ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jiga-jigan ‘Yan Siyasa A Kano Na Ci Gaba Da Fafatawa Don Dorewar Siyasarsu

by Yusuf Shuaibu
5 months ago

Yanayin siyasa a Jihar Kano ya shiga wani hali da ya fi tashin hankali da rashin tabbas a tarihin siyasar jihar, yayin da jiga-jigan ‘yan siyasa ke ci gaba da fafatawa don dorewar siyasarsu, wanda suke sauya sheka daga wannan jam’iyya zuwa wancan, a matsayin wata dabara na samu damar dorewar siyasa a 2027.

Abin da ya fara a matsayin kunkuri na jiga-jigan ‘yan siyasan Kano, wanda ya zama sake tsara kawance tsakanin manyan ‘yan siyasan don samun tasiri a Kano da ma kasa baki daya.

A tsakiyar wannan hadin gwiwar siyasar da ke bayyana Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf da tsohon gwamnan Rabiu Kwankwaso, da tsohon mataimakin gwamna Nasiru Gawuna, mutanen nan guda uku suna da tasiri, wadanda suka sauya ra’ayinsu da ke ci gaba da sake fasalin siyasa a jihar.

ADVERTISEMENT

A cikin sauyin tsarin siyasa da ke faruwa, abin da ya fito fili shi ne, sauyin da ya jawo cece-kuce shi ne na Gwamna Yusuf, wanda ya taso a karkashin kungiyar siyasa ta Kwankwasiyya da Kwankwaso ke jagoranta, ya sake daidaita matsayinsa ta hanyar hadawa da tsarin siyasa na tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, ta dawowarsa cikin jam’iyyar APC.

An fassara wannan mataki a matsayin yunkurin dabarun hada mulki da karfafa samun goyon bayan tarayya.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

A bangaren daya kuma, Gawuna, wanda a baya ya kasance mutum mai muhimmanci a cikin APC kuma dan takarar gwamna a 2023, ya sake tsara matsayinsa a cikin hadakar ‘yan adawa a jam’iyyar ADC. Sauyin da ya yi ana ganin shi ne a matsayin daya daga cikin manyan sauye-sauyen siyasa masu muhimmanci a tarihin Kano a baya-bayan nan.

Girgizar siyasa ta karu lokacin da Kwankwaso ya fice hukuma daga jam’iyyar NNPP kuma ya shiga ADC, wannan mataki ya haddasa girgizar siyasa a cikin tsarin jam’iyya da kuma hanyoyin kasa da aka gina a kan dogon tasirinsa.

Yayin da yake magana a lokacin rajistarsa a hukuma a gidansa, Kwankwaso ya bayyana wannan mataki a matsayin mai ciwo amma ya zama wajibi.

“Ina sanar da sauya shekata daga jam’iyyar NNPP nan take,” in ji shi. Yana kara da cewa wannan mataki ta samo asali ne daga bukatar samun hadin kan siyasa mafi fadi a cikin kasa nan.

Taron ya samu halartar shahararrun ‘yan siyasa, ciki har da Dabid Mark da Aminu Tambuwal da Rotimi Amaechi da Peter Obi, wanda ke nuna bayyana sabuwar hadin gwiwar ‘yan adawa mai fadi a cikin jam’iyyar ADC.

A tsakanin wadannan sauye-sauyen, shugaban jam’iyyar ADC na Jihar Kano, Musa Ungogo, ya ce jam’iyyar na amfani da dabaru wajen jawo hankalin sababbin mambobi da kuma kiyaye hadin kai a ciki.

A cewar Ungogo, hankalin ADC bai tsaya kan harkokin siyasa ba, yana karkata kan warware matsalolin al’umma da ci gaban tattalin arziki.

“Ba mun tsaya game da kwace mulki ba ne, har ma da yadda za a ceto mutane daga ‘yan fashi da yunwa da talauci,” in ji shi. Ya kara da cewa shigar Kwankwaso cikin jam’iyyar ta kara karfafa tsarin jam’iyyar kuma ta kara inganta kiraye-kiraye na hadin kai.

Ya bayyana cewa shugabannin jam’iyya sun yarda su yi amfani da yarjejeniya wajen zabar ‘yan takara, inda ya lura cewa irin wannan hanya zai hana rikice-rikice a ciki da kuma tabbatar da adalci kafin shekarar 2027.

Yanayin ya kara sake tsare-tsare a matakin farko. Kungiyar Kwankwasiyya, ta bakin mai magana da yawun kungiyar, Mansur Kurugu, ya tabbatar da cewa sauye shekan sun karfafa jam’iyyar ADC kuma sun kara kwarin gwiwa a tsakanin magoya baya.

Lamarin siyasar Jihar Kano ta kara rikicewa, musamman a cikin APC, biyo bayan yin murabus na mataimakin gwamna, Aminu Gwarzo, wanda ya haifar da tsananin shawarwarin siyasa da sake fitowa da muhawara kan wanda zai maye gurbinsa.

