ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ana Tuhumar Mutum Biyu Kan Dala 461,600 Da Suka Yi Ɓatan Dabo A Filin Jirgin Saman Kano

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago

Hukumar EFCC ta fara bincike kan wasu maza biyu, Jamilu Shuaibu Waya da Usman Namadi, bisa zargin rashin bayyana jimillar Dala 461,600 a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Jihar Kano.

Mai magana da yawun hukumar EFCC ya bayyana a wata sanarwa ranar Litinin cewa an kama waɗanda ake zargin ne a ranar Juma’a, 8 ga Mayun 2026, bayan sun iso Nijeriya daga Dubai cikin jirgin Ethiopian Airlines ET941.

Rahoton ya ce jami’an Kwastom shiyyar Kano/Jigawa ne suka tare su yayin binciken bayyana kuɗaɗen waje da ake gudanarwa a filin jirgin.

ADVERTISEMENT

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta bayyana cewa da farko waɗanda ake zargin sun bayyana Dala 130,000 da kuma Dala 180,000 bi da bi a wajen rajistar bayyana kuɗaɗe.

Sai dai bayan ƙarin bincike da jami’an kwastam suka gudanar, an gano wasu ƙarin kuɗaɗe da ba a bayyana ba da aka ɓoye a jikinsu.

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

Hukumar ta ce an gano ƙarin Dala 120,000 a wajen wanda ake zargi na farko, wanda ya sa jimillar kuɗin da ke hannunsa ta kai Dala 250,000, yayin da aka gano ƙarin Dala 31,600 a wajen na biyun, wanda ya sa jimillar kuɗinsa ta kai Dala 211,600.

Rahoton ya ce kuɗaɗen da ba a bayyana ba sun saɓa wa sashe na 3 da na 4 na dokar hana safarar kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya ta shekarar 2022.

Da yake jawabi yayin miƙa waɗanda ake zargin ga EFCC, muƙaddashin Kwanturola na Kwastam na yankin, Mataimakin Kwanturola UU Adamu, ya yaba da haɗin gwiwar da ke tsakanin Hukumar Kwastam da EFCC wajen yaƙi da laifukan kuɗi da safarar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba a ƙasar nan.

Adamu ya ce: “Bari na nuna godiya bisa ci gaba da haɗin gwiwa da Daraktan EFCC na shiyyar Kano saboda goyon bayan da suke bayarwa wajen cimma manufofinmu na yaƙi da safarar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba.”

Daraktan EFCC na shiyyar Kano, Mataimakin Kwamandan EFCC, ACE1 Friday S. Ebelo, ya tabbatar wa Hukumar Kwastam cewa za su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

“EFCC za ta gudanar da cikakken bincike ba tare da sassauci ba a kan wannan batu. Za mu gurfanar da lamarin yadda ya kamata domin tabbatar da cewa masu karya dokokin hana safarar kuɗaɗe sun fuskanci hukunci yadda ya dace,” in ji Ebelo.

Ya kuma yaba wa Hukumar Kwastam bisa ci gaba da haɗin gwiwa da EFCC, yana mai cewa haɗin kai tsakanin hukumomi na da muhimmanci wajen yaƙi da laifukan kuɗi.

Ebelo ya ƙara da cewa haɗin gwiwar tsakanin hukumomin biyu na ƙara ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi wajen daƙile safarar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba a kan iyakokin Nijeriya.

Bayan miƙa waɗanda ake zargin a hukumance, an kai su tare da kuɗaɗen da aka ƙwato da sauran kayayyakin shaida zuwa ofishin EFCC na shiyyar Kano, inda ake ci gaba da bincike.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya

An Kama ‘Yan Nijeriya Huɗu A Indiya Bisa Zargin Damfara Ta Intanet

LABARAI MASU NASABA

Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

July 13, 2026
Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

July 13, 2026
Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

July 13, 2026
Me Ya Sa Ake Ganin Afrika Na Da Damar Taka Rawa A Tsarin Tattalin Arzikin Duniya?

Me Ya Sa Ake Ganin Afrika Na Da Damar Taka Rawa A Tsarin Tattalin Arzikin Duniya?

July 13, 2026
Jiragen Kasan Sin Sun Yi Tafiye-Tafiyen Fasinjoji Sama Da Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Jiragen Kasan Sin Sun Yi Tafiye-Tafiyen Fasinjoji Sama Da Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

July 13, 2026
Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

July 13, 2026
Majalisar Gudanarwa Ta Sin Ta Wallafa “Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15 Kan Kiyaye Lafiyar Al’ummar Kasar”

Majalisar Gudanarwa Ta Sin Ta Wallafa “Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15 Kan Kiyaye Lafiyar Al’ummar Kasar”

July 13, 2026
Xi Zai Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026, Inda Zai Gabatar Da Muhimmin Jawabi

Xi Zai Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026, Inda Zai Gabatar Da Muhimmin Jawabi

July 13, 2026
Sin Ta Fitar Da Rahoton “Sake Karyata Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

Sin Ta Fitar Da Rahoton “Sake Karyata Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 13, 2026
Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Nazarin Tattalin Arziki Tare Da Masana Da ‘Yan Kasuwa

Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Nazarin Tattalin Arziki Tare Da Masana Da ‘Yan Kasuwa

July 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.