ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Munafunci Dodo Ya Kan Ci Mai Shi

by Sulaiman
10 months ago
Dodo

Katobarar da firaministar kasar Japan Takaichi Sanae ta yi a kwanakin baya, cewa wai “farmakin kasar Sin a kan Taiwan” na iya zama “barazana ga dorewar kasar Japan”, lamari ne da zai sa Japan ta dauki matakan soja, ya yi matukar fusata al’ummar kasar Sin, har ma gwamnatin kasar Sin ta dauki kwararan matakai na mayar da martani, don bayyana niyyarta a kan batun Taiwan, wato batun Taiwan ba na wasa ba ne, kuma duk wanda ya yi wasa da batun lallai zai kare a kansa.

Akwai aminaina ‘yan Nijeriya da suka min tambaya, cewa me ya sa kasar Sin ta mayar da martani mai karfin haka game da kalaman Takaichi Sanae? Domin amsa tambayar, zan so in tattauna tare da ku game da tarihin yankin Taiwan, da ma ainihin abun da ya haddasa batun Taiwan, da ma mugun burin da Takaichi Sanae ke neman cimmawa.

In mun yi nazari a kan tarihi da ma dokoki, za mu tabbatar da cewa, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin. Muna iya gano sunan Taiwan a littattafan gargajiya na kasar Sin tun karni na 3. Tun karni na 12 kuma, gwamnatocin daulolin gargajiya na kasar Sin suka fara mulkin yankin Taiwan. A shekarar 1895, kasar Japan ta mamaye yankin Taiwan bisa yakin da ta tayar, daga nan kuma ta shafe tsawon shekaru 50 tana wa yankin mulkin mallaka, wanda ya zama tarihi mafi muni ga yankin Taiwan. Bayan yakin duniya na biyu, Sanarwar Cairo, da Sanarwar Potsdam, da takardar ba da kai ta Japan da dai sauran wasu takardu masu karfin doka na duniya, a bayyane ne suka bukaci Japan da ta mayar da Taiwan, da ma tsibiran Penghu da ta sata daga hannun kasar Sin. Ya zuwa ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1945, gwamnatin kasar Sin ta sanar da maido da mulki a yankin Taiwan, daga nan kuma, yankin Taiwan ya dawo karkashin mulkin kasar Sin bisa doka kuma a zahiri. Ba da jimawa ba bayan da kasar Sin ta cimma nasarar yaki da mamayar dakarun kasar Japan, jam’iyyar Kuomingtang da a wancan lokaci take mulki a kasar Sin ta tada yakin basasa, sai dai ba a kai shekaru uku ba ta ci tura, har ma ta gudu zuwa yankin Taiwan. Kasar Amurka ta nuna goyon baya ga jam’iyyar Kuomingtang, ta hanyar hana rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin su ‘yantar da yankin Taiwan, lamarin da kuma ya haifar da batun Taiwan da muke fuskanta a yau. Duk da matsalar siyasa da babban yankin kasar Sin, da kuma yankin Taiwan suka fuskanta a cikin sama da shekaru 70 da suka wuce, ba a taba raba Taiwan daga kasar Sin ba, kuma kasancewar yankin Taiwan wani bangare ne na kasar Sin abu ne na zahiri wanda ba a taba canza shi ba.

ADVERTISEMENT

To, da haka muke iya gano cewa, katobarar Takaichi Sanae ta kasance tsoma baki cikin harkokin gida na kasar Sin, wadda kuma ta lalata dokokin kasa da kasa, da ma tsarin odar duniya bayan yakin duniya na biyu.

Ga wadanda za su iya tunawa da tarihi, sun san ba wannan ne karon farko da Japan ta yi amfani da kalmar “barazanar dorewar kasa”, da “kare kai”, wajen kaddamar da munanan farmakin soji ba. A cikin shekarar 1931, Japan ta bayyana “ko za a samu iko a yankin Manchuria na kasar Sin” a matsayin abin da ke “barazana ga dorewar kasa”, har ma ta fara kai hari ga yankin arewa maso gabashin kasar Sin, daga nan har ta fadada yaki zuwa sauran sassan Asiya. Har wa yau, Japan ta kuma taba kallon “ko za a kai hari tashar ruwa ta Pearl Harbour ko a’a”, a matsayin “abin da ke barazana ga dorewar kasa”, lamarin da daga baya ta haddasa yakin tekun Pasifik. A yau kuma, firaministar kasar Japan ta sake ambaton batun “barazana ga dorewar kasa”, ke nan me take neman cimmawa? Ko tana son maimaita abubuwan da suka faru a tarihi, tare da sake yin gaba da jama’ar kasar Sin da na Asiya baki daya? Ko kuma tana fatan ganin an lalata tsarin odar duniya bayan yakin duniya na biyu?

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Bana ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin kin tafarkin murdiya a duniya, haka kuma ake cika shekaru 80 da kasar Sin ta dawo da yankin Taiwan daga mulkin mallaka na kasar Japan. Kasar Sin za ta tsaya tsayin daka a kan hana farfadowar ra’ayin nuna karfin soja, tare da kiyaye nasarorin da aka cimma a yakin duniya na biyu, da ma tsarin odar duniya bayan yakin. Kamata ya yi sassan kasa da kasa su ma su hada hannu wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Japan a nata bangaren, ya kamata ta martaba zaman lafiya a maimakon yin watsi da tarihi. (Lubabatu)

Dodo
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Ɗalibai 50 Da Aka Sace A Neja Sun Tsere CAN

Ɗalibai 50 Da Aka Sace A Neja Sun Tsere CAN

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.