ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masana Sun Nemi A Yi Wa Hukumomin Jarrabawa A Nijeriya Kwaskwarima

by Leadership Hausa
6 months ago

Tsarin tafarkin tafiyar da lamarin jarrabawa a Nijeriya yana fama da katsalandan din wasu daga waje da kuma yadda sha’anin siyasa na ‘yan majalisa yake shafar abin kamar dai yadda kwararru suk bayyana

Duk idan ana maganar tafiyar da lamarin ilimi kamar yadda ya dace duk inda ake tunanin aje a dawo dole ne a gane cewa duk abin yana bayan yadda gudanar da harkokin jarrabawa masu nagarta, suke zaman kansu, ba kuma su rika samun sa baki cikin harkokinsu, daga wasu daga waje.

  • Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Ta Farko Game Da Tattalin Arziki Mai Alaka Da Yanayin Duniyarmu
  • An Yi Matukar Inganta Harkokin Sadarwa A Kasar Sin Cikin Shekaru Biyar Da Suka Wuce

A Nijeriya, kasar da ta kasance lamarin jarrabawa shi ne wata kafa da ba karamin tasiri take yi bag a rayuwar matsa masu yawa, irin haka ne yasa nagartar su hukumomin jarrabawar abin nasu ba kawai ya dogara ne kan yadda ake tafiyar da harkokin mulki na wuraren an gano cewa lamarin gaba daya ya shafi kasa ne.

ADVERTISEMENT

Wani zargin da bai dade da bayyana ba kan yadda ‘yan majalisa suke yi katsalandan, da kuma kunatawa,akan abubuwan dashafi harkallar kudi, wadda ita ce ta bude wani abin kace- nace da aka yi kan lamarin shin ko yadda su ‘yan majalisar suke sa ido kan harkoikn ire- iren wadancan hukumomin jarrabawar abin yana neman wuce makadi da rawa ne, har abin yana neman shafar irin damar da tsari mulk ya basu ta kasancewa suma fa suna da ‘yanci na masu zaman kansu?

Shi yasa kwararru suke ta kiraye- kiraye akwai bukatar sumaa sakar masu mara, su kasance suna da cikakken ‘yanci na hukumomi masu zaman kansu, su samu damma ta tafiyar da harkokinsu ba tare da wata gallazawa bad aha wurin wasu.

LABARAI MASU NASABA

Matar Gwamnan Zamfara Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Tsarin Bunƙasa Ilimin Ƴa Mace

Hukumar Ilimin Bai-ɗaya Ta Jihar Yobe Ta Raba Kayan Karatu

Domin su a nasu hasashen tsarin tafaiyar da su hukumomn na jarrabawa yana samun inganci ne kawai matsawar idan babu wata maganar sa ido daga wasu ‘yan siyasa ta hanyar matsa masu,shi yasa suka kara da cewa maganar ingancin sakamakon harkar karatu ta jarrabawa ba zai tafi daidai ba cikin inganci muddin aka ce da akwai masu hana ruwa gudu dangane da hakan.

Kamar yadda suka ce, samar da hanyar kawo gyara a bangaren ilimi yan farawa ne daga samun kariya daga duk wani sharhin da zai shafi siyasa,a kuma tabbatar da kowane lokaci cancance za’a rika mafan da ita a matsayin wani tubali na bukatar kawo ci gaban hakan.

Da yake furta albarkacin bakinsa kan lamarin kwararre kuma masani kan harkar ta ilimi, Collins Moji cewa ya yi ita maganar samun sakamakon jarrabawa wanda babu duk abubuwan da za su sa ayi tir da shi,hakan yana farawa ne daga fara ginin ilimin ne tun farko da amana, su kuma daliban a basu dama ta daukar satifiket / takardar shedar ilimi da daraja.

“Ya ce maganar kare jarrabawa daga katsalandan din siyasa abin ba ya tsaya bane kan lamarin daya shafi harkokin karatu na makaranta ba da suka zama dole; wani abu ne wanda ya dace ayi saboda wadanda za su kasance cikin lamari abin ya amfane su fiye da yadda yake amfanar da wadanda suke a ciki yanzu kamar dai yadda ya jaddada”.

