Tawagar kwararrun likitocin kasar Sin ta uku ta isa birnin Kinshasa, fadar mulkin kasar Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo, a jiya Asabar, don tallafawa aikin dakile annobar Ebola a kasar.
Wakilin ma’aikatar lafiya ta kasar Congo Kinshasa, Luku Maleyo Marius, ya tarbe likitocin na kasar Sin a filin jiragen sama, inda ya ce, har yanzu ana cikin mawuyacin hali a fannin tinkarar cutar Ebola a kasar, kuma zuwan kwararrun likitoci Sinawa zai samar da gagarumin taimako a fannin ayyukan sa ido kan yanayin bazuwar annobar, da kula da majiyyata, da binciken kwayoyin cuta, da dai sauransu.
A nata bangare, ma’aikatar lafiya ta kasar Congo Kinshasa ta ce tana son karfafa hadin gwiwa tare da bangaren Sin, a kokarin inganta ayyukan tinkarar annobar.
Sa’an nan a madadin likitocin kasar Sin, Yang Xiaochen, wanda shi ne shugaban tawagar kwararrun likitocin Sin ta uku, ya ce shi da abokan aikinsa za su bayar da taimako bisa hakikanan bukatun da ke akwai a wurin, kuma a kan tushen ayyukan da tawagogi 2 na likitocin Sin suka yi.
Ban da haka, Yang ya ce, za su karfafa cudanya da hadin gwiwa tare da hukumomin kiwon lafiya na Congo Kinshasa, da abokan hulda na kasa da kasa, a kokarin bayar da gudunmowa ga yunkurin gaggauta kawar da annobar Ebola ta wannan karo. (Bello Wang)