Ajiye aiki, wanda aka sanar a ranar Juma’a, 27 ga Maris, a cikin wata sanarwa biyo bayan ci gaba da shirin korar Gwarzo da majalisar dokokin Jihar Kano ta fara.

Murabus din mataimakin gwamnan ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin jam’iyyun siyasa da bangarorin siyasa kan wanda ya kamata ya gaje shi, tare da mabambantan muradu a cikin APC da waje suna neman samun tasiri a cikin lamarin.

Sai dai kuma, an ruwaito cewa Ganduje ya amince da Murtala Garo a matsayin mataimakin gwamna.

Wata sahihiyar majiya wanda ta nemi a sakaye sunanta, ta bayyana cewa Ganduje ya ne hakan yayin wani taro na musamman da Shugaban kasa, Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya yi ganawar sirri da Ganduje da tsohon ministan tsaro, Badaru Abubakar, a taruka daban-daban a fadar shugaban kasa, wanda ake ganin wani bangare ne na ci gaba da shawarwarin siyasa a manyan jihohi kafin zaben 2027.

A cewar majiyar, Ganduje ya gabatar da Garo a matsayin abokin siyasa mai aminci tare da karfi wajen motsa mutane a matakin kasa a duk fadin Jihar Kano. Ya bayyana shi a matsayin mutum mai dogaro a cikin tsarin APC kuma wanda zai iya karfafa nasarorin siyasar jam’iyyar.

Majiyar ta ambaci tsohon gwamna yana bayyana amincewa da Garo na hada tsarin jam’iyya da kuma kirkiro goyon baya a cikin rukunoni masu muhimmanci na zabe, musamman a matakin farko, sakamakon cewa a lokuta da dama yana da tasiri a siyasar Jihar Kano.

Garo, wanda a baya ya yi aiki a matsayin kwamishina kananan hukumomi da masarautu na Jihar                    Kano a karkashin gwamnatin Ganduje, ana ganin shi a matsayin daya daga cikin kusoshi na siyasa mafi kusa ga tsohon gwamnan, tare da tasiri mai yawa a dukkanin kananan hukumomi a jihar.

Haka kuma shi ne mataimakin dan takarar gwamna na APC a zaben 2023, wanda ya yi takara da Gawuna.

Sai dai kuma ko kafin rahoton goyon bayan Ganduje, masu ruwa da tsaki na siyasa a cikin Kano ta Kudu sun fara gudanar da shawarwarin cikin gida, suna bayyana damuwa kan yin watsi da tsarin yankuna, inda suke ganin a yi la’akari da tsarin yankuna wajen zabar sabon mataimakin gwamna.

A cewar majiyar, masu ruwa da tsaki sun yi ikirarin cewa matsayin mataimakin gwamna a tarihi yana canzawa tsakanin Kano ta Arewa da Kano Tsakiya, wanda hakan ya bar Kano Kudu a baya.

Bayan matsayi na jam’iyya, masana harkokin siyasa suna cewa abubuwan da ke faruwa suna nuna sauye-sauye masu zurfi a tsarin siyasar Kano.

Wani masanin siyasa a jami’ar Bayero Kano, Kamilu Fagge, ya bayyana cewa sauye-sauyen suna faruwa ne galibi saboda son kai fiye da ra’ayin siyasa.

“Abin da muka shaida a Kano shi ne, yanayin siyasa mai juyawa inda biyayya ta zama na biyu. Babban abin da ke motsawa shi ne, tsira da burin siyasa na kashin kai,” in ji shi.

Fagge ya yi gargadin game da rikice-rikicen cikin gida a cikin APC, yana nuna cewa rukunonin da ke fafatawa da Ganduje, Barau Jibrin, da sauran sababbin masu zuwa, duk suna kokarin samun tasiri ne kafin zaben 2027.

Yayin da Jihar Kano ke kusantar shekarar 2027, jihar na ci gaba da kasancewa a cikin yanayin siyasa mai canzawa wanda aka bayyana shi da sauyin kawance, sake tsara dabaru, da karuwar gasa.

Duk da APC na nuna kwarin gwiwar samun nasara, kungiyar Kwankwasiyya tana cewa tana da rinjaye a matakin farko, kuma ADC na ci gaba da jan hankalin masu tasiri da ke neman sabbin jam’iyyar siyasa.

Abin da ke bayyana shi ne, an fara fafata siyasar 2027 a kawai a matsayin gasa don samun kuri’u ba, amma a matsayin gwagwarmaya don samun muhimmancin siyasa, tsarin mulki, da dorewar siyasa a daya daga cikin mafi karfi wuraren siyasa a Nijeriya.

Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Kafafen Yada Labarai Na Jamus Da Birtaniya: Kasar Sin Na Da Karfin Jure Mummunan Tasirin Matsalar Makamashi Ta Duniya

Kafafen Yada Labarai Na Jamus Da Birtaniya: Kasar Sin Na Da Karfin Jure Mummunan Tasirin Matsalar Makamashi Ta Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.