ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Birane 10 Da Suka Fi Daɗin Zama A Duniya A 2026

by Sulaiman and Rabi'u Ali Indabawa
1 month ago
Birane

Wani sabon kundin nazarin yanayin tattalin arzikin duniya na mujallar ‘The Economist’ ya bayyana birane 10 da suka fi daɗin zama a duniya a wannan shekara ta 2026.

Rahoton na shekara-shekara ya yi nazarai kan birane 173 na duniya kafin fitar da rahoton nasa.

Mujallar kan yi nazarain abubuwa a biranen da suka haɗa da kwanciyar hankali da tsarin kiwon lafiya da al’adu da muhallai da ilimi da kuma abubuwan more rayuwa kafin tantance matsaytin da zai bai wa kowane birni.

ADVERTISEMENT

Rahoton ya ƙara fito da yadda ƙasashen Turai ke ci gaba da kankane wuraren da suka fi daɗin zama a duniya, yayin da yankin Australia ke biye.

BBC ta duba rahoton tare da bibiyar mazauna wasu daga cikin biranen domin jin yadda suke gudanar da rayuwa a cikinsu.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Waɗanne birane ne?

1. Copenhagen Babban birnin ƙasar Denmark ne kan gaba a jerin, wadda kuma ta kasance a matsayin shekara biyu a jere. A cewar Mujallar Copenhagen na da kyakkyawan tsarin zaman lafiya da kwanciyar hankali da ingantaccen tsarin ilimi da abubuwan more rayuwa, kuma birnin na cikin mafiya kyawawan al’adu da ɗabi’un mazaunansa.

Ga mazauna birnin, rayuwa a birnin na cike da abubuwan jin daɗi da yalwar lokaci da kuma yin abubuwan nishaɗi haɗe da sauƙin rayuwa.”Za ka iya hawa keke ka je wurin aiki, sannan bayan ka tashi ka je wurin ninƙaya, daga baya kuma ka koma gida domin cin abincin dare. Wannan abu ne na yau da kullum a nan duka a rana guda,” a cewar Laura Amira Ƙassem, wata ɗalibar likitanci kuma mai bincike wadda ta shafe shekara takwas tana zaune a birnin.

Ta ƙara da cewa Ingantattun titunan kekuna da tsaftar ruwan birnin da ya dace da ninƙaya, kuma girman birnin da ya dace da tafiya a ƙafa ko hawa keke ”Wani abu da Laura ta ce ba ta taɓa gani ba.

2. Vienna Duk da cewa a shekarar da ta gabata ne birnin na ƙasar Australia ya ra rasa matsayinsa na ɗaya, amma ingantaccen tsarin kiwon lafiya da iliminsa ya sa shi a matsayi na biyu, cikin birane mafiya daɗin zama a duniya. Ga mazauna Vienna kuwa, rayuwa a birnin ta ta’allaka ne kan sauƙin zirga-zirga, ko ta hanyar ababen hawa ko kuma tafiya a ƙafa, da kuma jin daɗin rayuwar tituna.

Franziska Hochmüller, wadda ke aiki da Hukumar Yawon Buɗe Ido ta Vienna, ta ce:”Ayyukana na yau da kullum sun haɗa da hawa ɗaya daga cikin shahararrun jiragen ƙasan birnin zuwa wurin aiki.” “Maimakon in kasance ina duba wayata, na fi son karanta littafi ko kuma kallon kyawawan gine-ginen da nake wucewa a hanyata.

Wannan na tunatar da ni a kowace rana yadda rayuwa a Ɓienna take da ban mamaki, duk da cewa abubuwan da ke cikinta na yau da kullum ne.”MelbourneBirni na uku mafi daɗin zama a 2026 kamar yadda mujallar ‘The Economists’ ta bayyana shi ne Melbourne.

