ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Lokaci Ya Yi Da Matasan Nijeriya Za Su Ƙwato Ƙasarsu — Kwamred Yahaya Abdullahi

by Bello Hamza
2 months ago

A wata tattaunawa ta musamman da Editanmu Bello Hamza ta yi da Shugaban Matasan Jam’iyyar African Action Congress (AAC) na ƙasa, Kwamret Yahaya M. Abdullahi, ya bayyana cewa lokaci ya yi da matasan Nijeriya za su farka domin kwato makomar ƙasarsu ta hanyar shiga siyasa da kuma zaɓen shugabanni masu gaskiya da kishin talaka waɗanda ke da riƙon amana.

Kwamaret Yahaya ya ce jam’iyyar AAC ita ce jam’iyya ɗaya tilo mafi tsayawa kan gaskiya, adalci, da yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya, yana mai cewa dubban matasa daga sassa daban-daban na ƙasar nan na ci gaba da shiga jam’iyyar saboda sun gaji da tsohuwar siyasar yaudara da rashin adalci da tsoffin yan siyasar ƙasar suka shafe tsawon shekaru suna gudanarwa, rayuwar talaka kullum yana cikin ƙunci, tashin hankali, damuwa da sauransu kuma ba wanda ya isa ya fito ya yi magana.

“Ina miƙa gaisuwa ta musamman ga dukkan matasan Nijeriya da masu kishin ƙasa. Yau Nijeriya na cikin mawuyacin hali saboda tsawon shekaru na gazawar shugabanci, rashin adalci, rashin aikin yi, da kuma danniyar talakawa. Amma muna da yakinin cewa matasa za su iya sauya wannan tarihi idan suka haɗu suka tsaya tsayin daka wajen kare ƴancinsu, tare da faɗa da dukkan wani tsari na zalunci.”

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa yayin ziyarce-ziyarcen da yake kaiwa jihohi daban-daban, ya gana da matasa, masu fafutuka, da shugabannin al’umma da dama da suke nuna sha’awar tsayawa takara a ƙarƙashin tutar jam’iyyar AAC.

“Abin farin ciki ne ganin yadda matasa ke ƙara fahimtar cewa siyasa ba mallakin attajirai ko masu mulki kaɗai ba ce. Nijeriya tamu ce baki ɗaya, kuma lokaci ya yi da matasa za su shiga gaba wajen ƙwato makomar ƙasarsu,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Ya ce: “Ina kira ga duk wani matashi ko ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa da yake da burin kawo sauyi kada ya ji tsoro ko ya yi ƙasa a gwiwa. Ku zama ɗan gwagwarmayar kwato yancin Jama’a, ya shiga jam’iyyarmu ta AAC domin yaƙi da dukkan wani mummunan mulki a faɗin Nijeriya.

Kwamret Yahaya ya kuma buƙaci matasan Nijeriya su mara wa jagoran jam’iyyar AAC baya, wato Omoyele Sowore, yana mai cewa Sowore ya shafe shekaru yana gwagwarmayar kare haƙoƙin talakawa da yaƙi da zalunci ba tare da tsoro ba.

A cewarsa: “Matasan Nijeriya dole su fahimci cewa idan suna son ƴanci na gaskiya, shugabanci nagari, da ƙasar da za ta ba su dama, dole su fito su yi faɗa ta hanyar dimokuradiyya. Omoyele Sowore ya nuna jarumta da sadaukarwa wajen yaƙi da cin hanci, rashin adalci, da danniyar gwamnati. Lokaci ya yi da matasa za su haɗa kai su zaɓi shugabanni masu gaskiya maimakon waɗanda suka jefa ƙasar nan cikin matsala.”

Ya ƙara da cewa AAC ba jam’iyyar siyasa ce ta anfani kawai ba, illa wata tafiya ce ta neman ƴanci da adalci ga talakawan Nijeriya.

“Sai mun haɗu tare ne za mu iya gina Nijeriya mai adalci, inda matasa za su samu aiki, talaka zai samu kariya, kuma gwamnati za ta yi aiki domin jama’a ba domin masu ƙarfi ba,” in ji shi.

Babban abin da ya fi tayar da hankalinmu a Arewacin Nijeriya yanzu shi ne matsalar tsaro, wannan abu ne da ya addabi jama’ar Nijeriya, musamman Arewacin Nijeriya, a kwanakin baya Sowore ya yi wata magana inda yake cewa a cikin mako biyu zai magance matsalar tsaro idan ya zama shugaban ƙasa, inda ya bayyana cewa masu kawo matsalar tsaro suna Abuja, su za’a magance idan aka magance su to an kammala da matsalar tsaro, amma matukar suna yawo to lallai matsalar zai ci gaba da hauhawa a faɗin Nijeriya.”

“Babban Burinmu a yau shine mu tabbatar da mun magance dukkan wani damuwa da zai addabi talaka a faɗin Nijeriya, abu na farko shine matsalar tsaro, Arewacin Nijeriya da noma kawai zamu iya rike kanmu, Ƙasar ‘Ukraine’ bata wuce jihohi uku a faɗin Nijeriya ba amma abun kunya har lokacin da take yaƙi sai da ta bama Nijeriya tallafin abinci wannan babbar abun kunya ne, a ƙasar da muke da komai na arziki tun daga filin noma har arziƙin ƙarƙashin ƙasa duk Allah ya bamu amma saboda shugabannin Nijeriya damuwarsu kawai su azurta kansu, kullum muna cikin fama da talauci.

Haka idan muka koma ɓangaren tattalin arzikin ƙasa, muna da masu Ilimin da za su cire wa Nijeriya kitse a cikin wuta, a kullum abin da Omoyele Sowore yake cewa shi ne zalunci ne ya dabaibaye Nijeriya ba rashin abin da ya kamata ba, muna da waɗanda za su yi ayyuka a ƙasar nan tuƙuru domin ci gaban ƙasar, amma abin kunya har yanzu mafi ƙarancin albashi a Nijeriya bai wuce dubu ɗari ba, wasu ƙasashen da ba’a aiki kamar Nijeriya albashin ya zarce na Nijeriya kusan kashi uku, kullum ma’aikata ke wahala a Nijeriya.

Ya yi wa dukkan masu neman takara da magoya bayan jam’iyyar fatan alheri tare da jaddada cewa gwagwarmayar ceto Nijeriya tana buƙatar haɗin kan matasa daga kowane ɓangare na ƙasa.

Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kafa Cibiyar NIPHID: NCDC Ta Yi Kuskuren Fahimtar Ƙudirin Dokar
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ƙungiyar Kansilolin APC Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Idan Ba A Daina Zargin Sanata Yari Ba

MASU ALAKA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC
Manyan Labarai

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa
Siyasa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026
Next Post
CMG Ta Tsara Tare Da Watsa Shiri Mai Dogon Zango Na “Sadaukarwa”

CMG Ta Tsara Tare Da Watsa Shiri Mai Dogon Zango Na “Sadaukarwa”

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

July 15, 2026
Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.