ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nazarin Kisan Gillar Da ‘Yan Kato Da Gora Suka Yi Wa Wani Matashi A Biniwe

by Leadership Hausa
4 months ago
Kisa

Yayi da a kasar nan ake kokarin magance wata matsala, sai kuma aga wata sabuwar matsalar ta kara kunno kai, wannan lamarin, za a iya cewa, ya yi daidai da batun kisan gillar da aka yi wa wani mai yi wa kasa hidima mai suna Ben Agir.

Ana dai zargin wasu ‘yan kungiyar Kwato da Gora ne, suka hallaka marigayin ne, a yankin Mbajor da ke a karamar hukumar Buruku, ta jihar Biniwe, inda kisan ya nuna a zahiri, ba batun ana kan wani kokarin, dakile wata matsalar, sai kuma wata ta bulla.

Jihar ta Biniwe dai, na ci gaba da fuskantar matsalar hare-haren ‘yan bindiga musamman a wasu kauyukan ta hanyar cin galaba a kan jami’an tsaro da aka girke, a yankunan da hare- haren ke yin kamari.

ADVERTISEMENT

Kazalika, jihar ta kasance akwai jami’in tsaro iri-iri kamar ‘yansanda jami’ain sibil difens, jami’an tsaro na farin kaya wato DSS, wadanda aka ba za su, zuwa kananan hukumomin jihar, bisa nufin tabbatar da tsaro.

Amma abin bakin cikin, shi ne, yadda ake ta ci gaba da samun yawan hare-haren na ‘yan bindiga a yankunan jihar, na ci gaba da jefa fargaba, da kuma tayar da hankulan alummomin da ke a yankunan, wanda a zahiri, hakan ke nuna cewa, ana samun gibin gazawar samun bayanan sirri.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

An dai kafa jami’an na ‘yan Kato da Gora ne, bisa nufin rage kalubalen na rashin tsaro, amma abin takaici, sai aka buge da ana zargin wasun su da azabtar da mutanen da ba su ji, ba su kuma gani ba da yawan yin kame da kuma karbar cin hanci, a gun wadanda suka kama.

Shin bisa irin wannan mummunar dabi’ar ta ‘yan Kato da Gora, me ke nan za a iya cewa, kasar ta amfana da shi?

Bugu da kari, bisa wannan dabi’ar ta su, a kan alumomin, za a iya cewa, horon da aka ba su domin gudanar da aikinsu na samar da tsaro, ya tafi a banza, musamman ganin yadda suke wuce Makadi da Rawa, na ka’idar da aka gindaya masu, na ayyukansu na bayar da tsaro, ga alumma.

‘Yan da dama, musamman a yankunan karkara, na ci gaba da fuskantar barazana daga gun ‘yan Kato da Gora, wadanda a zahiri, an kafa su ne, da nufin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Marigayi Ben dai, an tura shi zuwa jihar Gombe ne, domin yiwa kasar hidima.

Rahotannin sun ce, ‘yan Kato da Gorar, sun hallaka marigayin ne, bayan sun kama, bisa zarginsa da satar wani Babur, inda suka lakada masa na Jiki, har ta kai ga, ya fita daga cikin hayyacinsa.

An ji ma ace, Ben ya sace Babur din ne, amma mai ya kai ‘yan Kato da Goran, aikata masa wannan danyen hukuncin da har ta kai gay a rasa ransa?

Bugu da kari, shin wane irin horo ne, aka bai wa ‘yan Kato da Goran, da har za su rinka daukar doka a hannunsu?

Hakazalika, irin makamancin wannan yanayin ya faru a watan Agustan 2025, yayin da gungun wasu ‘yan Kato da Gora, a jihar Anambara suka kutsa, a cikin masaukin Oba, na Idemili, a karamar hukuma ta Kudu, suka lallasa wata mai yi wa kasa hidima, mai suna Jennifer Elohor.

Sai dai, gwamnatin jihar, daga baya ta kore su daga aiki tare da gurfanar da su, a gaban kotu, inda a yanzu, suke ci gaba da fuskantar tuhuma.

Karin wani abin takaicin shi ne, a yayin da Jennifer ke dakon samakamakon huncin da kotun za ta yanke wa ‘yan Kato da Goran da suka aikata mata ta’asar sai kuma aka samu bullar wani sabon lamarin na kisan gillar da aka yiwa marigayi Ben a jihar Biniwe.

A Nijeriyar mu ta yau dai, a bayyane yake yadda masu kayan Sarki, ke yin amfani da karfin ikonsu, suna gallaza wa jama’a. Misali, a lokacin zanga-zangar #ENDSARS, wasu ‘yansanda sun yi amfani da karfin Tuwo wajen tumurmusa wasu masu gudanar da zanga-zangar ta #ENDSARS, wanda hakan ya sanya akaita ta kai komin, ganin an haramta rundunar ta #ENDSARS, daga baya kuma aka samu nasarar yin hakan.

Lokaci dai ya yi ga daukacin matakan gwamnati uku na kasar takawa ‘yan Kato da Gora da kuma suran jami’an tsaron kasar, kan take ‘yancin ‘yan Adam.

Ya zama wajbi. Jami’an tsaro a kasar nan su kwan da sanin cewa, an kafa su ne, domin kare rayukan ‘yan kasar amma ba wai daukar rayukansu bisa zalunci ba

Kazalika, dole ne, ‘yan Kato da Gora da ke a jihar ta Biniwe da sauran wadanda ke sauran sassan kasar nan da su sani cewa, an kafa su ne, domin wanzar da aikin zaman lafiya da kare rayukan ‘yan Nijeriya da dukiyoyinsu.

Muna mika ta’aziyyar mu ga iyayen marigayi ben, da kuma hukumar ta NYSC ta kasa, bisa wannan rashin da a yi.

A ra’ayin wannan Jaridar, ba tare da bata wani lokaci ba, gwamnatin jihar Biniwe, ta tabbatar da an hukunta ‘yan Kato da Goran da ake zargin da aikata wannan mummunar ta’asar ga Ben.

Haka, ya zama wajbi, a san irin horon da za a rinka bai wa ‘yan Kato da Goran tare da kuma sanya ido a kansu, musamman domin kaucewa hallaka jama’a, ba gaira ba sabat.

Kisa
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Gudunmawar Likitocin Dabbobi Wajen Hana Barkewar Cututtuka

Gudunmawar Likitocin Dabbobi Wajen Hana Barkewar Cututtuka

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.