Kwanan nan, na karanta wasu bayanai da suka shafi yadda kasar Najeriya ke fitar da karin kayayyaki zuwa kasar Sin.
Misali a jaridar Vanguard, an ce darajar kayayyakin da Najeriya ta fitar zuwa kasar Sin a farkon rabin shekarar bana ta kai dalar Amurka biliyan 2 da miliyan 250, jimillar da ta karu da kaso 81 bisa ta makamancin lokacin a bara. Kana wani labari daga jaridar LEADERSHIP ya ce, sakamakon yadda kasar Sin ta soke harajin fito da ta kan karba kan kayayyakin kasashen nahiyar Afirka dake da huldar diflomasiyya da ita, kudin kayayyakin da kasar Sin ta shigar daga Najeriya a watan Mayu da na Yunin bana, dukkansu sun karu da kaso 40 bisa jimillar watan da ya gabace su. To, wadannan alkaluma sun nuna cewa, kasar Sin tana kokarin sayen kayayyaki daga kasar Najeriya.
Kana ta hanyar tantance yanayin ciniki a duk duniya, za a fahimci cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa ta fuskar sayen kayayyakin kasashe daban daban. Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, kasashe da yankuna kimanin 80 suna fitar da dimbin kayayyakinsu zuwa kasar Sin, ta yadda kasar ta zama ta biyu a duniya a fannin shigar da kayayyaki daga ketare, cikin shekaru 17 a jere.
Da ma wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma sun ce, wai kasar Sin tana matsawa sauran kasashe lamba a fannin tattalin arziki, sakamakon yadda take fitar da dimbin kayayyaki zuwa kasashen. Sai dai, a bisa alkaluman da muka ambata a baya, mun san cewa kasar Sin ita ma tana kokarin shigar da kayayyaki daga ketare, don neman samun daidaiton ciniki, da more damar raya tattalin arziki tare da sauran kasashe.
Dimbin mutanen kasashen yamma sun yarda da tsarin “Cin nasara daga faduwar wani bangare”. Amma ra’ayin Sinawa ya sha bamban da nasu. A ganin mutanen kasar Sin, yunkurinsu na raya tattalin arziki ba ya nufin neman yin babakere a duniya, sai dai domin ci gaban tattalin arziki ya amfanar da karin mutane.
Wannan tunani nasu ya tabbatar da manufar kasar Sin ta neman samun ci gaba na bai daya tare da sauran kasashe daban daban. (Bello Wang)