A matsayinsa na birni na biyu mafi girma a duniya, Melbourne ya kasance ɗaya daga cikin birane masu kyawawan al’adu da tsarin muhalli mai kyau.Ga mazauna birnin, bambancin al’adu na daga cikin abubuwan da ke ɗaukar hankali da sanya nishaɗi, inda kowace unguwa ke da nata salo da kuma irin kamanninta al’adunta.

Anne-Marie Lennon, babbar manajar babban kantin sayar da kayyaki na Crowne Plaza Carlton, wadda ta yi aiki a Birtaniya da Ireland da Australia, ta ce:”Melbourne babban birni nemai yanayin rayuwa irin na ƙaramin gari, inda mutane ke kusantar juna.” “Mutane a nan suna son sanin juna sosai.

Haka kuma akwai al’adu da abinci da kiɗe-kiɗe da kayan kwalliya da fasaha. Kowace unguwa tana da nata yanayi da kuma asalin da ya bambanta ta da sauran unguwanni.”

4. Sydney Wanda shi ne babban birnin ƙasar Australiya ya kasance ya kasance a matsayi na huɗu cikin wannan jeri. Mazauna birnin sun ce birnin na ƙunshe da tarin abubuwa na yanayi, da ɗimbin al’adu, da sauƙin rayuwa.

Steve Kemper, Ministan Ayyuka da yawon buɗe Ido na Jihar New South Wales (NSW), ya ce: “duk inda kake a birnin Sydney ba za ka yi nisa da kyawawan wurare da abubuwan gani ba, kama daga ruwa zuwa kyawawan tsaunukan Blue Mountains ko kuma rairayin bakin teku.”Ya ƙara da cewa haɗuwar al’adu daban-daban da unguwanni iri-iri da abinci masu daɗi da kuma salon rayuwa su ne abubuwan da suka sa Sydney ta zama ta musamman. Birni ne na duniya da ke ɗaukar yanayi na zaman mutane cikin kwanciyar hankali”.

“Sydney kuma birni ne mai yawan jama’a daga mabambantan al’adu da asali. Akwai abinci iri-iri masu kyau da kuma mutane daga sassa daban-daban na duniya, haka kuma a lokaci guda birnin na da yanayin natsuwa kuma ba ya cunkushe da jama’a sosai. Wannan haɗuwa ta siffofi abu ne da ba kasafai ake samu a babban birni ba,” kamar yadda ya yi ƙarin haske.

5. Zurich Birnin Zurich na ƙasar Switzerland ne a matsayi na biyar cikin jerin biranen duniya mafiya daɗin zama a 2026 a cewar mujallar ‘The Economists’.

Mazauna birnin sun ce haɗuwar ingantaccen tsarin rayuwa da kuma sauƙin zuwa wuraren da ke da yanayi na halitta su ne ginshiƙan rayuwa mai inganci da birnin na Zurich.

Manuela Leonard, wadda haifaffiyar Zurich ce, ta ce ” binrin Zurich ya wadata da kyawawan tafkuna da koguna masu ɗaukar hankali”. ”A kowace rana nakan yi tafiya a gefen Tafkin Zurich da Kogin Limmat ko Kogin Sihl, kuma hakan yana ba ni damar samun lokaci na kaina,” in ji Leonard.

“Ruwan kogunan mai tsabta ne, sannan akwai wuraren hutawa fiye 1,200 da aka tanada a sassa daban-daban na birnin,” in ji ta.

Duk da cewa ta shafe rayuwarta gaba ɗaya a Zurich, Leonard ta ce har yanzu tana ci gaba da mamakin yadda birnin yake da tsabta da kuma yadda ake kula da shi sosai.

Sauran biranen 5 da ke kan gaba sune: Geneva, Osaka, Adelaide, Vancouver, da Tokyo.

Birane
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Birane
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Ministan Tsaron Kasar Sin Ya Sha Alwashin Gaggauta Gina Karfin Soji Na Zamani Domin Shirin Tunkarar Abokan Gaba

Ministan Tsaron Kasar Sin Ya Sha Alwashin Gaggauta Gina Karfin Soji Na Zamani Domin Shirin Tunkarar Abokan Gaba

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.