ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fiye Da Yara Miliyan 2 Ne Ke Gararamba Da Bacci A Wuri Mai Ƙazanta A Kano – GIOPPINI

by Abubakar Sulaiman
7 months ago
Kano

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Wata ƙungiya mai zaman kanta, Global Improvement of Less Privileged Persons Initiative (GIOPPINI), ta ce sama da yara miliyan biyu ne ke kwana a muhalli mara tsaro da rashin tsafta a Kano a kullum. Daraktan zartarwa na ƙungiyar, Mohammed Ali Mashi, ya ce binciken da suka gudanar ne ya fitar da wannan ƙididdiga, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin tayar da hankali.

A cewarsa, an gano yaran na zaune a wurare daban-daban a cikin birnin Kano, ciki har da filin sukuwa, da Central Hotel, da tashar jirgin ƙasa, da titin asibitin Nassarawa, da gadar Dangi, da Zoo Road, da gadar Lado, da Sabon Gari, da tashar Mariri da Kofar Ruwa. Ya ce da dama daga cikinsu sun fito ne daga jihohi maƙwabta ko karkara da sunan neman ilimin Alƙur’ani, amma yunwa da rashin kulawa suka sa suka bar makaranta suna rayuwar titi.

  • Tinubu Ya Tura Kashim Shettima Kano, Ya Yi Alƙawarin Tallafin Kuɗi Ga Ƴan Kasuwar Singa
  • Tinubu, Shettima Zasu Ziyarci Kano Halartar Tarɓar Gwamna Yusuf Zuwa APC

Mashi ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, matsalar na iya rikiɗewa zuwa barazana ga tsaro da zaman lafiyar jihar, domin rayuwar titi na jefa yara cikin aikata laifi da cin zarafi. Ya ce lamarin ba na jin ƙai kaɗai ba ne, illa ma barazana ce ga zaman lafiya.

ADVERTISEMENT

Ya buƙaci gwamnati, shugabannin al’umma da na addini da ƙungiyoyin farar hula su haɗa kai wajen samar da shirye-shiryen gyara da mayar da yaran cikin al’umma ta hanyar samar musu da mafaka, da abinci, da lafiya da ilimi. Haka kuma ya jaddada buƙatar tsare-tsaren gwamnati da za su daidaita zirga-zirgar yara tsakanin jihohi da kuma tabbatar da kulawa ga iyalai masu rauni domin daƙile ci gaba da faɗaɗar talauci da sakaci.

Kano
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Next Post
Ƴan Bindiga Sun Sace Ƴan Uwan Limamin Izala A Bauchi

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.