Nijeriya na da dinbin matasa da ke zaman kashe wando daga Arewa har Kudu ba tare da aikin baki ballantana na fari ba lamarin da yake babban kalubale ga tsaron kasa kuma babbar barazana mai zaman kan ta da ke kassara rayuwar matasa.
A dalilin rashin aikin yi da miliyoyin matasa ke fama tuni da dama daga ciki suka fada a cikin mummunar dabi’ar maula da bangar siyasa ba tare da gwamnati da masu ruwa da tsaki a lamarin sun dauki kwararan matakan shawo kan gawurtacciyar matsalar tun gabanin ta fi karfin magancewa.
A bayyane yake cewar Nijeriya na cikin kasashen duniya da ke da mafi yawan matasa a inda sama da kashi 60 zuwa 70 suke matasa masu jini a jika ‘yan kasa da shekaru 30 da ke cikin adadin akalla mutane miliyan 230 na al’ummar kasar.
A kowace shekara a na yaye dimbin dalibai a jami’oi, kwalejojin ilimi da na kimiyya da fasaha da na aikin jinya da ungozoma wadanda ke komawa zaman kashe wando saboda rashin aikin yi lamarin da ke jefa rayuwarsu a cikin mawuyacin yanayi.
Tun a farkon hawansa mulki, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa samar da ayyukan yi na daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa tun daga 2023 zuwa 2026.
A mabambantan jawabansa, Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa na mai da hankali kan karfafa tattalin arziki, tallafawa kanana da matsakaitan sana’o’i da jawo masu zuba jari daga waje domin samar da sabbin ayyukan yi ga matasa.
Akalla ayyukan yi miliyan 50 ne Shugaba Tinubu ya yi alkawarin samarwa ta hanyar bunkasa masana’antu, noma, da tattalin arzikin zamani, sai dai a yayin da gwamnatin ta cika shekaru uku saman mulkii; ‘yan Nijeriya na ci gaba da kukan rashin gani a kasa a alkawulan da Shugaban ya yi wa matasan kasar nan.
A mabambantan lokuta jam’iyyar ADC ta soki gwamnatin Tinubu da gazawa wajen magance matsalar rashin aikin yi a Nijeriya, tana mai cewa halin da matasa ke ciki na zaman kashe wando na barazana ga tsaron kasa da zaman lafiyar al’umma.
Jam’iyyar ta bayyana cewar rashin aikin yi ya jefa miliyoyin matasa cikin talauci da rashin makoma, lamarin da ke kara haddasa matsalolin zamantakewa a fadin kasar nan. A cewar jam’iyyar matasan da ba su da aikin yi na kara fadawa cikin talauci tare da aikata laifuka.
Sai dai jam’iyyar ta yi alkawarin cewa idan aka ba ta dama a zaben 2027 za ta bullo da sabbin tsare-tsare da za su kawo sauyi a fannin samar da ayyukan yi domin za ta fito da tsare-tsaren bunkasa masana’antu, noma da kananan sana’o’i domin samar da ayyukan yi masu yawa da dorewa tare da mayar da hankali kan horas da matasa da fasahar zamani tare da samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari domin bude hanyoyin samun aikin yi a fadin kasar nan.
Rahotannin baya-bayan nan a 2025–2026, sun nuna cewar duk da raguwar kididdigar rashin aikin yi a hukumance, matsalar rashin aikin yi da karancin kwakkwaran aiki a tsakanin matasa a Nijeriya har yanzu matsala ce mai zaman kan ta.
A wani rahoto a 2025 ya bayyana cewa kusan matasa miliyan 80 ne a Nijeriya suke zaman kashe wando ba su da aikin yi wanda ke wakiltar kashi 53% na jimillar matasan kasar, lamarin da ke nuna gagarumar matsalar rashin aikin yi da matasa ke fama a kasar da ta fi kowace kasa yawan jama’a a Afirka.
Rahoton kan halin da matasan Nijeriya ke ciki ya bayyana cewa yawaitar rashin aikin yi a tsakanin matasa tare da karuwar matsalar tsaro da kuma raguwar amincewa da gwamnati ya jefa matasan Nijeriya a cikin rauni da wariya a cikin al’umma.
Kwakkwaran rahoton wanda Jonathan Abakpa, jami’in shirye-shiryen matasa da wayar da kai na kungiyar Plan International a Nijeriya ya gabatar, ya nuna cewa sama da rabin matasan kasar har yanzu ba su da aikin yi kuma suna fafutukar ganin sun samu ayyukan yi amma lamarin ya faskara.
Haka ma rahoton ya bayyana cewa akalla kimanin dalibai miliyan 1.7 ne ke kammala karatu daga jami’o’i da kwalejojin fasaha a Nijeriya a kowace shekara, amma tattalin arzikin kasar bai da karfin daukar su a fagen neman aiki yadda ya kamata.
