ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Umarci DSS Ta Mutunta Umarninta Kan Shari’ar Filin Firo Na Bauchi

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
3 months ago

Babbar kotun Jiha mai zamanta a Bauchi ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Aliyu Bin Idris ta gargaɗi hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da kada ta karya umarnin kotu da ya hana ta shiga wani babban fili da ake takaddama a kansa da ke ƙauyen Firo a ƙaramar hukumar Ganjuwa ta jihar.

Mai Shari’a Idris ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Alhamis yayin sauraron ƙara mai lamba BA/251/2026, wadda masu filin, Hajiya Fatima Abdullahi, Ishaq Mohammed Kobi da Murtala Isma’il, suka shigar.

Masu ƙarar sun kai ma’aikatar filaye da safiya ta Jihar Bauchi, Babban Lauyan Jihar Bauchi, da kuma hukumar tsaron farin kaya (DSS) da ke Jihar Bauchi gaban kotun ne bisa neman kotun ta hana su ƙoƙarin mamaye babban filin.

ADVERTISEMENT

Kotun ta sake jaddada umarninta na baya wanda ya hana DSS da jami’an ma’aikatar filaye shawagi ko shiga filin da ake taƙaddama a kansa da ke yankin Dam ɗin Gubi a ƙauyen Firo har sai an kammala shari’ar.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan zaman kotun, lauyan masu ƙara, Barista Abdullatif Gwani Isa, ya bayyana cewa masu ƙarar sun shigar da ƙarar ne domin kare haƙƙinsu na mallakar filin da suke iƙirarin sun mallaka bisa doka.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Ya yi zargin cewa jami’an DSS tare da haɗin gwiwar wasu jami’an Ma’aikatar Filaye sun shiga babban filin gonar ba tare da sanarwa, tuntuɓa, amincewa ko wata sahihiyar izini ta doka ba, sannan suka fara dubawa da yi mata alama domin yiwuwar ƙwace domin kokarin mallakar da filin wa hukumar DSS.

A cewarsa, masu ƙarar sun nemi kariyar kotu, inda suka samu umarnin wucin gadi da ya hana waɗanda ake ƙara katsalandan ko amfani da filin har sai an kammala Shari’a kan lamarin.

Ya ce kotun ta sake nanata cewa DSS da jami’an ma’aikatar su mutunta umarninta, bayan zargin cewa har yanzu ana ci gaba da wasu ayyuka a filin duk da kasancewar umarnin kotun yana nan.“Kotun ta hana DSS da jami’an Ma’aikatar Filaye shiga gonar domin ƙwacewa, ko shata filin har sai an bi dukkan matakan doka da suka dace,” in ji shi.

Barista Isa ya bayyana cewa yayin da Ma’aikatar Filaye ta riga ta gabatar da martaninta tare da miƙa wa masu ƙara kwafin takardun amsarta, DSS har yanzu ba ta gabatar da nata martani ba.Ya ƙara da cewa an ɗage sauraron shari’ar ne saboda ma’aikatar filayen ba ta miƙa kwafin amsarta ga DSS ba.

Lauyan ya ce Mai Shari’a Idris ya sake jan kunnen lauyoyin DSS da Ma’aikatar Filaye da su tabbatar da cewa waɗanda suke wakilta sun bi umarnin kotu yadda ya dace kafin ranar zama ta gaba.Isa ya jaddada cewa masu ƙarar ba sa adawa da duk wata halastacciyar amsar fili da gwamnati za ta yi, muddin an bi tanade-tanaden dokar amfani da filaye (Land Use Act), ciki har da bayar da sanarwar neman amsar fili da kuma biyan diyya mai tsoka idan ya zama dole.Ya nuna kwarin gwiwar cewa adalci zai tabbata daga ƙarshe.

Ita ma da take magana, Hajiya Fatima Abdullahi ta ce ita da sauran masu ƙarar su ne halastattun masu filin, domin sun mallake shi ne ta hanyar saye da kuma rabon filaye da hukumar ƙaramar hukumar Ganjuwa ta yi musu bisa ka’ida.

Ta ce tun bayan samun filin suna amfani da shi ba tare da wata matsala ba, ciki har da noma da kuma rabon wasu sassa domin sayarwa, har sai da rikicin da ake ciki yanzu ya taso.

A cewarta, a shekarar 2020, Ma’aikatar Filaye ta karɓi wasu filaye daga mutane da dama domin samar da makarantar horaswa ta DSS. Ta bayyana cewa wannan ƙwacewar ta takaita ne ga wani yanki da aka fayyace, kuma ba ta shafi filin da ake taƙaddama a kansa yanzu ba.Fatima ta kuma bayyana cewa a shekarar 2024, DSS ta nuna sha’awar sayen wasu ƙarin filaye daga gare ta. Sai dai bayan ta aika wasiƙar nuna amincewarta da sayar da filayen, hukumar ba ta sake ce mata komai ba balle ta biya ta kuɗin, lamarin da ya sa ta ci gaba da tallata filayen ga masu sha’awar saya.

Ta yi zargin cewa daga baya DSS tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Filaye sun shiga filin ba tare da izinin doka, sanarwar ƙwace fili ko biyan diyya ba. A cewarta, hukumar ta fara kafa alamomin iyaka (beacons) da kuma yi wa filin shata a wani yunƙuri da ta bayyana a matsayin ƙoƙarin ƙwace filin ba bisa ƙa’ida ba.

Fatima ta kuma yi zargin cewa wasu jami’an DSS sun yi wa masu ƙarar barazana, inda suka gargaɗe su cewa duk wanda ya shiga ko ya yi aiki a filin za a harbe shi, abin da ta ce ya hana su amfani da haƙƙinsu na mallaka da amfani da filin.Ta yi ƙorafin cewa wani ɓangare na filin mallakin marayu ne da take kula da su, tare da roƙon kotu da ta tabbatar an yi adalci.

Daga bisani, Mai Shari’a Aliyu Bin Idris ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga Yuli, 2026, domin sauraron buƙatar da aka gabatar, bayan ba da damar kammala isar da takardun martanin Ma’aikatar Filaye ga DSS yadda ya kamata.

Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ‘Yansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekara 70 Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Binciken CGTN Ya Nuna Yadda Cimma Yarjejeniya Tsakanin Amurka Da Iran Ta Fallasa Koma Bayan Tasirin Amurka A Harkokin Duniya

Binciken CGTN Ya Nuna Yadda Cimma Yarjejeniya Tsakanin Amurka Da Iran Ta Fallasa Koma Bayan Tasirin Amurka A Harkokin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.