Gamaiyar kunkiyoyi masu zaman kansu sun nuna rashin jin dadinsu akan yada ake rajurawa su hukumomin shrya jarrabawar wajen amsar na goro daga wurinsu.

Kungiyoyin sun yi shi zargin ne akan kallon da ake yiwa Shugaban jwamitin jarrabawa ta bai daya na majalisar Wakilai ta kasa, Honorabul. Oboku Oforji. Zargin idan har ya zama gaskiya, hakan yana bukatar tambayoyin da suke da alaka da lamarin gaskiya, babu wta kunbiya- kunbiya kan lamarin da yake da alaka da kudi, da kuma kowa ya gane da iyakar sa idan ha rana bukatar harkar sa idon ta ‘yan majalisa a aikata abin cikin nagarta.

Hakan ya sa kungiyoyi masu zaman kansu suka yi zargin kallon kamar wata kafa ce ta samun inganci duk da yake idan an ware zargin amsar na goro, ko babu komai su hukumomin shirya jarrabawar an lura da cewa akwai ci gaba kan harkokin nasu.Sun hada da hukumar shiya jarrabawar shigar manyan makarantu (JAMB), Hukumar shirya jarrabawa kasashen yammacin Afirka (WAEC),hukumar shiray jarrabawa ta kasa (NECO) da kuma hukumar shirya jarrabawar da, ta sha shafi harkokin kasuwanci da fasaha (NABTEB)a shekaru da suka gabata.

Su hukumomin kamar dai yadda suka ce,sun kasance cikin lamari na sa ido kwarai da gaske ba domin komai ba sai saboda kawai su inganta ayyukansu su hana magudi, tare da iiyawa da ‘yan kudaden da ake basu duk da haka ma akwai kallon da al’umma suke yi masu.

Komrade Okpanachi Jacob, shi ne mutumin da ya shirya lamarin kungiyar matasa mai da’awa da gaskiya kan lamarin ci gaba, cewa shi zargin ana kallon sane ta bangaren amfani da karfin su ‘yan majalisar a matsayin makamar da tsuke da ita wajen samun gallazawar.

Ya yi maganar da take nuna shi Shugaban kwamitin ana zarginsa da tada hankalin Shugabannin hukumomin jarrabawar, suka rika kaasancewa cikin halin matsi,na lokaci zuwa lokaci, da hakan ya samr da wani yanayi na ban tsoro maimmakon a ce irin ayyukansu ne suka zo yi na duba yadda al’mura suke tafiya. Duba yadda ayyukan suke tafiya, gamaiyar kungiyoyin ai ana bukata ne ta, a bunkasa su hukumomin ta hanyar sanin irin halin da suke cike da kuma yadda suke tafiyar da ayyukansu, amma ba maganar a sa gwiwarsu ta yi sanyi da kada masu hankali wajen bukatar su cika ma wasu bukatunsu na kansu zalla kawai.

Gamaiyar kungiyoyi masu zaman kansu ta bayyana cewar: “Mun yi kira da Shugaban majalisar Wakilai ta kasa, Honorabul. Tajudeen Abbas, cewar ya cire Honorabul. Oboku Oforji kan matsayinsa na Shugaban kwamitin jarrabawa bai daya, inda zai fuskanci binciken da kwamirin da’a na majalisar zai yi ma sa, domin lamarin yana bukatar da ayi bincike na gaggawa saboda muhimmancin sa.

“Idan kuma an ki cire shi daga mukamin da kuma yi masa cikakken bincike hakan zai sa ayi gaggarumar zanga- zanga a majalisar kasa, domin a bukaci yin cikakken bincike dangane da lamurransa a majalisar.

“Domin a samu cikakken binciken samun nasara kan lamurran da suka shafi jarrabawa a Nijeriya, muna bukatar da Shugaban majalisar Wakilai ta kasa da ya nada wani dan majalisa da yake da gaskiya da rikon amana , ya kuma san me meme aka nufi da harkar jarrabawa ya Shugabanci shi kwamitin mai muhimmanci, wanda yake da aikin yin binciken dangane da ilimin yara na Nijeriya yake kasancewa.

“Domin ci gaba da kasancewa da harkar ta lamarin gaskiya kamar yadda ake yi a wasu sassan duniya, ya dace ayi wa Honorabul. Oboku Oforji cikakken bincike. Hakanan ma kamar yadda suka yi karin haske suna kira da hukumomi yaki da karaba rashawa da cin hanci, shi ma su yi masa cikakken bincike, domin hakan ya zama izna ga wasu.

