ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Larabawan Da Suka Dauki Kasadar Ceton Yahudawa Lokacin Kisan Kiyashi

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
4 months ago
Yahudawa

An karrama mutum 28,000 wadanda ba Yahudawa ba saboda daukar kasada na ceto rayukan Yahudawa lokacin kisan kiyashi na Holocaust – sai dai duk da cewa an kashe dubban mutane lokacin da ‘yan Nazi suka mamaye Arewacin Afirka, babu Balarabe daya da aka taba karramawa saboda ceto ran Bayahude a kasar Larabawa.

“Wani Balarabe mai sana’ar gasa biredi a Tunisiya ya kasance yana barin karin biredi a shagonsa a kowace rana domin bai wa Yahudawan da ba su da karfi.”

“Matan Larabawa na daukar ‘ya’yan Yahudawa zuwa gidajensu domin kula da su – saboda babu abinci ko kuma madara.”

ADVERTISEMENT

“A Algiers, an hana Musulmai daukar kayan Yahudawa da aka kwace kuma babu Balaraben da ya tsallake wannan umarni.”

Wadannan na cikin labaran da Dakta Rob Satloff, babban daraktan wata cibiya a Washington ya tattara, na yadda ‘yan Arewacin Afirka ke taimakon Yahudawa lokacin yakin duniya na biyu.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

‘Yan Nazi sun kashe sama da Yahudawa miliyan shida a Turai, sai dai sun kuma gallazawa al’ummomin Yahudawa da ke arewacin Afirka, wanda ya samu goyon baya daga shugabancin Bichy, abin da ya janyo kashe-kashe, daidaitawa da kuma lalata kayakin Yahudawa da dama.

“Duk abin da ya faru da Yahudawa a Turai ya faru da Yahudawa a kasashen Larabawa,” kamar yadda Satloff ya shaida wa BBC.

A cewar cibiyar tunawa da kisan kiyashin Yahudawa da ke Amurka, kusan Yahudawa rabin miliyan ne ke rayuwa a kasashen Moroko, Aljeriya, Tunisiya da kuma Libya. Kuma Satloff ya yi kiyasin cewa wadanda aka kashe zai iya kai wa tsakanin 4,000 zuwa 5,000.

 

Daukar babbar kasada

Akwai wasu Larabawa uku da suka cancanci lambar yabo a wajen tunawa da kisan kiyashin Yahudawa, a cewar Yad Bashem.

A Tunisiya, kasar da ‘yan Nazi suka mamaye baki daya a arewacin Afirka – daga Nuwambar 1942 zuwa Mayun 1943 – an tilasta wa Yahudawa saka abubuwa da ke taurari masu alamar ruwan dorawa.

Sai dai lokacin ‘yan Nazi suka bukaci dukkan Yahudawa su fito don tilasta musu aiki, daya daga cikinsu mai suna Joseph Naccache ya tsere.

Gomman shekaru bayan nan, ya fada wa Satloff a Paris yadda wani Balarabe ya dauki kasadar ba shi mafaka.

“Sojojin Nazi sun yi ta yada labarai kan matasan Yahudawa, a watan Disambar 1942,” a cewar Satloff. ”

Idan aka kama wani yana bai wa mutumin da sojojin ke nema, wannan babban laifi ne.

“Naccache ya tsere daga neman da ake yi masa, inda yake kokarin ganin ‘yan Jamus din ba su tafi da shi ba, inda ya kare da komawa wani gidan wanka.”

Mai gidan wankar, Hamza Abdul Jalil, ya fada wa Naccache cewa zai kare shi ta hanyar boye shi a wurinsa.

“Ba wanda aka tseratar kadai na samu gani ba, na samu damar komawa Tunis kuma na samu gidan wankar da kuma dan mutumin da ya ceci Naccache,” kamar yadda Satloff ya fada wa BBC. “Yana da dukkan bayanai. Labari ne mara dadi kuma na same shi daga dukkan bangarori.”

Tsohon magajin garin Tunis, Si Ali Sakkat, shi ma ya dauki kasada domin samar da abinci da kuma mafaka ga Yahudawan da suka tserewa azabtarwa, a garin mahaifarsa da ke tsaunin Zaghouan, mai nisan kilomita 55 daga babban birnin kasar.

 

‘Yin fito na fito da barazana’

Sai dai, daya daga cikin labaran Satloff shi ne Khaled Abdul-Wahab, wanda ya jiyo wani sojan Nazi na cewa ya mayar da hankalinsa kan wata Bayahudiya a Tunisiya.

Da tsakiyar dare, Abdul-Wahab ya tseratar da matar da iyalanta, wadanda ke cikin buya, ya dauke su zuwa gonarsa mai nisan kilomita 30 daga Tunis, inda ya boye su.

Sai dai wannan shi ne mafarin kafin mamayar Nazi ta kawo karshe, ya boye mata 20 da kuma yara, bayan da aka tilasta wa mazajensu zuwa aikin dole.

Uku daga cikin matan sun bukaci cibiyar Yad Bashem da ta karrama Abdul-Wahab – sai dai an yi watsi da bukatar har sau biyu.

Mutumin “kirki” ne, a cewar cibiyar, kuma labarin da aka bayar na abin da ya yi ya nuna dattaku, sai dai bai wa Yahudawa mafaka yana bisa ka’ida kuma sun zauna cikin gonar Abdul-Wahaba tare da sanin ‘yan Nazi ba, abin da ya sa bai cancanci karramawar ba da ake bai wa mutanen da suka sayar da ransu wajen ceto Yahudawa daga kashe-kashen ‘yan Nazi lokacin kisan kiyashi.

