ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Lokacin Da Duniya Ke Kira Ga Zaman Lafiya, Japan Ta Zabi “Sake Daukar Makamai”!

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Japan

An bude taron share fage na dandalin tsaro na Xiangshan na shekara ta 2026 a birnin Beijing na kasar Sin jiya Juma’a. Wakilai sama da 120 daga kasashe fiye da 40, da kungiyoyin kasa da kasa sun hallarta tare da gudanar da tattaunawa kan jigon “Tsarin shugabancin tsaro na duniya: kalubale da mafita”. A wani bangare kuwa, Japan ta fara harba makamai masu kai hari ketare a karon farko, a atisayen hadin gwiwa na Amurka da Philippines na “kafada da kafada” a ranar 6 ga watan Mayu. Matakan sun nuna nau’ika biyu mabanbanta na yanayin tsaron duniya.

Duniya a yau ba ta cikin kwanciyar hankali. Yake-yake na ci gaba da dabaibayi Yankin Gabas ta Tsakiya, rikicin Ukraine ya dade yana wakana, kana wasu manyan kasashe suna daukar ra’ayin bangaranci, yayin da ikon Majalisar Dinkin Duniya ke fuskantar yiwuwar durkushewa. A daidai lokacin da dandalin tsaro na Xiangshan ke kokarin nazarin “mafitar zaman lafiya da tsaron duniya”, ’yan siyasa masu tsattsauran ra’ayi na Japan na kara hanzarta “sake daukar makamai don farfado da ra’ayin fin karfi”. A watan Afirilun bana sun sassauta dokar dake yi wa kasar tarnakin fitar da makamai masu kisa a hukumance. A ranar 6 ga watan Mayu kuma sun fara harba makamai masu kai hari a Philippines a karon farko a ketare. Kazalika, a ranar 8 ga watan Mayu, firaministan kasar Takaichi Sanae, ta bayyana a fili cewa shirinta na ziyartar Amurka yana da nufin “kara karfafa karfin takara”. A lokaci guda kuma, ‘yan majalisa 126 na Japan sun ziyarci haikalin Yasukuni, wato wurin tunawa da wadanda suka aikata lafin yaki. Kuma Japan tana ci gaba da hanzarta gyaran kundin tsarin mulkinta. Ba shakka daga fadada sojoji da gyaran kundin tsarin mulki zuwa ziyartar haikalin Yasukumi, Japan tana zama daya daga cikin manyan masu kawo rudani da rashin tabbaci a tsarin tsaron yankin Asiya da tekun Pasifik.

Sabanin manufar “tsaro ta ra’ayin bangaranci” na Japan, bana ake cika shekaru 20 da kafuwar dandalin tsaro na Xiangshan, wanda ya kasance yana bin manufar “tattaunawa cikin daidaito, da hadin gwiwa da koyi da juna”. A wannan taro, ana mayar da hankali kan batutuwa kamar “tsarin kasa da kasa da bin doka”, da “sabon kalubalen tsaro a yankin Asiya da tekun Pasifik”, kana da “Alhakin kiyaye tsaron duniya na hadin gwiwa” da sauransu.

ADVERTISEMENT

Shugabar ofishin dandalin Li Shuyin ta nuna cewa, dandalin ya mai da hankali kan tsarin shugabancin tsaro na duniya, domin inganta aiwatar da shawarar shugaban kasar Sin Xi Jinping ta kyautata shugabancin duniya, da kuma magance matsalar gibin zaman lafiya, da gibin tsaro da gibin shugabanci.

A gefe guda, Japan tana harba makamai a ketare, tare da keta kundin tsarin mulkin zaman lafiya na bayan yakin duniya na biyu.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A gefe guda kuma, wakilai sama da 120 daga kasashe daban-daban suna tattaunawa, da gudanar da shawarwari a birnin Beijing domin neman hanyoyin zaman lafiya.

Hanyoyi biyu, makoma biyu ne. Kamar yadda Li Shuyin ta fada, muna bukatar “Mu bar kowace kasa ta tattauna tare duba da yanayin da ake ciki, ta yadda za a inganta kiyaye tsarin kasa da kasa, da bin dokar kasa da kasa.

“Lokacin da ’yan majalisa masu tsattsauran ra’ayi na Japan ke yunkurin ta da zaune tsaye a Asiya kamar yadda kasar ta taba yi, dandalin ya fitar da sako cewa, ba za a iya inganta tsarin shugabancin duniya ba, har sai an yi tattaunawa bisa daidaito da hadin kai da koyi da juna. (Marubuciya: MINA)

Japan
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Japan
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al’ada

NDLEA Ta Kai Mamaya Jami’ar BUK Ta Cafke Mutum 6 Da Ake Zargi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.