“Yayin da muke jinjinawa hukumomin jarrabawar akan ayyuka nigari da suke yi duk kuwa da yake ba isassun kudade aka basu ba, sun kasance a ayyukan da aka sansu da sun a yadda suke gwada lamarin daya shafi ilimi da yadda dalibai suke fahimtar sa da ganewa.Don haka ya dace su kasance basu da wata damuwar da za ta iya kawo masu cikas, bugu da kari kuma bai dace wasu su rika sa masu baki ciki al’amuransu ba.”

Kungiyar ta ce yayin da su kudaden aka bukace saboda sunan kwamitin,an samu mayar da wasu sauran mambobin kwamitin inda suka zama saniyar ware duk lokacin da aka ce idan ire- iren wadannan kuaden sun shigo. Wannan kamar yadda suka ce , yana nufi kwamitin bai yin aiki kamar yadda ya dace yayi a cikin majalisarm sai dai kuma lamarin da awai daure kai yadda aka bukaci su kudaden.

Shi ma lamarin daukar kwararru ya kara lalata lamarin ya zama mai matukar wuya. Gamaiyar kungiyoyin sun nuna rashin jin dadinsu akan irin yadda aka gano abubuwa basu tafi kamar yadda ya dace ba, wato yadda aka dauki kwararru da sallamarsu, inda suka ce maganar daukar su kwararrun da sallamarsu duk an yi abin ne ta hanyar da bata kamata ba, musamman ma idan aka lura da wassu basu da niyyar su yi aiki kamar yadda ake bukatar su da su yi, abin ya kasance yana da alaka da bukatun wasu ko wani.

Duk da yake da maganar mayar da Naira milyan 43 an yi haka ne saboda saboda wani adaga cikin biyan da aka yi, duk da hakan ita kungiyar tana bukata a binciki dalilin da yasa aka yi biyan da kuma mayar da kudaden,wannan ya zma dole ne ta hanyar bincike, musamman ma sauran ‘yan kwamirin an ce basu zo ba a wurin aikin da ake zargin an biya kudin.

Abin da yake ya zarce lamurran kudi, kunfiyoyin masu zaman kansu sun yi maganar dangane da wasikun da ake zargi nan rubuta wa hukumomi kamar su Babban Bankin kasa da kuma ofishin Akanta janar na kasa ,inda aka bukaci su bada bayanan asusun ajiya na su hukumomin shirya jarrabawa.

Kamar dai yadda kungiyar ta ce ire- iren wadancan bayanan ana yin amfani da su ne wajen cin mutuncin wadanda suka ki yarda su bada abinda aka yi bukata. Idan hakan gaskiya ne, hakan zai kasance wani babban abin ki ne da gudu, har ila yau awanda yake da matukar hadari wajen al’umma muddin suka fahimci su ‘yan majalisar suna yin amfani da damar da suka samu ne domi su maida dama ta kasance hagu.

Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Yadda Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiya Bayan Shekara 22
  • Leadership Hausa
    Bukatar Kawo Karshen Akidar Kyamar Baki A Kasar Afirka Ta Kudu

MASU ALAKA

Matar Gwamnan Zamfara Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Tsarin Bunƙasa Ilimin Ƴa Mace
Ilimi

Matar Gwamnan Zamfara Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Tsarin Bunƙasa Ilimin Ƴa Mace

June 20, 2026
Hukumar Ilimin Bai-ɗaya Ta Jihar Yobe Ta Raba Kayan Karatu
Ilimi

Hukumar Ilimin Bai-ɗaya Ta Jihar Yobe Ta Raba Kayan Karatu

June 20, 2026
NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund
Ilimi

NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

June 13, 2026
Next Post
Ƴansanda Sun Kama Fitattun Shugabannin Ƴan Fashi Biyu A Kwara

Ƴansanda Sun Kama Fitattun Shugabannin Ƴan Fashi Biyu A Kwara

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026
Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

June 25, 2026
Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

June 25, 2026
Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

June 25, 2026
Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

June 25, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

June 25, 2026
Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

June 25, 2026
Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

June 25, 2026
Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

June 25, 2026
Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

June 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.