“Saboda mamayar Nazi a Tunisiya ta dauki akalla watanni shida, hakan bai kai ga dabbaka tsarin son kawo karshen Yahudawa ba,” in ji cibiyar Yad Bashem.

A watan Dismabar 2011, Eba Weisel, wadda Abdul-Wahab ya bai wa mafaka tana shekara 13, ta rubuta wani littafi a jaridar New York Times, inda ta nuna fushinta kan kin karrama shi.

“Na san cewa ina iya rayuwa saboda Abdul-Wahab ya yi fito na fito da marasa imani wajen ceto rayuwata, kamar yadda ya tseratar da sauran iyalaina,” in ji ta. “Ina fatan cibiyar Yad Bashem za ta sake duba batun kafin a ce babu wanda ya rage da zai bayar da labari.”

 

‘Labaran da suka fi dacewa’

Cikin sama da mutum 28,000 da aka bai wa lambar girmamawa saboda tseratar da Yahudawa lokacin kisan kiyashi, mutum 70 cikinsu sun kasance Musulmai amma daya ne Balarabe, wani likita a kasar Masar Mohamed Helmy, wanda ya boye wata Bayahudiya da kuma taimakawa iyalanta a Berlin.

Yayin da labaran Satloff suka kasance masu karfi, Dakta Mehnaz Afridi, darakta a Jami’ar Manhattan a Amurka, ya ce suna duba labaran da suka fi dacewa.

Afridi ta fada wa BBC cewa: “Ga wasu da ke Isra’ila, karramawa Larabawa da suka ceci Yahudawa yana da tsarkakiya a siyasance.

Ga wasu kuma a kasashen Larabawa, bayyana cewa Yahudawa na son ceto daga ‘yan Nazi a kasashen Larabawa yana saka shakku kan kisan kiyashin.”

 

‘Gabatowar kisan kiyashi’

Afridi ita da kanta tana kira don ganin an karrama sarkin Moroko.

“Lokacin gwamnatin Bichy na ‘yan Nazi, an umarci Moroko da ‘yan birnin Tangiers cewa su tursasa Yahudawa fita zuwa sansanin tara masu aikin tilas.

Sarkin Moroko, Mohammed B, ya yi watsi da bukatar aiwatar da dokokin haramta wariya ga Yahudawa ko kuma tura Yahudawan Moroko zuwa Faransa,” in ji ta.

A shafin intanet na cibiyar Yad Bashem, Jackie Metzger, daga makarantar nazarin kisan kiyashin Yahudawa, wadda ta dade da yin ritaya, ta rubuta cewa: “Idan kisan kiyashi na nufin daruruwan kashe-kashe, to hakan bai faru a arewacin Afirka ba.

Ya kamata tarihin Yahudawa a wannan lokaci ya yi maganar cewa an kusa afkawa cikin kisan kiyashi, amma ba a kai ga haka ba.

Sai dai a wani martani da cibiyar ta mayar, ta ce “Arewacin Afirka na cikin bangaren kisan kiyashi na Yahudawa.”

“‘Yan Nazi sun yi niyyar aikata wa Yahudawan Afirka da na Falasdinawa da kuma Gabas Ta Tsakiya abin da suka yi a Turai,” a cewar cibiyar.

Bayanan hoto,Cibiyar Yad Bashem ta karrama sama da mutum 28,000 wadanda suka ceci Yahudawa

Ana yin muhawara sosai kan kowane irin labari da ake son karramawa, ba tare da nuna bambanci ba, in ji cibiyar, sai dai kwamitin tantancewa na cibiyar ba ya duba “batun karrama Yahudawa da suka yi ceto ba” saboda babu bukatar hakan daga wani wuri yanzu.

Labarai irin na Abdul-Wahab na ci gaba da samun karbuwa, in ji Afridi. “A 2009 an shuka wata cibiya don karrama shi a Wahington da kuma birnin Milan, inda aka yi wnai biki a gaban ‘yarsa, Faiza,” a cewar Afridi.

Satloff ya ce: “Ina alfaharin cewa kungiyoyi da kuma hukumomi da dama a arewacin Afirka da kuma Turai na karrama jajircewa da kuma namijin kokarin wadannan Larabawa da suka tashi tsaye don kare Yahudawa a wancan lokaci,” in ji shi.

Kuma ganin cewa hujjoji na kara fitowa, Satloff na fatan cewa akwai karin damarmaki na girmama wadannan mutane a nan gaba.

Yahudawa
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    NSCDC Ta Cafke Mutum 10 Da Ake Zargi Da Satar Kayan Gwamnati Da Kuma Fashi A Kano
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƴansanda Su Ƙi Karɓar Cin Hancin Naira Miliyan 500 Daga Hannun Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙasashen DR Congo Uganda Da Sudan Sun Haɗa Kai Domin Yaƙar Ibola
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Zafin Rana Ya Yi Ajalin Mutum 16 A Indiya
Yahudawa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada
  • Sulaiman
    Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa
  • Sulaiman
    Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
  • Sulaiman
    Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa
Labarai

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
Manyan Labarai

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Next Post
Fiye Da Yara Miliyan 2 Ne Ke Gararamba Da Bacci A Wuri Mai Ƙazanta A Kano – GIOPPINI

Fiye Da Yara Miliyan 2 Ne Ke Gararamba Da Bacci A Wuri Mai Ƙazanta A Kano - GIOPPINI

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.