“Wannan ba kawai kididdiga ba ce, yana wakiltar mafalkin da ya kasa tabbata da kuma baiwar da ke ga matasa da aka yi watsi da ita. Matsin rayuwa da rashin mafita na jefa matasa da dama zuwa kauracewa kasa ba bisa ka’ida ba, aikata laifukan yanar gizo da kuma wasu hanyoyin rayuwa masu hadari.”
Bayanai daga kungiyar kwadago ta duniya ya nuna yawan matasa masu shekaru 15–24 da ba su da aikin yi a Nijeriya yana kusan kashi 6.5% wanda shine kididdigar da fitacciiyar kungiyar ta bayyana wanda kason ya nuna irin mawuyacin halin da matasa ke ciki a kasar nan.
Haka ma rahotanni a 2026 sun nuna cewa kusan kashi 90% zuwa sama na matasan da ke aiki suna cikin bangaren ire- iren ayyukan da ba su da tsari, ba su da tabbataccen albashi kuma ba su da kariyar doka.
Bugu da kari an kiyasta cewa miliyoyin matasa na cikin yanayin rashin cikakken aiki ko kuma ba su da aikin yi bakidaya. Rahotanni sun nuna a duk shekara, sama da matasa miliyan 3 zuwa 4 ne ke shiga fagen neman aiki a Nijeriya, amma damar samun aikin yi a gwamnatocin tarayya, jiha da kananan hukumomi da kamfanoni masu tsari ba su kai wannan adadi ba.
Kari da karau akwai yawan matasan da ba su da aikin yi, ba su karatu kuma ba su samun horon sana’a wanda hakan ya kara nuna irin kalubalen da ake fuskanta wajen amfani da dimbin matasan kasar yadda ya kamata.
Sabbin rahotanni sun nuna cewa duk da saukin da aka gani a alkaluman hukumomi, har yanzu rashin aikin yi, karancin aiki mai inganci da kuma dogaro da ayyukan da ba su da tsari suna daga cikin manyan matsalolin ci- gaba da ake fuskanta a Nijeriya.
A wani lokaci can baya shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa kusan kashi 55 cikin dari na matasan Nijeriya na fama da rashin cikakken aikin yi saboda karancin kwarewar fasaha da ake bukata a ma’aikatu da dama, yana jaddada muhimmancin koyar da sana’o’in zamani da fasaha domin rage matsalar rashin aikin yi.
A biranen Nijeriya yadda matasa ke yawon ragaita a cikin unguwanni da saman tituna daga nan zuwa can suna maular kudi ko abin da za su ci ya riga ya zama ruwan dare wanda ba kawai alamar talauci ba ce, alama ce ta matsanancin rashin aikin yi da ke kara ta’azzara a tsakanin matasa.
Nijeriya na da dimbin matasa masu ilimi da sanin ya kamata amma rashin aikin yi ya hana da yawa daga cikinsu samun damar dogaro da kai ta yadda za su iya rike kan su, iyayensu da na kasa da su.
A yanayin rashin aikin yi matasa da dama na tsunduma a sabgar maula ba wai domin sun zaba ba sai don ba su da wani zabi don haka ya zama tamkar tilas a gare su lamarin da ke zubar da kima da darajar su a cikin al’umma.
Rashin abinci, rashin kudin sufuri da na kananan bukatu a bisa ga rashin aikin yi kan tilasta matasa da dama neman taimako daga jama’a a wannan layin da wancan lungun wanda hakan ya kara nuna yadda matsalar aiki ke sauya rayuwar matasa daga kyakkyawan fata zuwa fadi tashin rayuwa.
Sai dai wannan bahaguwar matsalar ba ta tsaya ga maula ko roko kawai ba domin a yayin da matasa ke fama da kuncin rayuwa, wasu ‘yan siyasa na amfani da wannan damar wajen jawo su a cikin sha’anin bangar siyasa ta hanyar amfani da su wajen tayar da tarzoma, haddasa rikita-rikitar siyasa ko tsoratar da abokan hamayya a yayin yekuwar neman zabe ko lokacin zabe.
Masana ilimin zamantakewa sun bayyana cewa maular da matasa ke yi ba matsala ce ta dabi’a ba kawai, babbar illa ce da ta wanzu a dalilin rashin damar samun aiki, karancin horon sana’oi da rashin samun tallafi wadanda suna daga cikin manyan dalilan da ke jefa matasa su a cikin maula.
Baya ga wannan a Nijeriya daya daga cikin manyan matsalolin da suka yi tarnaki da zama kafar ungulu ga wanzuwar ingantaccen tsarin mulkin dimokuradiyya shi ne bangar siyasa a bisa ga yadda ‘yan siyasa ke amfani da matasa domin tsoratarwa da barazana ga abokan hamayya.
