ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 21, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yari Ya Dace Da Rayuwar Mulki Da Kasuwanci

by Sulaiman and Naziru Adam Ibrahim
1 month ago
Yari

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya, Sanata Abdulaziz Yari, da alama ya fara sabawa da rayuwar attajiri mai tasiri a harkokin kasuwanci, musamman a fannin makamashi da samar da makamashi.

Yari, wanda aka zaɓa Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma a shekarar 2023, ya yi yunƙuri mai ƙarfi na zama Shugaban Majalisar Dattawa jim kaɗan bayan shiga majalisar inda har ya kusa kai yawan ƙuri’un da Shugaban Majalisar Dattawa na yanzu, Godswill Akpabio, ya samu.

A yayin wannan takara, Yari ya girgiza tsarin siyasar majalisar, tare da zargin cewa wasu daga cikin abokan siyasarsa sun yi masa butulci duk da tabbacin da ya yi cewa suna tare da shi.Sai dai daga irin rayuwar da yake yi a yanzu da kuma yadda ya karkata zuwa harkokin kasuwanci, mutum zai iya tunanin cewa Yari na shirin rage yawan shiga harkokin siyasa, yana fitowa ne kawai lokaci zuwa lokaci a Majalisar Dattawa inda yake wakiltar al’ummar Mazaɓar Zamfara ta Yamma.

ADVERTISEMENT

A ƙarshen shekarar da ta gabata, Yari ya zama sabon shugaban kamfanin Geregu Power PLC, inda ya maye gurbin Femi Otedola, tare da karɓar ragamar gudanar da kamfanin samar da makamashi.Wannan ciniki mai darajar ɗaruruwan miliyoyin daloli ya gudana ne tsakanin kamfanin MA’AM Energy Ltd na Yari da kamfanin Amperion Power Distribution Company Ltd na Otedola, yayin da aka ƙiyasta darajar Geregu Power da kusan naira tiriliyan 2.83.

Duk da haka, da kuma yadda yake nuna sha’awa ga harkokin kasuwanci, alamu na nuna cewa Yari, bai juya baya ga siyasa gaba ɗaya ba, duk da cewa ba kasafai ake ganinsa a tarukan siyasa ko wasu muhimman harkokin siyasa a jihar ba.

LABARAI MASU NASABA

Abubuwan Da Ke Tattare Da Jami’in Soja Sambo Dasuki

Siyasar 2027: Yadda Ƴan Adawa Ke Ƙara Shiga Tsaka-mai-wuya

Kafin zaɓen fidda gwani na APC, wanda aka tantance masu neman tikitin jam’iyyar zuwa Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Yari bai halarci taron masu ruwa da tsaki da aka shirya domin cimma matsaya kan masu neman muƙaman zaɓe ba.Kusan dukkan manyan fitattun ‘yan siyasar Zamfara, sun halarci taron ciki har da tsoffin gwamnoni Ahmad Sani Yarima, Mahmuda Shinkafi, da Bello Matawalle.

Haka kuma, shugabannin jam’iyya a matakin jiha da ƙasa, tare da sanatoci masu ci kamar Sahabi Yau Kaura, da Ikra Aliyu Bilbis, sun kasance a wurin taron.Sai dai duk da rashin halartarsa, Yari ya samu tikitin takarar Sanata na APC a mazaɓarsa cikin sauƙi ba tare da wata gagarumar adawa ba.

A halin yanzu ma, ƙungiyoyin matasa suna yaƙin neman ganin Shugaban ƙasa ya naɗa Yari a matsayin Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa, inda suke faɗaɗa wannan gangamin zuwa ga ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki masu alaƙa da shugaban ƙasa.

Jagorantar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na iya zama wata dama da za ta sake dawo da Sanata Yari, cikin zafin fafatawar siyasa, duk da cewa a yanzu ya fi karkata ga harkokin kasuwanci da makamashi.

