ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Laifin ‘Yan Arewa Ne Kan Yadda Muka Bari Matsalar Tsaro Ta Addabe Mu — Sule Lamido

by Sadiq
4 months ago

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya ce mutanen Arewacin Nijeriya su daina ganin laifin wani a waje, domin su kansu ne suka taka rawa wajen taɓarɓarewar tsaro a yankin.

Lamido ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Premier Radio da ke Kano a ranar Laraba.

Ya ce matsalar tsaro da ake fama da ita tana da alaƙa da rashin shugabanci na gari da kuma lalacewar tarbiyya a cikin al’umma.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, yawancin shugabannin siyasa sun yi watsi da aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, sun mayar da hankali kan siyasa maimakon shugabanci na gari.

Ya ce dole ne ‘yan Arewa su tashi tsaye su dawo da tarbiyya da ladabi ga matasa domin a magance matsalar tsaro.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Lamido ya kuma zargi wasu ‘yan siyasa da cewa suna amfani da matasa ta hanyar da ke lalata rayuwarsu, abin da ke ƙara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankin.

Ya ce waɗanda ke aikata laifuka kamar Boko Haram da fashi da makami ba baƙi ba ne, ‘yan yankin ne da suka taso a cikin al’umma.

A cewarsa, “’Ya’yanmu ne,” yana mai cewa matsalar ta samo asali ne daga lalacewar tarbiyya, wanda ya ce ita ya kamata a fara gyarawa tun daga gida.

Tsohon gwamnan ya kuma goyi bayan kafa ‘yansandan jihohi, amma ya ce dole ne a ba su horo mai kyau kafin fara aiki.

Ya ce abin takaici ne ganin yadda wasu daga cikin mutanen yankin ke sace juna ko aikata laifi ga ‘yan uwansu domin neman kuɗin fansa, yana mai cewa shugabanni sun fi mayar da hankali kan siyasa maimakon warware matsalolin jama’a.

A ƙarshe, Lamido ya ce adalci, gaskiya da tarbiyya su ne mafita wajen dawo da zaman lafiya a Arewacin Nijeriya.

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Tinubu Ya Naɗa Mai Shekaru 39 A Matsayin Sabon Shugaban JAMB

Tinubu Ya Naɗa Mai Shekaru 39 A Matsayin Sabon Shugaban JAMB

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.