayyukanta zasu ci gaba ba tare da nuna wariya ko tsallake wasu wajen gudanar da bincike ko kuma tabbatar da adalci kan waɗanda aka zalunta dama hukunta wanda aka samu da laifi ba.
Yayinda a gefe guda sanarwar ke sake jaddada goyon bayan ICC ga dukkanin jami’anta a kowanne mataki tare da ƙarfafa musu gwiwar ganin sun ci gaba da ayyukansu a doron gaskiya.
Tuni Jamus ta fitar da sanarwar cikakken goyon baya ga jami’an kotun ta ICC dama kotun baƙi ɗaya game da sabbin takunkuman na Amurka, tana mai kira da a haɗa ƙarfi don bayar da kariya ga kotun.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Jamus ta fitar ta bayyana cikakken goyon bayan ƙasar ta Turai ga ICC tana mai bayyana muhimmancin kotun.














