ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 27, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’ar JOS Ta Zama Zakara Wajen Bin Ƙa’idojin Ba Da Guraben Karatu

by Idris Aliyu Daudawa
2 months ago

Jami’ar Jos (UniJos) ta kasance zakara a lokacin da aka taro na 6 na yadda manyan makarantu suke bada guraben karatu wanda daga ƙarshe nambar girma ce ake badawa, Hukumar shirya jarrabawar manyan makarantu wato JAMB ita ce ta shirya taron.

Jaridar LEADERSHIP ta bayyana cewa taron na 6 an yi shi ne tare da tsarin yadda Hukumar ta ke bada guraben karatu na  shekarar 2026 na manyan makarantu wanda aka yi a Abuja.

Jami’ar Jos da aka fi sani da UNIJOS ita ce ta kasance Zakara wajen lashe babbar kyauta ta Naira miliyan ɗari biyar Naira (N500,000,000.00) tare da wasu waɗanda suka yi nasara su takwas da su ma suka raba Naira miliyan ɗari bakwai da hamsin (N750,000,000.00).

ADVERTISEMENT

Kamar yadda bayanin da ya fito daga mataimakin Rajistara,harkar labarai, wallafawa, tsara yadda abubuwa suka dace su kasance, hulɗa da jama’a, Emmanuel Madugu ya ce a Jos, kasancewar Jami’ar Jos wadda ta  samu babbar kyauta, hakan ya kasance ne saboda yadda take bin ƙa’idojin bada guraben karatu bil haƙƙi da gaskiya, kamar dai yadda lamarin ya ke na tsarin bada guraben na karatu, ita ce kan gaba wajen ba ɗalibaiƴan ƙasashen wajen guraben karatu.

Ya ce JAMB ta ɓullo da karramawar ce ta NATAP-M domin ta ƙara bunƙasa aikata lamurra da gaskiya, yin abubuwa domin cancanta, yin abubuwa kamar yadda ya dace ayi su; da kuma uwa uba yin abinda ya fi kome kyau kan yadda ake bada guraben karatu a Nijeriya da kuma hanyar da ake bi.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Zai Ƙara Wa Sojoji Albashi Nan Ba Da Jimawa Ba – Ministan Tsaro

Taimakon Ƴan Bindiga: Kotu Ta Yanke Wa Mata 3 Hukuncin Shekaru 14 A Magarƙama

“Irin wannan abu mafi kyau da muhimmanci yana zuwa ne kamar wata kyauta ce ta ranar haihuwar Farfesa Tanko Ishaya, wanda ranar haihuwar shi ta kasance 11 ga Mayu.

Sai dai kuma,lokacin da yake nuna jin daɗin shi mataimakin Shugaban jami’ar Farfesa Ishaya Tanko,ta samar da lamarin na karramawar.

Ya ce karramawar ta nuna yadda tsarin Jami’oin Nijeriya ya ken a yadda ake tafiyar da harkokin bada guraben karatu, hakane kuma yasa ta bi tsare- tsaren kamar yadda suke na yadda Hukumar shirya jarrabawar  manyan makarantu suke, musamman ma dangane da guraben karatu na shekarar karatu ta 2025/2026.

Tanko ya ba Ministan ilimi tabbacin cewa  Jami’oin Nijeriya za su ci gaba da taimakawa gwamnati ta ɓangaren sake fasalin ilimin Jami’oi yadda zai samu ci gaba da bunƙasa a Nijeriya.Bugu da ƙari ya bada tabbacin cewa duk masu ruwa da tsaki cewa,za ayi namfani da kuɗaɗen da aka samu ta hanyar da ta dace, saboda a samu fdamar bunƙasa abubuwan  more rayuwa da suke taimakawa ɓangaren ilimi, kayan aiki da kuma ayyukan.

