ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Matasa Za Su Yi Wa Talauci Layar-zana -Farfesa Adedimeji

by Sani Anwar
9 months ago
Farfesa

Mataimakin Shugaban Makarantar Nazarin Tattalin Arziƙi ta Afirka da ke Abuja, Farfesa Mahfouz Adedimeji, ya buƙaci ƴan Nijeriya, musamman matasa da su ɗauki matakan da za su taimaka musu wajen kawar da talauci da kuma taɓarɓarewar tattalin arziƙi.

A cewar mataimakin shugaban, ana kafa gwamnati ne, domin magance buƙatun al’umma, waɗanda a farko suka haɗa da abinci, sutura da kuma matsuguni, wanda dukkaninsu sashe ne tattalin arziƙi.

  • Jakadan Sin Ya Gana Da Shugaba Tinubu, Inda Ya Jaddada Alkawarin Sin Na Karfafa Alaka Da Nijeriya
  • Sin Ta Baiwa Kauyen Gwaji Na Rage Talauci Na Sin Da Habasha Na’urorin Aikin Noma

Ya ƙara da cewa, idan har aka magance muhimman buƙatu na tattalin arziƙi, babu shakka za a iya shawo kan ƙalubale da dama wanda miliyoyin mutane ke fuskanta, inda ya ƙara da cewa; wannan falsafar ta ɗauki nauyin shigar da ilimin tattalin arziƙi a matsayin ginshiƙin horas da ɗalibai, ba tare da la’akari da nau’o’insu ba. Shugaban ya bayyana wannan tsari a matsayin ilimin da ke keɓe a jami’a.

ADVERTISEMENT

Yayin da yake bayyana mummunan talauci a matsayin wanni nau’i na rashin ilimi da cikakkiyar lafiya, rashin isasshiyar rayuwa da rashin samun damar yin amfani da kayan amfani na yau da kullum, Farfesa Adedimeji ya ce; guje wa talauci ga mutane, musamman matasa na buƙatar haɓaka aiki ta hanyar ilimi, samar da samfurorin kasuwa da kuma samun basirar da ke haifar da samun kuɗin shiga ko yin aikin da za a biya mutum kuɗi.

Don, wanda ƙwararre ne a fannin ilmin kimiyya ta duniya, kuma jami’in hukumar kula da hada-hadar kuɗi ta Nijeriya, ya kuma jaddada cewa; rage kashe kuɗaɗe da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga, dabaru ne guda biyu da aka gwada lokaci bayan lokaci na shawo kan matsalar tattalin arziƙi tare da ƙarfafa wa matasa gwiwa, wajen koyon dabi’ar sa kai, domin yana daga cikin samun ƙwarewa da kuma jawo hankalin masu zuwa a nan gaba.

LABARAI MASU NASABA

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

Farfesa Adedimeji ya gabatar da cewa, gyare-gyaren da gwamnatin tarayya ta yi a ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na nuna wasu kyawawan alamu; domin a hankali darajar naira ta ƙaru idan aka kwatanta da kuɗaɗen ƙasashen waje a baya.

Har ila yau, babbar hanyar samun ci gaba ga Nijeriya, a cewarsa; ta ta’allaƙa ne da fannoni daban-daban na tattalin arziƙi, bunƙasa ilimi da sana’o’i, inganta harkokin kiwon lafiya, cibiyoyin tsaro na zamantakewa, samar da ababen more rayuwa da kuma samar da kyakkyawan shugabanci da riƙon amana.

Sannan, ya kuma buƙaci ƴan Nijeriya da su rungumi dabi’ar yin aiki tuƙuru, kana kuma su kasance masu imani, amana, haƙuri da kuma fata na gari.

Farfesa
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Rahotonni

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara
Labarai

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Next Post
Makonni Biyu Bayan Sace Ɗaliban Makarantar Papiri A Neja, Har Yanzu Babu Tuntuɓa

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.