ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masu Garkuwa Na Neman Naira Miliyan 150 Kan Yaran Da Suka Sace A Kogi

by Sani Anwar
4 months ago
Kogi

Masu ‘yan ta’adda da suka yi garkuwa da yaran gidan marayu da makaranta da ke wani yanki mai nisa a Zariagi, kusa da mahadar Kabba da ke Lokoja a Karamar Hukumar Lokoja ta Jihar Kogi, sun bukaci a biya su kudin fansa kimanin naira miliyan 150, kafin su saki yaran.

Lamarin, wanda ya faru a daren ranar Lahadin da ta gabata, an yi garkuwa da mutane kimanin 26 da suka hada da yara 24 da kuma mata biyu na mai gidan da suka shiga, a lokacin da wasu dauke da makamai suka kutsa kai cikin gidan.

Wani malami a makarantar, Isah Hajarat ya shaida wa wakilinmu cewa; an fara kai harin ne da misalin karfe 11:00 na dare, lamarin da ya jefa yankin cikin rudani.

ADVERTISEMENT

“Wasu daga cikin yaran, sun yi nasarar tserewa a yayin harin, amma har yanzu mutum tara suna hannun wadanda suka sace sun,” in ji ta. “Masu garkuwa da mutanen, sun tuntubi mai gidan tare da neman kudin fansa kimanin naira miliyan 150.”

Daya daga cikin daliban da suka tsere, Faruk Alhassan, ya bayyana yadda lamarin ya faru, inda ya bayyana yadda suka samu kansu cikin firgici lokacin da ‘yan bindigar suka far wa harabar.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

“Lokacin da suka zo, sai muka fara ihu da gudu domin mu samu mu tsira, wasu daga cikinmu, sun buya a daya daga cikin dakunan gidan, amma sai suka bi mu har can suka yi kokarin daukar kanina, inda nan take muka fara kuka,” in ji shi.

Faruk ya kara da cewa, daga baya Allah ya taimake shi ya samu ya gudu cikin daji, inda ya tuntubi mahaifinsa, shi kuma ya sanar da jami’an tsaro.

Duk da cewa, bai iya tantance maharan a fili ba, amma ya lura cewa; wasu daga cikinsu sun rufe fuskokinsu, dauke da manyan bindigogi da sauran muggan makamai.

Har ila yau, ya kuma yi kira ga gwamnati, da ta kara kaimi wajen ganin an ceto wadanda aka yi garkuwar da su.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan ‘yansanda na Jihar Kogi, CP Naziru Bello Kankarofi, ya ce; an kubutar da mutane 17 daga cikin wadanda aka sacen ta hanyar yin hadin gwiwa da jami’an tsaro da mafarauta da kuma ’yan banga.

“Mutanenmu sun samu kiran waya da misalin karfe 11:45 na rana, kuma nan take suka garzaya zuwa wurin, muna aiki tare da kungiyoyin tsaro na yankin, mun kuma samu nasarar ceto mutane 17 da lamarin ya rutsa da su, yayin da wasu da suka hada da matan mai gidan biyu da wasu ‘ya’yansa, har yanzu ba a samu damar kubutar da su ba,” in ji shi.

Kwamishinan ‘yansandan ya kara da cewa, ana nan ana ci gaba da gudanar da aikin hadin gwiwa tsakanin jami’an ‘yansanda, sojoji, mafarauta da kuma kungiyoyin ‘yan banga, domin ganin an kubutar da sauran wadanda harin ya rutsa da su.

Haka zalika, Kankarofi, ya nuna damuwarsa game da matakan tsaro na wajen, tare da lura da cewa; yankin da aka sace wadannan mutane, yanki ne mai nisa da yake a kebe, sannan kuma babu ingantaccen tsaro.

“Makarantar tana cikin wani yanki mai nisa da dazuzzuka, sannan babu hanyar shiga, babu kuma isassun gine-gine a wurin.

Kogi
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
ADC Ta Fara Sayar Da Fom Din Takara Kafin Babban Taron Jam’iyya

Zaɓukan Fidda Gwani: ADC Ta Buƙaci INEC Ta Ƙara Mata Lokaci

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.