Da yake jawabi lokacin bada karramawar ga Shugabannin jami’ar da ɗaliban jami’ar, Farfesa Tanko  ya bayyana cewa karramawar na daga cikin sakamakon mizanin da JAMB  ta yi amfani da shi na duk jami’oin waɗanda suke daga cikin  waɗansu abubuwan da aka yi amfani da su wajen tsare- tsare biyar, inda Jami’ar Jos ta kasance ta ɗaya(1) wadda take ɗalibai ƴan ƙasashen waje guraben karatu;ta kuma kasance ta biyu (2) da take bin ƙa’idoji na amfani da tsarin da za ayi amfani da shi na shekarar 2025, ta shida( 6) da tafi bada damar guraben karatu a Nijeriya.

Waɗannan bada kambun bunƙasar ya sa Jami’ar ta zama Zakara a taron karo na 6 na lamarin da ya shafi bada guraben karatu na daga cikin manyan makarantu, na daga cikin dalilan da suka aka karrama Jami’ar Jos.

Farfesa Tanko ya ce irin ɗaukakar da Jami’ar ta samu ko shakka babu hakan ya nuna ba ayi ma lamarin mulki na Jami’ar riƙon sakainar kashi ba,na ɗora ita jami’ar a cikin wani lamarin da yasa kowane lokaci a kullun  ɗaukaka ta ke ƙara samu.

Ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da mulkinsa ko jagorancin shi ya sag aba da kuma maida hankali shi ne,na tabbatar da  Jami’ar Jos ta ci gaba da kare kambun ta na wadda ta shiga yin kafaɗa- kafaɗa da jami’oin ƙasashen waje.

Farfesa Tanko ya ce irin karramawar da aka yi ma jami’ar ta yi dai dai da wadda aka karrama shi da nambar girmamawa da ta ce shi ne mutumin Jihar Filato na shekarar 2026 saboda yadda jagorancin shi ke taimakawa wajen ci gaban ɓangaren ilimi.

Tun farkon wannan shekarar ne, Jami’ar Jos ta kasance ta 10 a Jami’oin Nijeriya, wanda wata kafa ta ilimi mai zurfi da ta kasance sananna wato Times Higher Education ta kasance ita ce mai bada matsayin kowace Jami’oi  a duniya a shekarar 2026.

Irin wannan babban ci gaban shi yasa jami’ar Jos da sauran wasu Jami’oi huɗu mashahurai, kamar su Jami’ar Ahmadu Bello Zariya Ahmadu,Jami’ar Nijeriya ta, Nsukka, Jami’ar Ilorin, da kuma Jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya, Minna, suna daga cikin mizanin Jami’oin duniya daga cikin 1201 zuwa1500.

Mataimakin Shugaban jami’ar bugu da ƙari ya yi bayani kan dalilan da suka sa Jami’ar take ƙara bunƙasa saboda yadda ake yi mata kallon, tabbacin gaskiya,da kuma yadda ɗalibanta suke daga cikin ɗaliban wasu Jami’oi a Nijeriya.

Ya ƙara uin bayani da ke nuna nasarar da Jami’ar ta sa, saboda irin maida hankali da sadaukar da kan da Malaman Jami’ar suka yi, don haka ya yi kiran ya dace karramawat ta kasance wani mizani ne yadda za a sa ran samun irin hakan nan gaba.

Tanko  ya yi bayanin da ke nuna kuɗaɗen za ayi amfani da su ne domin a ƙara bunƙasa tasirin jami’ar na yadda ta ke da dama ta ba ɗaliban ƙasa da ƙasa guraben karatu,da karatu wanda yake ɗauke da ƙwarewa ta bunƙasar ilimin da ake koya ma su ɗaliban.

Shugaban sashen hulɗa da ɗalibai, Farfesa Christopher Piwuna, a na shi jawabi ya jinjinawa mataimakin Shugaban jami’arin saboda irin jajircewar da ya nuna ta ɓangaren Shugabanci, musamman ma ta ɓangaren bada guraben karatu.

