ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwararan Sauye-sauyen Da Obi Da Kwankwaso Suka Jawo A Siyasar Nijeriya Gabanin Cikar Wa’adin INEC

by Sulaiman and Yusuf Shuaibu
4 months ago
Obi

Tsohon gwamnan Jihar Anambra, Mista Peter Obi da takwaransa na Jihar Kano, Sanata Musa Kwankwaso, da wasu sun bar jam’iyyar ADC tare da komawa NDC, wanda hakan ya janyo kwararan sauye-sauye a cikin siyasar Nijeriya a halin yanzu.

Lalle al’umma na cikin tashin hankali yayin da jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa ke cikin gasa ta sake tsari kafin cikar wa’adin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), na ranar 10 ga Mayu, wa’adin mika rajistar mambobin jam’iyyu.

Biyo bayan hukuncin kotun koli a ranar Alhamis da ta gabata, wacce ta sanya babban jam’iyyar adawa ta ADC da jam’iyyar PDP, a matsayin jam’iyyu mara tabbas, kamar yadda wani shugaba na siyasa ya fada a daren jiya cewa, manyan ‘yan siyasa masu adawa suna barin dukkan jam’iyyun biyu zuwa wasu jam’iyyun don samun damar yi takara a 2027.

ADVERTISEMENT

A karshen mako, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya sauya sheka daga PDP jam’iyyar APM, shi ma dan takarar shugaban kasa a 2023 na jam’iyyar LP, Mista Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Musa Kwankwaso, sun jagoranci mutanensu masu yawa, wanda suka bar ADC suka kuma koma NDC.

Domin tabbatar da wannan mataki, sun yi wani taron a Abuja tare da tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson, da sauran shugabannin NDC.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Kamar yadda yake, wannan mako ne mai matukar muhimmanci a tsarin zabukan shekarar 2027. Domin cancantar yin takara a kowace mukami a shekara mai zuwa, dole ne wanda yake son takara ya kasance mamba mai rajista na jam’iyyar siyasa. Ana sa ran karin sauyin sheka a wannan makon.

Tsarin kujeru a majalisar dattawa da majalisar wakilai zai kuma canza yayin da ‘yan majalisa suke canza jam’iyyunsu na asali. Yawancin jam’iyyun siyasa sun tsara abubuwan da za su faru tun daga yau.

Wannan na fitowa ne yayin da fadar shugaban kasa ta yi dariya da Obi kan ficewarsa daga jam’iyyar ADC, ko da yake wata kungiya ta yi gargadi kan APM da NDC suna da suna daya a matsayin mai ba da shawarwari na shari’a.

Obi da Kwankwaso da sauran shugabannin ADC da suka sauya sheka ciki har da Sanata Bictor Umeh da Sanata Kabir Marafa da Sanata Aishatu Dahiru Binani da Sanata Kabir Gaya da Wakili Ehiozuwa Johnson Agbonayinma da Wakili Bictor Ogene, da tsohon shugaban IPAC, Cif Peter Ameh, sun isa gidan Dickson da misalin karfe 5:14 na yamma kuma suka yi taro na sirri da tsohon gwamnan Jihar Bayelsa.

Wasu a taron sun hada da shugaban jam’iyyar NDC, Moses Cleopas, tare da mambobin kwamitin zartarwa na jam’iyyar.

Bayan tattaunawar sirri, shugabannin NDC sun yi gagarumar tarbi da kuma yin rajista ga Obi da Kwankwaso a matsayin mambobi jam’iyyar NDC.

Obi ya ce yanayin siyasa a yanzu, wanda yake cike da rikice-rikicen cikin gida da yawan shari’o’i a kotu, ya tilasta wa shugabanni da dama neman wasu jam’iyyu. Ya yi kira ga ‘yan siyasa da su mayar da hankali wajen magance talauci da rashin tsaro da wahalar tattalin arziki.

A cewarsa, fifikon Nijeriya dole ne ya kasance a hade da aminci, da arzikin da ake rabawa tare. Ya jaddada bukatar samun kasa mai kyau ba tare da la’akari da asali ba, domin ‘yan kasa su sami damammaki iri daya don yin nasara, kuma yadda iyalai ke rayuwa ba tare da tsoro da rashin tabbas na tattalin arziki ba.

A cikin jawabinsa, Kwankwaso ya jaddada hadin kai da shiga harkokin siyasa cikin himma a matsayin muhimman abubuwa wajen gina kasa mai zaman lafiya da arziki. Ya yaba wa shugabannin NDC. Ya ce tattaunawa da masu ruwa da tsaki sun cimma abubuwa masu muhimmanci, musamman wajen bunkasa ilimi da karfafa matasa da mata.

Ya bayyana NDC a matsayin fiye da jam’iyyar siyasa, yana kiranta a matsayin motar ci gaban al’umma da hadin kai.

Kwankwaso ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya, musamman masu neman mukamai, da su amfana da karamin lokaci da ake da shi don yin rajista da shiga cikin ayyukan jam’iyyar kafin zabe.

Obi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Obi
Yusuf Shuaibu
+ posts Bio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Zargin Kashe Dadiyata: Sufeto Janar Ya Ba Da Umarnin Binciken Wasu Jami’ai

Zargin Kashe Dadiyata: Sufeto Janar Ya Ba Da Umarnin Binciken Wasu Jami’ai

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.