ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabon Tsarin Tattaunawa Don Kawo Karshen Rikicin Fulani Makiyaya Da Manoma

by Abubakar Abba
4 months ago
Manoma

Batun magance yawan samun rikici a tsakanin Fulani makiyaya a kasar nan, shi ne ya kasance kan gaba a taron masu ruwa da tsaki da masu yin dokoki da kuma masu zuba jari a kasar suka gudanar a babban birnin tarayyar Abuja.

Taron ya kunshi batun noman zamani da fitar da amfanin gona zuwa ketare na Afrika na shekarar 2026 (AGROMEKA EDPO 2026).

Taron wanda ya kasance na kwana biyu, cibiyar baje kolin kasuwanci da  masana’antu, reshen Abuja ce ta shirya shi, tare da hadaka da gonar JMT Plus.

ADVERTISEMENT

Manufar taron shi ne, domin samar da dauki wajen yin amfani da kayan zamani a fannin aikin noman kasar, tare kuma da fitar da amfanin da aka noma zuwa kasashen ketare.

Kazalika, taron ya wuce batu kan mayar da hankali a kan hada-hadar kasuwanci, amma ya bayar da damar tattaunawa a kan yadda za a kawo karshen rikice-rikicen da ke yawan afkuwa a tsakanin monoma da Fulani makiyaya

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

An dai shafe shekaru da dama a kasar nan, ana samun yawan afkuwar wannan matsala, wacce kuma har yanzu ta ke ci gaba afkuwa, wanda lamarin ke haddasa rasa rayukan dukkanin bangarorin biyu da haifar da dakatar da yin kiwon dabbobi da da yin noma, tare da kuma zama babbar barazana ga tsaron kasar.

Hakazalika, rikice-rikicen a tsakanin bangarorin biyu, ya fi yin kamari a yankin Nijeriya ta tsakiya, wato Middle Belt, ya kuma samo asali ne a kan batun mallakar kasar noma da albarkatun ruwa da afkuwar sauyin yanayi da yawan karuwar al’umma, tare da kuma rashin samar da kyakyawan tsari ga fannin aikin noma na kasar nan.

Cif Emeka Obegolu, shugaban cibiyar da yake bayani a kan shirin ya bayyana cewa;  shirin ya kuma hada da manyan masu ruwa da tsaki da za su tattauna a kan yadda za a lalubo da mafita a rikice-rikicen da ke afkuwa a tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma, musamman domin ci gaba da bunkasa fannin aikin na noma a fadin kasar nan.

Ya ci gaba da cewa, manoma da Fulani makiyaya da jagororin al’umma da ‘yan kasuwa da ke hada-hadar kasuwancin amfanin gona da kuma jami’in gwamnati, za su halarci taron na tattaunawar, domin kawo karshen kalubalen da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin bangarorin biyu

Obegolu ya danganta baje kolin, a matsayin batun baje haja, inda ya ce; taron ya kai matakin yadda kasar za ta fara yin aikin noma da kaya na zamani.

Taken taron shi ne, yin amfani da fasahar zamani, domin zuba jari a fannin fitar da kayan amfanin gona zuwa kasashen ketare tare kara habaka fannin akin noma da kuma rage asarar da ake yi, sakamakon rikice-rikicen Fulani makiyaya da kuma manoman kasar nan.

Ya ci gaba da cewa, rungumar yin noma da kayan na zamani, ciki har da yin noman rani, zai rage yawan lalacewar kasar noma a kasar nan tare da kuma magance yawan samun rikice-rikice a tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoman kasar.

Manoma
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Katsina Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Mahaddata Alƙur’ani – Gwamna Radda

Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Sayar Wa Da Manoma Takin Zamani Kan Farashi Mai Rahusa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.