ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, October 29, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jigon APC Kuma Tsohon Shugaban NPA, Aminu Dabo, Ya Fice Daga APC A Kano

by Abubakar Sulaiman
2 weeks ago

Jam’iyya mai mulki a matakin tarayya ta sake fuskantar babban koma-baya a Jihar Kano, biyo bayan murabus ɗin babban jigon jam’iyyar kuma tsohon Manajan Daraktan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Ƙasa (NPA), Arch. Aminu Dabo, wanda ya ajiye muƙaminsa na Shugaban Masu Ruwa da Tsaki (Caucus Chairman) na APC a Ƙaramar Hukumar Dambatta tare da ficewa daga jam’iyyar gaba ɗaya.

Sanarwar murabus ɗin ta fito ne ta hanyar wata wasiƙa mai kwanan wata 7 ga watan Oktoba, 2026, wadda Arch. Aminu Dabo ya aike wa shugaban jam’iyyar APC na Mazabar Dambatta ta Gabas, inda ya sanar da janye zama ɗan jam’iyyar mai mulki a hukumance.

Mataimakin Arch. Aminu Dabo a ɓangaren yaɗa labarai, Abdullahi Othman, shi ne ya tabbatar da batun murabus ɗin a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a birnin Kano ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba, 2026.

ADVERTISEMENT

Ya bayyana cewa tsohon shugaban na NPA bai fayyace ainihin dalilansa na yanke wannan hukunci a cikin wasiƙar ba, haka kuma bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai koma ba a halin yanzu.

Ficewar Arch. Aminu Dabo wanda ya taɓa zama Kwamishinan Filaye da Tsare-tsare a Kano, wanda ya kuma nemi takarar gwamnan jihar a baya, kuma shugaba kuma mamallakin kwalejojin kiwon lafiya masu zaman kansu na Aminu Dabo College of Health Sciences and Technology da Aminu Dabo College of Nursing Sciences ta jefa ƴan siyasa a jihar cikin fargaba da hasashen sauyin sheƙa yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a

’Yan Bindiga Sun Sace Mata 29 Da Wani Yaro A Jihar Neja

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata
  • Abubakar Sulaiman
    ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    INEC Na Fuskantar Suka Kan Amfani Da Manhajar AI

MASU ALAKA

Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a
Manyan Labarai

Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a

October 28, 2026
’Yan Bindiga Sun Sace Mata 29 Da Wani Yaro A Jihar Neja
Manyan Labarai

’Yan Bindiga Sun Sace Mata 29 Da Wani Yaro A Jihar Neja

October 28, 2026
TUC Ta Yi Watsi Da Ƙarin Tallafin Sufuri Na ₦70,000, Ta Nemi A Biya Mafi ƙarancin Albashin ₦300,000
Manyan Labarai

TUC Ta Yi Watsi Da Ƙarin Tallafin Sufuri Na ₦70,000, Ta Nemi A Biya Mafi ƙarancin Albashin ₦300,000

October 28, 2026
Next Post
Faɗaɗa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Alamun Fargaba Ne Da Tsoro –Atiku Abubakar

Faɗaɗa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Alamun Fargaba Ne Da Tsoro --Atiku Abubakar

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Damu Matuka Game Da Ci Gaba Da Tashin Hankali A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Damu Matuka Game Da Ci Gaba Da Tashin Hankali A Yankin Gabas Ta Tsakiya

October 28, 2026
Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a

Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a

October 28, 2026
Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Tsaurara Tsaro Bayan Kashe Mutane A Taraba

Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Tsaurara Tsaro Bayan Kashe Mutane A Taraba

October 28, 2026
Tsibirin Lemu: Wuri Mai Ni’ima Da Ke Kunshe Da Tarihin Gwagwarmayar Kafuwar Kasar Sin

Tsibirin Lemu: Wuri Mai Ni’ima Da Ke Kunshe Da Tarihin Gwagwarmayar Kafuwar Kasar Sin

October 28, 2026
Sin Da Gambia Sun Gudanar Da Taron Musayar Kwarewa A Kungiyar Ciniki Ta Duniya

Sin Da Gambia Sun Gudanar Da Taron Musayar Kwarewa A Kungiyar Ciniki Ta Duniya

October 28, 2026
Sin Ta Yi Kira Da a Gaggauta Tsagaita Bude Wuta Tare Da Yin Tattaunawa Cikin Ruwan Sanyi Tsakanin Amurka Da Iran

Sin Ta Yi Kira Da a Gaggauta Tsagaita Bude Wuta Tare Da Yin Tattaunawa Cikin Ruwan Sanyi Tsakanin Amurka Da Iran

October 28, 2026
Gwamnati Da NLC: Abin Da Ma’aikata Ya Kamata Su Sani Kan Tallafin Sufuri Na ₦70,000

Gwamnati Da NLC: Abin Da Ma’aikata Ya Kamata Su Sani Kan Tallafin Sufuri Na ₦70,000

October 28, 2026
’Yan Bindiga Sun Sace Mata 29 Da Wani Yaro A Jihar Neja

’Yan Bindiga Sun Sace Mata 29 Da Wani Yaro A Jihar Neja

October 28, 2026
Sin Da Karin Kasashe 25 Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar MDD Ta Inganta Hada-Hadar Dakon Hajoji

Sin Da Karin Kasashe 25 Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar MDD Ta Inganta Hada-Hadar Dakon Hajoji

October 28, 2026
Abubuwan Da Ke Hana Yaran Arewacin Nijeriya Zuwa Makaranta

Abubuwan Da Ke Hana Yaran Arewacin Nijeriya Zuwa Makaranta

October 28, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.