ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ƙara Faɗaɗa Tallafin Ilimi A Jihar Kogi

by Rabi'u Ali Indabawa
1 month ago
kogi

Kamfanin Simintin Dangote, reshen Obajana, ya ƙara faɗaɗa ayyukan tallafinsa ga al’umma ta hanyar raba kayayyakin karatu ga ɗalibai a Lakwaja, babban birnin Jihar Kogi.

Babban Manajan Sashen Harkokin Jin Daɗin Al’umma na Dangote Cement, reshen Obajana, Ademola Adeyemi, ya bayyana cewa wannan wani ɓangare ne na shirye-shiryen alhakin zamantakewa na kamfanin (CSR).

A cewarsa, wannan tallafin ilimi da aka kai Lokoja ya biyo bayan irin wannan rabon kayayyakin karatu da kamfanin ya yi wa ɗaliban makarantun gwamnati a al’ummomin Oyo, Iwaa, Obajana da Apata. Haka kuma, kamfanin ya ƙaddamar da wani asibiti na miliyoyin naira a Obajana, wanda ya ƙara wa jerin ayyukan ci gaban al’umma da suka haɗa da asibitocin da aka gina a al’ummomin Iwaa da Oyo.

ADVERTISEMENT

Ya ce tsawon shekaru, kamfanin ya zuba biliyoyin Naira wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaban al’ummomin da ke karɓar baƙuncinsa, ciki har da shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki, gina hanyoyi da samar da ruwan sha mai tsafta. Ya kuma jaddada cewa kamfanin zai ci gaba da faɗaɗa irin waɗannan ayyuka.

Adeyemi ya ƙara da cewa shirye-shiryen kula da alhakin zamantakewa na kamfanin suna tafiya da manufofin gwamnati na ci gaba, kuma ana aiwatar da su ne ta hanyar haɗin gwiwa mai ɗorewa da amfani ga ɓangarorin biyu.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar kuma aka raba wa manema labarai a Lokwaja, an bayyana cewa kayayyakin karatun da aka raba sun haɗa da jakunkunan makaranta, littattafan rubutu, kayan rubutu, kwalaben ruwa da sauran muhimman kayan koyo domin inganta karatun ɗalibai da kuma shirya su domin shiga sabon zangon karatu.

Sanarwar ta ce wannan tallafin ya biyo bayan binciken tantance buƙatun da Kamfanin Simintin Dangote ya gudanar, inda aka gano cewa ɗalibai da dama suna zuwa makaranta ba tare da jakunkunan makaranta ba, yayin da wasu kuma ke ɗaukar littattafansu a hannu. Haka kuma an gano cewa ɗalibai da dama ba su da muhimman kayan koyo kamar littattafan rubutu, alƙaluma, fensir da sauran kayan karatu na yau da kullum.

Da yake jawabi, Babban Malamin Makarantar UBE LGEA School, St. Luke Model II, Adankolo, a Ƙaramar Hukumar Lakwaja, Abubakar Sanni, ya nuna matuƙar godiyarsa ga mahukuntan Kamfanin Simintin Dangote bisa wannan tallafi.

Ya kuma gode wa Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, saboda faɗaɗa shirin tallafin ilimi na kamfanin har zuwa makarantun da ke babban birnin jihar, ba tare da taƙaita shi ga al’ummomin da kamfanin ke gudanar da ayyukansa kaɗai ba.

Waɗanda suka amfana da tallafin, shugabannin makarantu, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki a al’umma sun bayyana godiyarsu ga Kamfanin Simintin Dangote bisa wannan taimako da ya zo a kan lokaci, tare da yi wa kamfanin addu’ar samun ci gaba da nasara a ƙoƙarinsa na inganta rayuwar al’umma da tallafa wa ci gaba mai ɗorewa.

kogi
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Adadin Masu Amfani Da Intanet A Sin Ya Kai Sama Da Mutane Biliyan 1.12

Yadda Na Yi Amfani Da Intanet Wajen Bunƙasa Sana’ata —Fatima Mubaraka

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.