ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Neman Belin Malami

by Leadership Hausa
8 months ago

Daga Rabiu Ali Indabawa

Wata Kotun Koli ta Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatun beli da tsohon Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), da wasu mutum biyu da ake zargi da safarar kudi.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya ki amincewa da bukatar a ranar Talata domin bai wa masu kara damar mayar da martani a rubuce yadda doka ta tanada.

ADVERTISEMENT
  • Sin Ta Jaddada Hadin Gwiwa Kan Sauyin Yanayi Da EU Inda Ta Lashi Takobin Daukar Matakai Kan Ka’idojin Cinikayya Na Rashin Adalci
  • Gwamnatin Jigawa Ta Lalata Kwalaye 5,520 Na Taliyar Yara Da Lokacin Ingancinta Ya Ƙare

Ya bayar da umarnin a tsare Malami da dansa Abdulaziz Malami, da kuma wata Hajia Bashir Asabe, ma’aikaciyar kamfanin Rahamaniyya Properties Ltd, a Cibiyar Gyaran Hali ta Hukumar Gidajen Yari ta Nijeriya da ke Kuje, Babban Birnin Tarayya (FCT).

Tun da farko, lauyan masu kara, Kelechi Ekele (SAN), ya yi adawa da bukatar belin da lauya mai karewa, Joseph Daudu (SAN), ya shigar, yana mai cewa an kawo bukatar ne ba tare da sanarwa ba, wanda ba za a iya mayar da martani a baki a gaban kotu ba.

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta zargi Malami, dansa da Asabe da hada kai wajen boye dukiyoyi da ake zargin sun samo asali ne daga haramtattun aiki, wadanda aka baza a manyan wurare a birnin Abuja da jihohin Kebbi da Kano.

Sai dai dukkan wadanda ake tuhuma sun musanta laifukan da ake zarginsu da su.

A cikin tuhumar, an zargi Malami da cewa tsakanin watan Yuli 2022 da Yuni 2025, ya yi amfani da kamfanin Metropolitan Auto Tech Ltd wajen boye haramtattun kudi Naira 1,014,848,500 da ke cikin asusun Sterling Bank Plc mai lamba 0079182387, sannan kuma ya sake amfani da kamfanin wajen boye haramtattun jimillar kudi Naira 600,013,460.4 a wannan asusun.

Haka kuma, an kara zargin Malami da cewa a watan Maris 2021, ya yi amfani da wadannan kudaden da aka ajiye a matsayin jinginar samun rancen Naira miliyan 500 daga bankin ga kamfanin Rahaan Hotels Ltd.

Gwamnatin Tarayya ta kuma zargi Malami da sauran wadanda ake tuhuma da cewa, a wani lokaci a watan Nuwamba 2022, sun boye haramtattun kudi Naira miliyan 500 da aka biya wa Efab Properties Ltd domin sayen katafaren gida mai dakuna biyu (ludury dupled) da ke Amazon Street, Plot 3011, cikin Cadastral Zone A06, Maitama District, Abuja.

An kara zargin wadanda ake tuhuma da cewa, a wani lokaci a watan Satumba 2024, sun hada kai wajen boye haramtattun kudi Naira 1,049,173,926.13 da aka biya ta asusun Union Bank Plc na Meethak Hotels Ltd, asusun ajiyar kudi (Sabings Account) mai lamba 0179011105, tsakanin watan Nuwamba 2022 da Satumba 2024.

Haka kuma, an zargi iyalan Malami da cewa tsakanin watan Nuwamba 2022 da Oktoba 2025, sun karbi iko da kudi Naira 1,362,887,872.96 da aka biya ta asusun ajiyar kudi na Meethak Hotels Limited a Union Bank Plc.

Bugu da kari, tare da Hajia Asabe Bashir, Malami ya boye haramtattun kudi Naira miliyan 700 da aka biya domin sayen kadarar da aka bayyana a matsayin lamba 3, Onitsha Crescent, Area 11, Garki, Abuja (Hamonia Hotels Ltd).

Tsakanin watan Satumba 2020 da Disamba 2020, an zargi wadanda ake tuhuma da hada kai wajen boye kudi Naira miliyan 850,000,000 da aka biya domin sayen kadarar da aka bayyana a matsayin Plot 683, Jabi District, Cadastral Zone B04 (Meethak Hotels Ltd, Jabi).

Tun da farko kuma, a watan Fabrairu 2018, ana zargin su da sayen kadarar da ke lamba 3, Rhine Street, Maitama, Abuja (Meethak Hotels Ltd) kan jimillar kudi Naira miliyan 430.

Bugu da kari, an zargi wadanda ake tuhuma da cewa tsakanin watan Maris da Yuni 2021, sun boye haramtattun kudi Naira miliyan 325 domin sayen kadarar da ke lamba 1241B, Asokoro District Zone (lamba 11A, Yakubu Gowon Crescent, Asokoro).

Haka kuma, tsakanin watan Nuwamba 2015 da Janairu 2016, ana zargin su da boye haramtattun kudi Naira miliyan 120 domin sayen kadarar da aka bayyana a matsayin lamba 27, Efab Estate, 5th Abenue, 59th Crescent, Gwarimpa, Abuja.

Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura

MASU ALAKA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Labarai

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Next Post
Shari’ar Annabi SAW Ta Fi Ta Sauran Annabawa Sauƙi

Shari'ar Annabi SAW Ta Fi Ta Sauran Annabawa Sauƙi

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.