ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kashi 30 Kacal Ne Ke Yin Noma Da Kayan Noma Na Zamani A Nijeriya —AFAN

by Abubakar Abba
4 months ago

Ƙungiyar manoma ta ƙasa, reshen Jihar Legas (AFAN), ta yi iƙirarin cewa; kashi talatin cikin ɗari ne kacal na manoman ƙasar ke amfani da kayan aikin noma na zamani.

Ta danganta hakan ne, kan rashin ci gaba da noma amfani gona masu yawa a ɗaukacin faɗin ƙasar.

A cewar ƙungiyar, kimanin kashi 70 na manoman ƙasar, har yanzu suna yin noma ne da kayan gargajiya, wanda a yanzu, kashi 30 kacal ne ke yin amfani da kayan aikin noma na zamani.

ADVERTISEMENT

Mataimakin shugaban ƙungiyar, Mista Shakin Agbayewa, ya sanar da haka ne a Legas, wanda kuma ya danganta matsalar, kan rashin samun ingattacciyar ƙasar nomar da kuɗaɗe da sauran kayan aikin noma na zamani.

Agbayewa ya koka, kan yadda manoman ƙasar, ba a samar musu da kayan aiki na zamani, kamar taraktocin noma da sauran kayan aikin, na zamani.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

A cewarsa, tsadar kuɗin ɗaukar hayar taraktocin noma, wanda hakan ke ci gaba da haifar wa manoman ƙasar, musamman ƙanana da ke karkara, wani ƙarin ƙalubalen ne.

Ya yi nuni da cewa, duk da ƙalubalen da ake ci gaba da fuskanta a fanin, ya jaddada cewa; yin amfani da kayan aikin noma na zamani, na ƙara bunƙasa fannin a ƙasar, wanda kuma zai sanya a samu zuba jari na tsawon lokaci.

“Mai yiwuwa, yin amfani da kayan aikin noman na zamani, musamman na gajeren zango, ya kasance mai tsada, amma a dogon zango za a iya samun riba mai ɗimbin yawa,” a cewar shugaban.

Agbayewa ya ƙara da cewa, manoman da suka rungumi yin noma da kayan aikin na zamani, za su iya yin noma mai ɗimbin yawa tare da rage ɓata lokaci da kuma rage yin asara.

Ya ƙara da cewa, idan aka rungumi yin noma da kayan aikin na zmani, hakan zai ƙara taimakawa, wajen bunƙasa noma da rage ɗaukar hayar Leburori tare da kuma jawo ra’ayin matasan ƙasar, su rungumi fannin na aikin noma.

Agbayewa ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi, da su samar da cibiyoyin bayar da hayar taraktocin noma, sannan kuma a kan farashi mai rahusa, musaman domin manoman ƙasar su riƙa yin haya, idan sun tashi yin noma.

Ya kuma yi kira da a ƙara samar da masana’antu, ƙera kayan aikin noma na zamani a ƙasar, musamman domin samar da kayan gyaransu, wanda hakan zai sanya a rage shigo da kayan zuwa cikin ƙasar, daga ƙetare.

A cewarsa, ƙara faɗaɗa samar da kayan aikin noma na zamani, zai ƙara taimakawa, wajen samar da wadataccen abinci a ƙaar tare da rage shigo da abinci daga ƙetare.

Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya

Cibiyar IAR Ta Gudanar Da Ayyukan Bincike 140 Kan Sabbin Amfanin Gona 

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.