ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kuskure Goma (10) Da Matan Aure Ke Yi A Gidan Miji

by Bilkisu Tijjani
4 months ago
aure

Na (9) dana (10) su ne mafi muni

1. Tattauna sirrin matsalolin gidan miji da abokai da dangi:

A kowane gidan aure ana samun matsaloli, sai dai masu hankali acikin matan aure ke boyewa su bar komai a wurin Allah. Daukan sirrinki da mijinki ki sanar da wasu yana kawo babbar matsala a rayuwar aure.

ADVERTISEMENT

2. Yawan tattauna matsalolin miji da kushe kokarinsa a gaban ‘ya’yansa:

Wannan yana sa yara su raina kokarin da mahaifinsu ke yi acikin gida

LABARAI MASU NASABA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

3. Cusawa yara kiyayyar amaryar mahaifinsu (kishiya):

Wata rana za ki iya mutuwa ki bar yara a hannun kishiya ko rashin lafiya mai tsanani. To idan kin cusa musu kiyayyar, wannan zai iya haifar matsala babba a tsakaninsu.

4. Kiyayyar yaran kishiya da neman ganin bayansu:

Shin ko kin san cewa Allah zai iya daukaka ‘ya’yan kishiryarki su zamo manyan mutane masu daraja wata rana?

Sannan kuma su zama sune masu daukan nauyinki, to idan Allah ya kaiki wannan lokacin da wanne ido za ki kallesu.

5. Gasar haihuwar yara domin samun kaso mafi girma acikin gadon dukiyar miji:

Shin ko kin san cewa mijinki zai iya talaucewa kamin mutuwarsa? Ko kuma keki da yaran ku rigashi mutuwa.

6. Tunanin cewa miji zai mutu ya barki da yara a cikin wahala:

Waye ya sanar da ke cewa miji ke fara mutuwa ya bar matarsa? Mata sun fi yawan mutuwa su bar mazajensu sanadiyyar (haihuwa, hawan jini, ciwon sikari, tashin gobara a gida, kunar ruwan zafi, da sauransu.

Idan ki ka je assibiti, zaki samu mafi yawan masu jinya a (Dakin karban agaji na gaggawa na mata, da ICU) mata ne da kananan yara, kalilan ne maza acikinsu.

7. Kyauta acikin dukiyar miji ba tare da saninsa ba:

Dukiyar miji amana ce a gareki, dole ki sanar dashi duk abunda za ki aikata acikin dukiyarsa.

Ko bako zai shigo gida (mace ko namiji) dole ki sanarda miji domin neman yardarsa da amincewarsa.

8. Fifita bukatun naki dangi sama da dangin miji:

‘Yan uwa da dangin miji su ne sukafi kusanci dashi sama da dangin matarsa, kar ki tilasta mijinki yiwa danginki dawainiyar da baya yiwa nashi dangi.

9. Rashin godiya da hango ni’imar gidan wasu:

Dawainiyar gidan aure tana da yawa sosai, sai jarumi acikin maza ke iya daukar nauyin matarsa da yara na tsawo shekaru 10, 20, 30, ko 40

Abinci, sutura, sabulai, magani, ruwan sha, kudin lantarki, kudin gas, kudin makarantar yara, kudin tafiya mataranta da kai yara makaranta.

Wallahi duk matar dake raina kokarin mijinta, ba zatayi karshe mai kyau ba.

10. Sabawa miji da goyon bayan yara zuwaga barna:

Duk abunda yara ke aikatawa acikin gida, mahaifiyarsu ta san komai.

Wasu mata za su goyi bayan yara zuwaga barna saboda son zuciya irin nasu.

Idan miji ya hana yara fita, sai bayan mijin yaje aiki ko kasuwa sai mahaifiyarsu ta basu izinin fita.

Idan miji ya hana yara zuwa biki, mahaifiyarsu ta basu izini.

Idan miji ya hana yara fita babu hijabi, sai mahaifiyarsu ta basu damar fita da gyale.

Idan miji ya hana yara fita yawon banza, ko mu’amala da abokan banza, sai mahaifiyarsu ta basu izini.

Idan wani abu ya faru marar kyau, sai mahaifiyarsu tace kaddara ce kowa da irin tasa.

Matan aure
Bilkisu Tijjani
+ postsBio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

July 5, 2026
Matan aure
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 27, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026
Next Post
Matan aure

Aure Ba Sana’a:Imani Ko Ganganci?

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.