Yari
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Game Da Inganta Mu’amalar Shugabanninsu A Bana
  • Sulaiman
    Wang Yi: Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Manufofin MDD
  • Sulaiman
    Mayar Da Muradun Jama’a A Gaban Komai: Daga Hikimar Da Aka Gada Tsawon Dubban Shekaru Zuwa Akidar Zamani
  • Sulaiman
    Karfin Sin A Bangaren AI Ya Samarwa Kasashe Masu Tasowa Damarmakin Cin Gajiyar Fasahar
Yari
Naziru Adam Ibrahim
+ posts Bio
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    Ya Kamata Farashin Siminti Ya Sauka — Umahi Ga Masana’antun Siminti
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    A Ƙarshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Dama Ta Yin Takara
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    Shugaba Tinubu Ya Isa Nairobi Domin Halartar Taron Tattalin Arzikin Nahiyar Afirka
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    Gwamnatin Filato Ta Kwato Kadarorin Jihar Da Aka Wawashe

MASU ALAKA

Abubuwan Da Ke Tattare Da Jami’in Soja Sambo Dasuki
Nazari

Abubuwan Da Ke Tattare Da Jami’in Soja Sambo Dasuki

June 28, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe
Manyan Labarai

Siyasar 2027: Yadda Ƴan Adawa Ke Ƙara Shiga Tsaka-mai-wuya

June 19, 2026
Lionel Messi: Mutum Ko Aljan
Wasanni

Lionel Messi: Mutum Ko Aljan

June 17, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Tattauna Da Kim Jong Un

Xi Jinping Ya Tattauna Da Kim Jong Un

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Game Da Inganta Mu’amalar Shugabanninsu A Bana

Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Game Da Inganta Mu’amalar Shugabanninsu A Bana

July 20, 2026
Wang Yi: Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Manufofin MDD

Wang Yi: Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Manufofin MDD

July 20, 2026
Mayar Da Muradun Jama’a A Gaban Komai: Daga Hikimar Da Aka Gada Tsawon Dubban Shekaru Zuwa Akidar Zamani

Mayar Da Muradun Jama’a A Gaban Komai: Daga Hikimar Da Aka Gada Tsawon Dubban Shekaru Zuwa Akidar Zamani

July 20, 2026
NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir

NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir

July 20, 2026
Karfin Sin A Bangaren AI Ya Samarwa Kasashe Masu Tasowa Damarmakin Cin Gajiyar Fasahar

Karfin Sin A Bangaren AI Ya Samarwa Kasashe Masu Tasowa Damarmakin Cin Gajiyar Fasahar

July 20, 2026
Sin Ta Zamo Kan Gaba A Duniya A Fannin Kirar Mutum-Mutumin Inji

Sin Ta Zamo Kan Gaba A Duniya A Fannin Kirar Mutum-Mutumin Inji

July 20, 2026
Shari’ar Malami Ba Za Ta Dakatar Da Burinsa Na Gwamna Ba, Inji Jam’iyyar ADC Ta Kebbi

Shari’ar Malami Ba Za Ta Dakatar Da Burinsa Na Gwamna Ba, Inji Jam’iyyar ADC Ta Kebbi

July 20, 2026
Kimi K3 Ya Bayyana Yunkurin Sin Na Raya Fasahar AI A Bayyane Ta Yadda Kowa Zai Amfana

Kimi K3 Ya Bayyana Yunkurin Sin Na Raya Fasahar AI A Bayyane Ta Yadda Kowa Zai Amfana

July 20, 2026
Kwamandojin Kungiyar Ansaru Biyu Sun Amsa Laifin Garkuwa Da Mutane A Kotu

Kwamandojin Kungiyar Ansaru Biyu Sun Amsa Laifin Garkuwa Da Mutane A Kotu

July 20, 2026
Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin A Saliyo Ta Fara Horar Da Ma’aikatan Jinya Dabarun Likitancin Gargajiya Na Sin

Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin A Saliyo Ta Fara Horar Da Ma’aikatan Jinya Dabarun Likitancin Gargajiya Na Sin

July 20, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.