ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyakkyawar Huldar Manyan Kasashe Tushe Ne Na Bunkasuwar Duniya

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 months ago
Kasa

Bisa gayyatar shugaban kasar Sin Xi Jinping, shugaban kasar Amurka Donald Trump na yin ziyarar aiki a kasar Sin daga ranar 13 zuwa 15 ga watan Mayu, ziyarar da ta kasance ta farko da shugaban kasar Amurka ya kawo wa kasar ta Sin cikin tsawon shekaru 9, kuma ganawarsu a wannan karo ta biyo bayan ganarwarsu a Busan a shekarar da ta gabata. Wannan ziyara ta ja hankalin duniya matuka, duba da cewa muhimmancinta ya riga ya wuce huldar da ke tsakanin kasashen biyu.

“Kyakkyawar dangantakar Sin da Amurka mai dorewa ta dace da muradun kasashen biyu, kuma fata ne na al’ummun duniya.” A ‘yan shekarun nan, shugaba Xi ya gabatar da jerin muhimman kalamai game da dangantakar Sin da Amurka, ya kuma yi cikakken bayani kan hanyar da ta dace tsakanin kasashen biyu a sabon zamani.

A ganawarsu ta yau 14 ga wata, shugaba Xi ya jaddada cewa, muradun bai daya tsakanin Sin da Amurka sun fi sabani a tsakaninsu, kuma nasarar kowannensu dama ce ga juna, kuma duniya za ta cin gajiyar kyakkyawar dangantakar Sin da Amurka. A bangarensa, shugaba Trump ya sha bayyana shugaba Xi a matsayin shugaba mai girma. Trump ya ce: “Ina alfahari da kasancewa abokinka, kuma alakar da ke tsakanin Sin da Amurka za ta ci gaba da inganta sama da lokutan baya.”

ADVERTISEMENT

Ingancin dangantakar Sin da Amurka yana shafar zaman lafiyar duniya. A matsayin kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, jimillar tattalin arzikin Sin da na Amurka ta wuce kashi daya bisa uku na duniya baki daya, kuma jimillar cinikayyar kayayyaki a tsakaninsu ta kai kusan kashi daya cikin biyar na duniya. Ko a bara, kudin cinikayyar kasashen biyu ya kai kimanin dala biliyan 560, duk da takkadamar ciniki da suka fuskanta, adadin da ya yi daidai da jimillar tattalin arzikin wata kasa mai matsakaicin karfi a shekara guda.

A halin yanzu, yankin Gabas ta Tsakiya na ci gaba da fama da yake-yake, kuma matsalar zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz na kawo cikas ga tsaron makamashi na duniya, a yayin da ake fuskantar karin matsalolin tsaro wajen amfani da AI, kuma sauyin yanayi da sauran kalubalen duniya suna ta kunno kai. A cikin wannan yanayi mai sarkakiya, ganawar shugabannin Sin da Amurka ta aika da sako mai kyau ga duniya.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Al’ummun duniya suna fatan ganin ganawar shugabannin Sin da Amurka za ta taimaka ga fadada hadin gwiwarsu da kawar da matsalolin da ke tsakaninsu, tare da samar da kwanciyar hankali da tabbaci ga duniya mai fama da rashin tabbas. Kyakkyawar dangantakar Sin da Amurka ba kawai ta dace da muhimman muradun al’ummomin kasashen biyu ba, har ma ita ce fata na al’ummun duniya baki daya. Kazalika, taimakon juna tsakanin Sin da Amurka, ba wai kawai zai amfani kasashen biyu ba ne, har ma zai samar da alfanu ga duniya gaba daya.(Marubuciya: MINA)

Kasa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
  • Sulaiman
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • Sulaiman
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka
Kasa
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Kasa

Yadda Rashin Aikin Yi Ke Jefa Matasa Maula Da Bangar Siyasa

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.