ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyamar Baki: Majalisa Ta Bukaci Tinubu Ya Janye Lasisin Kamfanonin Afrika Ta Kudu

by Sulaiman and Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago
majalisar kasa

Sanata mai wakiltar Edo North, Adams Oshiomhole, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakan tattalin arziki masu tsauri kan kamfanonin Afirka ta Kudu da ke aiki a Nijeriya, sakamakon sabbin hare-haren kiyayya (denophobia) da ake kai wa ‘yan Nijeriya a South Africa.

Yayin da yake gabatar da batun a zaman majalisar dattawa a ranar Talata, Oshiomhole ya bukaci a wuce matakin korafi na diflomasiyya kawai, a rungumi manufar mayar da martani daidai da abin da aka yi (reciprocity).

Ya ba da shawarar musamman a janye lasisin MTN Nigeria, yana mai cewa ‘yan kasuwar Nijeriya za su iya cike gibin da hakan zai haifar.

ADVERTISEMENT

“Ba na son wannan Majalisa ta rika zubar da hawaye… Idan ka buge ni, zan buge ka. Wannan gwagwarmaya ce ta tattalin arziki,” in ji shi, yana mai cewa irin wannan mataki mai karfi zai tilasta hukumomin Afirka ta Kudu su dauki tsaron ‘yan Nijeriya da muhimmanci.

Oshiomhole ya jaddada cewa ‘yan Nijeriya da ke Afirka ta Kudu masu bayar da gudunmawa ne ga tattalin arziki, ba masu dogaro da wasu ba ne. Ya yi gargadin cewa ci gaba da jure irin wadannan hare-hare na aika sako mara kyau tare da raunana ikon Nijeriya na kare ‘yan kasarta da muradunta.

LABARAI MASU NASABA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

A cikin kuduri mai maki shida, Majalisar Dattawa ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta fara tattaunawa a matakin koli da South Africa da kuma Ghana domin kare ‘yan Nijeriya a kasashen waje tare da samar da tabbacin da za a iya aiwatarwa don hana aukuwar irin hare-haren a gaba.

Majalisar ta kuma nemi a gudanar da cikakken bincike na gaskiya da zaman kansa kan dukkan hare-haren da aka ruwaito, tana mai jaddada cewa dole ne a gano masu laifi da masu daukar nauyinsu, a kama su, a gurfanar da su a gaban kuliya, sannan a hukunta su bisa doka.

A wani bangare kuma, Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta sake duba dukkan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da Afirka ta Kudu, tare da dakatar da bayar da izinin kasuwanci ga sababbin kamfanonin Afirka ta Kudu da ke son aiki a Nijeriya, sakamakon sabbin hare-haren kiyayya ga ‘yan Nijeriya.

An amince da wannan kuduri ne a zaman majalisar na ranar Talata bayan wani kudiri da Donald Ojogo ya gabatar.

‘Yan majalisar sun nuna damuwa kan tsaron ‘yan Nijeriya a Afirka ta Kudu, tare da kira da a dauki matakai masu karfi don kare ‘yan kasa da muradun kasa.

A matsayin wani bangare na kudurin, Majalisar ta bai wa kwamitocinta na harkokin kasashen waje da ‘yan kasa mazauna kasashen waje, da kuma na hadin gwiwa a Afirka, umarni su yi hulda da ofishin jakadancin Nijeriya da ke Pretoria.

Kwamitocin za su taimaka wajen kafa cibiyar ba da agajin gaggawa ta awa 24 da kuma asusun taimakon shari’a domin tallafa wa ‘yan Nijeriya da ke fuskantar matsaloli a Afirka ta Kudu.

Majalisa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • Sulaiman
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace
Majalisa
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
Labarai

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana
Labarai

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Next Post
An Bude Taron Karawa Juna Sani Kan Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Na 2026

An Bude Taron Karawa Juna Sani Kan Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Na 2026

LABARAI MASU NASABA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.