Bangar siyasa matsala ce mai zaman kan ta da ke addabar matasa a Nijeriya tare da kassara rayuwar su a bisa ga yadda suke kasa amfanar kan su ballantana su amfani wasu wanda hakan na nufin bangar siyasa babbar barazana ce ga zaman lafiya da mulkin dimokuradiyya.
Ba ciri ba coge wannan dabi’ar na jefa matasa cikin dabi’ar shaye-shaye, rashin ilimi da amfani da miyagun makamai a yayin da ‘yan siyasa suka kebe nasu ‘ya’yan ga shiga duk wata sabgar bangar siyasa da kwamacalar siyasa.
A bayyane yake yadda ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa ke taka muhimmiyar rawa wajen gurbata tarbiyar matasa a Nijeriya ta hanyar saka su a cikin bangar siyasa, kazamar hanyar da suke amfani da ita wajen kai farmaki ga abokan adawa, a wasu lokutan har da wadanda suke da matsalar rikicin cikin gida.
Hasalima a bayyane yake cewar yadda ake amfani da matasa a bangar siyasa tuni ya zama abin damuwa a kasar nan lamarin da kullum gaba-gaba yake kara yi ba tare da ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa sun takawa lamarin burki ba saboda su ke amfana da matasan wajen cin karen su ba babbaka.
A lokutan zabe manya da matsakaitan jam’iyyun siyasa kan yi amfani da matasa a dalilin zaman banzan da suke yi suna ba su kudade kalilan domin su aikata ayyukan tashanci ta hanyar afkawa abokan hamayya a jam’iyyu daban-daban lamarin da babban laifi ne a dokar kasa da kundin dokar zabe.
Masu fashin bakin lamurran yau da kullum sun yi ta nanata cewar idan ba a magance matsalar rashin aikin yi ba, gagarumar matsalar za ta ci- gaba da kara ta’azzarar bangar siyasa, yawon maula da karuwar talauci a tsakanin matasa.
A kan wannan a na ganin samar da ayyukan yi, inganta ilimin fasaha da tallafawa matasa da jari na daga cikin matakan da za su rage yawan maula ko roko a tituna. Haka masu ra’ayin na ganin ya zama wajibi gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu su hada kai wajen assasa ayyukan da matasa za su samu aikin yi domin inganta rayuwarsu.
Wakilinmu ya labarto cewar masani harkokin tsaro a Nijeriya, Abdullahi Bakoji Adamu, ya ba da shawarar a dauki tsauraran matakan hukunta ‘yan siyasar da ke daukar nauyi ko goyon bayan rikicin siyasa gabanin zaben 2027.
Bakoji ya bayyana cewa karuwar matsalar bangar siyasa a Jihar Kano da sauran sassan Arewacin Nijeriya ya zama dole a dauke ta a matsayin babbar barazanar tsaro, ba wai kawai tashin hankalin da ke addabar matasa ba.
Masanin ya yi gargadin cewa irin wadannan ayyuka na barazana mai tsanani ga dimokiradiyya da kuma zaman lafiyar kasa kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da manema labarai a wannan makon yana cewar bangar siyasa babbar barazana ce ga tabbatar da mulkin dimokiradiyya da kuma zaman lafiya a tsakanin al’umma.
“Dole ne a hukunta ‘yan siyasa da ke daukar nauyin bangar siyasa. Wannan ya shafi gwamnoni, ‘yan majalisar dattawa da na wakilai da na jihohi da duk masu neman zababbun kujeru.” In ji Bakoji.
LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewar a yayin da Nijeriya ke shirin fuskantar zaben 2027, an fara ganin alamun tashin hankali a wasu wurare da suka shafi bangar siyasa ta yadda a irin wannan lokaci, galibi matasa ne ke amfani da su wajen aiwatar da ayyukan da ke haifar da tashin- tashina da ke iya jefa su a cikin matsala.
A kan wannan masu fashin bakin lamurran yau da kullum na bayyana cewar ya zama wajibi matasa su yi wa kan su karatun- ta natsu su guji shiga harkokin bangar siyasa da duk wani nau’in tashin hankali ko rikici, domin ba abin da take haifarwa face da-na-sani.
Bangar siyasa a kodayaushe kan gurbata rayuwar matasa tare da jefa su a cikin hadarin kamawa, rauni ko ma rasa rayuwa domin a dalilin hakan dubban matasa sun halaka. Hasalima sau da yawa, ‘yan siyasar da ke amfani da matasa a irin wannan yanayi ba su damu da makomar su ba, burinsu kawai shi ne cimma muradun siyasar su na dankanen lokaci.
Idan aka magance tushen matsalar, wato rashin aikin yi, za a iya rage yawan roko da kuma hana amfani da matasa a harkokin bangar siyasa wanda hakan zai taimaka wajen gina kasa mai cike da aman lafiya da ci gaba.















Discussion about this post