ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kafin Ki Nemi Saki, Nemi Amsar Waɗannan Tambayoyi Da Kanki

by Bilkisu Tijjani
4 months ago

Sau tari wasu matan suna zaƙewa akan a sake su ba tare da tsayawa sunyi tunani ko nazari mai zurfi da zai hanasu yin kuskuren da za suyi dana sani ba.

Ana samu wasu matan da tabbas ya dace su nemi saki. Wasu kuwa kwata kwata bai dace ba amma kuma sai su nemi yin hakan saboda rashin tsayawa sunyi dogon nazari.

Kamin ki biyewa zuciyarki data raya miki neman saki, to fa ya kamata ki yiwa kanki waɗannan tambayoyin kamar haka:

ADVERTISEMENT

1. Kina son mijin ki? Wannan shi ne abu na farko da ya kamata ki soma neman amsar sa da kanki domin ta hakan ne idan kin saku baza ki yi danasi ba.

2. Wani irin laifi ne? Dole ne ki duba nauyin laifin da kike tuhumar mijinki da shi ya kai ki nemi saki ko dai kawai ranki ne ya ɓaci.

LABARAI MASU NASABA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

Sau dayawa wasu matan suna neman saki ne akan yar ƙaramar matsalar da za a iya haƙuri dashi a zamantakewa na aure.

3. Yaya iyayyenki za su ji? Kamin ki nemi saki ya zama dole ki samu amsar yadda iyayyenki za su ji bayan mutuwar auren naki.

Iyaye ko waliyai suna iya hanaki jin daɗin zaman zawarci muddin basu goyi bayan mutuwar aurenki ba. Don haka ya zame miki wajibi ki soma samun amsar wannan matsalar kamin ki nemi saki.

4. Makomar yaranki? : Idan kuna da haihuwa a tsakaninku da mijin naki, ya zama wajibi ki samu amsar makomar ƴaƴanki da wannan mijin naki kamin ki bukaci ya sake ki.

Akwai mata da yawa da suke neman saki bayan an sake su kuma matsalar yaran da suka bari ya zame masu matsalar rashin kwanciyar hankali. Don haka dole ki samo amsar makomar ƴaƴanki kamin ma ki cewa miji ka sake ni.

5. Sabuwar Rayuwa? Kamin ki buɗe baki kice a sake ki, ki samu amsar yadda zaki fuskanci sabuwar rayuwar da za ki shiga ba kuma bayan an sake ki ba ki riƙa bin tsohon mijin na ki kina neman taimakon sa.

Dole ne ki samu amsar yadda za ki ci gaba da ɗaukar ɗawainiyar kanki koda kina da masu miki baza su miki yadda miji zai miki ba.

Dole ne ki samu amsar wajen da za ki zauna ko da kuwa kina da mazauni zai bambamta da zaman gidan miji.

Dole ne ki samu amsar yadda za ki ci gaba da kare kanki kamar yadda aure ya rufa miki asiri.

Waɗannan sune wasu daga cikin tambayoyin da ya kamata duk mace mai neman saki ta soma samun amsar su kamin tayi azarɓaɓin neman a saketa.

Shi dai zaman aure da haƙuri ne da kuma kau da kai. Duk matsalar da kike fuskanta a gidan mijinki da har kike neman saki akansa, wata na can tana haƙuri da matsalar data fi taki.

Ma’aurata a riƙa haɗawa da haƙuri. Mata a daina neman saki cikin fushi ba tare da duban abubuwan da zasu je su dawo ba. Allah Ya bamu haƙurin zama da juna.

Bilkisu Tijjani
+ postsBio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

July 5, 2026
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 27, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026
Next Post
Ana Tuhumar Mutum Biyu Kan Dala 461,600 Da Suka Yi Ɓatan Dabo A Filin Jirgin Saman Kano

Ana Tuhumar Mutum Biyu Kan Dala 461,600 Da Suka Yi Ɓatan Dabo A Filin Jirgin Saman Kano

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.