Ƙungiyar Kwankwasiyya ta mayar da martani ga kalaman tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, inda ta ƙi amincewa da ra’ayin cewa tasirin siyasar Rabiu Musa Kwankwaso a Kano yana raguwa.
Martanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara fafatawa kan tikitin takarar shugaban ƙasa na haɗakar jam’iyyun adawa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.
Da yake magana a tashar Trust TV, kakakin ƙungiyar, Hon. Habib Mailemo, ya yi watsi da kalaman Atiku, yana mai cewa Peter Obi da Kwankwaso ne kaɗai ke da abin da ya kira “goyon bayan jama’a na gaskiya” a faɗin ƙasar.
“Peter Obi da ubangidana, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, su ne kaɗai ke da magoya baya na gaskiya waɗanda ba a sayensu da komai. Burinsu ya yi daidai da imani da ƙwarewarsu da kuma tarihin aikinsu, kuma talakawa na son su a zuciya,” in ji shi.















Discussion about this post