Ya tuna da cewa ƴan shekarun da suka gabata, mataimakin Shugaban jami’ar ya kasance shi ne wanda aka sa gaba kan lamarin da ya shafi bada guraben karatu inda aka samu wasu matsaloli, ya kuma ɗauki dogon lokacin kafin ya gano bakin zaren.

Don haka ne ma Piwuna ya bayyana cewar karramawar tana nuna yadda shi mataimakin Shugaban jam’iar ya ke son a riƙa aikata lamurran gaskiya.

Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Sarakunan Da Suka Yi Wa Turawan Mulkin Mallaka Turjiya A Nijeriya
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Yajin Aiki: Ƙungiyar Likitocin Nijeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adin Mako Huɗu

MASU ALAKA

Labarai

Tinubu Zai Ƙara Wa Sojoji Albashi Nan Ba Da Jimawa Ba – Ministan Tsaro

July 27, 2026
Labarai

Taimakon Ƴan Bindiga: Kotu Ta Yanke Wa Mata 3 Hukuncin Shekaru 14 A Magarƙama

July 27, 2026
Sakamakon Dangantakar Sin Da Afrika Na Taba Mutane Masu Rauni Da Karamin Karfi
Ra'ayi Riga

Sakamakon Dangantakar Sin Da Afrika Na Taba Mutane Masu Rauni Da Karamin Karfi

July 27, 2026
Next Post
Kashi 30 Kacal Ne Ke Yin Noma Da Kayan Noma Na Zamani A Nijeriya —AFAN

Kashi 30 Kacal Ne Ke Yin Noma Da Kayan Noma Na Zamani A Nijeriya —AFAN

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Zai Ƙara Wa Sojoji Albashi Nan Ba Da Jimawa Ba – Ministan Tsaro

July 27, 2026
Har Kullum Sin Na Adawa Da Yadda Amurka Ke Siyasantar Da Batutuwan Fasaha Da Na Tattalin Arziki

Har Kullum Sin Na Adawa Da Yadda Amurka Ke Siyasantar Da Batutuwan Fasaha Da Na Tattalin Arziki

July 27, 2026
Kasar Sin Ta Gabatar Da Matsaya Game Da Matakan Karshe Na Bincike Mai Lamba 301 Kan Tilasta Yin Kwadago Da Amurka Ta Fitar

Kasar Sin Ta Gabatar Da Matsaya Game Da Matakan Karshe Na Bincike Mai Lamba 301 Kan Tilasta Yin Kwadago Da Amurka Ta Fitar

July 27, 2026

Taimakon Ƴan Bindiga: Kotu Ta Yanke Wa Mata 3 Hukuncin Shekaru 14 A Magarƙama

July 27, 2026
Sin Za Ta Ci Gaba Da Ingiza Kyakkyawan Yanayin Cinikayya Tsakaninta Da Nahiyar Afirka

Sin Za Ta Ci Gaba Da Ingiza Kyakkyawan Yanayin Cinikayya Tsakaninta Da Nahiyar Afirka

July 27, 2026
Sakamakon Dangantakar Sin Da Afrika Na Taba Mutane Masu Rauni Da Karamin Karfi

Sakamakon Dangantakar Sin Da Afrika Na Taba Mutane Masu Rauni Da Karamin Karfi

July 27, 2026

WAFU B 2026: Nijeriya Ta Doke Ghana Da Ci 4-2 A Wasan Farko

July 27, 2026
An Samu Karin Sabbin Abubuwa Da Sin Ke Fitar Wa Waje Da Ake Wa Lakabi Da “New New Three”

An Samu Karin Sabbin Abubuwa Da Sin Ke Fitar Wa Waje Da Ake Wa Lakabi Da “New New Three”

July 27, 2026

NSCDC Ta Cafke Mutane 2 Da Ake Zargi Da Sace Kayan Titin Jirgin Kasa A Kano

July 27, 2026
Saura Kwanaki 100 A Bude CIIE Karo Na 9

Saura Kwanaki 100 A Bude CIIE Karo Na 9

July 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.