ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Gwamnatin Tarayya Na Fara Aikin Gina Mayankar Zamani A Garin Jos

by Abubakar Abba
2 months ago
Mayanka

A ƙoƙarinta na zamanantar da Mayankar dabbobi da ƙara bunƙasa fannin gwamnatin tarayya, ta fara aikin gina katafariyar mayankar da za a iya yanka Shanu kimanin 500 a kowace rana.

Babban Ministan Ma’aikatar Bunƙasa Kiwon DabbobiIdi, Mukhtar Maiha, ya sanar da haka ne a jawabinsa, yayin ƙaddamar da aikin a Jihar Filato.

Ya danganta aikin a matsayin wanda zai taimaka wajen zuba jari a fannin da ƙara samar da wadataccen abinci da kuma samar da aikin yi ga fannin na kiwon wannan ƙasa.

ADVERTISEMENT

Maiha ya sanar da cewa, Mayankar za ta samar da tsarin sarrafa Nama na zamani, inda hakan zai yi daidai da yadda ake gudanarwa a faɗin duniya.

Ya ƙara da cewa, tsarin zai kuma ƙara taimaka wa gwamnatin tarayya, kan ƙoƙarin da ta ke yin a ci gaba da haɓaka fannin na kiwon dabbobi a ɗaukacin faɗin ƙasar.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

A cewarsa, wannan aikin ana sa ran, zai samar da ayyukan yi na kai tsaye, da waɗanda ba na kai tsaye ba daga tsakanin 7,000 zuwa 10,000 a ɗaukacin fannin na kiwon dabbobi a ƙasar nan.

Ya ci gaba da cewa, aikin zai kuma ƙara inganta duba lafiyar dabbobi da jigilar Naman da aka sarrafa na dobbobin, musamman ta hanyar sanya Naman a cikin na’urar sanyi ta zamani tare da kuma ƙara samar Ƙiraza.

Kazalika, a Mayankar za a rinƙa sarrafa ƙashin dabbobi da Jininsu da ƙasusuwansu da sauran makamantansu, inda za a sarrafa su, domin sayarwa.

Ministan ya bayyana cewa, an zaɓo Jihar Filato domin gudanar da aikin ne, duba da cewa; ta kasance ingantacciyar ƙasar yin noma mai kyau tare da mayar da hankali a ɓangren kiwo, musamman na dabbobi.

Ya yi nuni da cewa, Filato ta kuma kasance tana da kyakkyawan yanayi tare da kuma kasancewa cibiyar gudanar da bincike kan lafiyar dabbobi, wato NƁRI da ke a Ɓom.

A nasa jawabin, gwamnan jihar ta Filato, Caleb Mutfwang, ya danganta wannan haɗakar a tsakanin gwamnatin tarayya da kuma ma’aikatar kula da kiwon dabbobi ta tarayya, a matsayin wani mataki na amfana da fannin na kiwon dabbobi.

Mutfwang, wanda aka wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa, Filato na goyon bayan yin amfani da Ruga ta zamani, musamman domin a ƙara bunƙasa fannin kiwon dabbobi a ɗaukacin faɗin jihar tare da ƙara haɓaka fannin tattalin arziƙin jihar.

Shi kuwa a nasa jawabin, Jami’i na ƙasa mai kula da shirin bunƙasa kiwon dabbobi da tallafawa iyalai (L-PRES), Dakta Sanusi Abubakar, ya sanar da cewa; Mayankar ta kai mataki na duniya, musamman wajen samar da ingantacce kuma tsaftattacen Nama.

Ya ƙara da cewa, Mayankar za ta kuma taimaka wajen janyo hankalin masu zuba jari tare da ƙara ƙarfafa fannin kiwon dabbobi na ƙasar.

A cewarsa, Bankin Duniya ne ya taimaka wa aikin, wanda kuma Gwamnatin Jihar Filato, za ta wanzar da shi.

 Ya ce, idan an kammala aikin, ana sa ran zai kasance wanda sauran yankunan da ke maƙwabtaka da Filato, su ma za su amfana da shi, musamman wajen adana Nama da kuma rabar da shi ko tura shi zuwa gurare daban-daban.

Mayanka
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Sin Ta Habaka Karfin Soja Ne Don Kare Ikon Mallakar Kasa Da Muradun Ci Gaba

Sin Ta Habaka Karfin Soja Ne Don Kare Ikon Mallakar Kasa Da Muradun Ci Gaba

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.